← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 121

Sashe 7

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci ya tafi, sai mun haɗu a wani page ɗin, In Sha Allah duk sauran wasu kayan gyara suna nan tafe, daga gyaran fatar jiki, har kan gyaran can ciki, ma'ana kayan karin ni'ima na mata da sauransu, amma fa ba alkawari na yi maku ba, idan na sami time zan rinƙa jefo maku a cikin page's ne....... Ma'assalam...✍️ PRINCESS TEEMA💋❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E3-4

Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati.

Can kasan maƙoshinsa ya ce "Babyn daddy ya naga kamar daddy ya yi ajiya ne?" Cikin nuna ko in kula domin bata ma san ma'anar maganar tasa ba, ta ce "Daddy ajiyar me kuma? A ina kuma kayi ajiyar?".

Miƙewa ya yi daga rumfar da ya yi mata ya zuba mata ido sosai, yana kare mata kallo, tabbas ta kara kyau sosai, amma kuma ba abin da yake tunanin ɗin bane, kawai dai kyau ne na tsantsan kula da take samu daga gare shi.

Ganin ba abin da yake tunani bane yasa ya shafa shafaffen cikinta nata tare da haÉ—e fuskokinsu, kasa kasa ya ce "Jelly ita kaÉ—ai Allah ya bani, ina bala'in son yara, wlh idan na kalli yara a hannun wasu, ji nake tamkar in je in kwacesu, ya Allah ka bani baby a wannan haÉ—uwar tamu da zamu yi yanzu". Ya kai karshen maganar yana yana mai hauro da hannunsa zuwa saman kirjinta.

(Tofa shi kuma Romeo ba abin da ya tsana kamar yara, ga wasu kuma a nan suna nema ido a rufe, Allah ya shirya Romeo da rashin son yara)

"Daddy nima ina son yara wlh, musamman ma kanana suna da kyau kamar me". A hankali hankali ya fara shafo breast ɗin nata yana faɗin "Musamman ma idan a kace yaran sun yi kama dake ba, wlh ba ƙaramin kyau za su yi ba".

Zata yi magana ya capko bakin nata tare da zura mata harshensa cikin tata ya fara kissing nata.

Shiru ta natsu tana biye mashi, yanzu idan da sabo, ta gama sabawa da jarabarsa, tun abin yana damunta har ya dai'na, ta rungumi kaddararta na hakura da jararrabar mijin nata, sai dai kuma shi ba kamar sauran irin mazanmu na yau da kullun bane, mafi yawancin maza suna ɗauka jima'i shi ne kawai aure, shi ba haka yake ɗauka ba, tabbas yana da jarabar tsiya, amma kuma yana ƙoƙarin ya zama cikakken miji, yana ƙoƙarin ya yi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, domin Annabi har wanke wanke yana taya su Nana A'isha, Nana A'isha da bakinta ta ce har ƴar tsere suna yi da Manzon Allah (S.A.W) a gida, ya kama maza su sani ba iya biyan buƙatarsu a wajen mace, da ciyar da ita da shayar da ita ne kawai ya zamana hakki a kansu ba, ya kamata su nemi sanin tarihin fiyayyen halitta domin su samu gobe mai kyau, ga dai misali akan daddyn Jelly, yana balain kaunarta, yana kula da ita, yana faranta mata, ya mai da ta tamkar wata sarauniya, to yanzu ku gaya mani me ya ragu da shi da yake yi mata hakan? Wlh babu abin da ya ragu da shi, sai ma karuwa da ya yi na samin ɗumbin lada wajen Ubangiji, ya yi koyi da Manzon Rahma, ba ko wani namiji ne zai iya yin hakan ba, amma yana da kyau ku rinƙa kwatantawa koma yayane, domin a rage wasu matsalolin na cikin rayuwar aure, kuma, mata na juyo gare mu, yana da kyau mu gyara halinmu, misali akan Aunty, Ayla, da kuma Umaisha, irin halinsu yasa dole mazajensu ke kyautata masu, hakuri, juriya, riƙo da addini, kyautata mashi, kome ya ce matukar bai saɓawa Allah ba cene mashi to, kuma kiyi mashi a lokacin, kada ki yi gardama ko ki yi musu da shi, ki daure ki jure ki yi biyayya, ko da baki samu jin daɗi yadda kk so a nan duniya ba, ki sani a lahira zaki more, zaki huta, zaki ji daɗi fiye ma da yadda ki ke so ɗin, kada ki yarda ki yi biyu babu, babu duniya kuma babu lahira, kada ki yi koyi da irin halinsu Ommu, ki tabbatar kin yi koyi da halin ɗaya daga cikin waƴan nan Aunty, Ayla, ku kwatatan ku yi tunanin me yasa mazansu ke kyautata masu? Meyasa suke kaunarsu? Saboda sun nunawa mazan nasu cewa sune sarakunansu, sune sama da su, ko wani namiji yana son girmamawa, dan haka mu gyara, Allah Ubangiji yasa mu dace.

STORY💋

Sosai ya more kayarsa ko in ce suka mori juna, domin kuwa yanzu ita ma ta kware sosai, ya koya mata, ta zama irinsa.

Sun jima kwance manne da juna yana zuba mata kalamai tare da shagwaɓa kamar wani yaro, ya zama tamkar ƙaramin yaro a gaban matar tasa, ba ya wani damuwa da zancen zata raina shi, dan yasan ba haka take ba, shiyasa yake zuba mata shagwaɓarsa son ransa, kuma da yawan maza ba wai basa son yin hakan da matansu bane, kamar yadda na faɗa a baya, gani suke yi kamar idan suka yi hanan da matan nasu, matan za su rainasu, wannan dalili yasa suke tsare gida abinsu, wani ma da ya fara hakan sai ta fara ce mashi ragon namiji, to ƙalu bale garemu mata, ko yau a ka haifi namiji to fa sama yake da ke, ko da kuwa kin kai shakara hamsin, Ubangiji ne ya fifitasu akan mu, mune a kasarsu, ba lallai sai miji bama, ko wani irin namiji sama yake da mace, to ina ga kuma ance mijinki? Wadda shi ne Annabi ya ce, da bawa yana yi wa bawa sujjada, to da tabbas zai yi wa mace umarni ta rinƙa yi wa mijinta domin girmamawa, tabbas Allah ya girmama miji sosai akan mata, ko me miji zai yi maki bai kamata magana ta raini ta shiga tsakaninku ba, tun da Ubangiji da kansa ya bashi wannan girma da kuma power, yana da kyau mu kula da hakan dan kada mu zo duniya a banza kuma mu koma a banza, Annabi ya ce mata sunfi yawa a wutar jahannama, wannan magana kuma kunsan tabbas haka ne, innalillahi wa inna ilaihir rajiun......😭 Ba kuma komai ne yasa mata suka fi yawa a wutar jahannama ba fa ce kin bin umarnin mazajensu, zagin mazajen da kuma rainasu, hakan yasa suka fi yawa a wuta, to dan Allah mai karatun littafi na, kada ki bari ki zama ɗaya daga cikin irin waɗan nan mata, nasihata a gareku shi ne, ku yi hakuri ku daure ku danne, da ki cuci mijinki, wlh gwara shi ya cuceki, kuma ki yi wa Allah ki yafe mashi tare da yi mashi addu'a shiriya, tabbas Allah baya barci, yana ganin komai da yake faru, sai ki ga sanadiyar yafe mashi da kika yi, Allah ya baki gidan aljanna ko da kuwa baki yi aikin shigarta ba, to dan haka ina mai mana nasiha akan hakan, sannan kome zaki yi ki tabbatar domin Allah zaki yi, dan ki samu wannan rabo ta ni'imar Allah, idan ki ka yi domin wani, to ki sani wanin bashi da wuta kuma bashi da aljanna, to is better for you ki yi domin mai wuta da aljanna, dan ki shiga cikin aljannar, Allah Ubangijin ya sa mu dace, ya kuma bamu ikon gyara kura kuran mu, ina kara jaddada mana, muji tsoron Allah, a duk in da muke, mu san Allah yana ganin mu, kuma mutuwa bata da tabbas, tana iya zuwa a ko da yaushe, tana iya ɗaukarki kina tsaka da cin abinci ko aikata wani abin, ace mutuwa ta ɗauki mutun yana aikata saɓon Allah, ina zai tsaya da wannan bala'in,. Akan abin da kika mutu za'a tasheki, kada ki manta a ranar gobe kirayama tabbas ba ke zaki yi magana ba bare ki yi karya, hannun da kika aikata sharri ko alkhairi, shi ne zai yi magana da izinin wadda ya halince shi da mu baki ɗaya, shi zai faɗi abin da kika aikata da shi, haka zalika sauran sassa na gaɓoɓin jikinki, to dan haka mu kiyaye, fatana shi ne mu gudu tare, mu kuma tsira a tare, Allah kuma ya sa hakan Amin, ba zan so ace mai karanta littafi na ta kauce hanya ba, zanji zafin hakan fiye da tunanin mai tunani. YA ALLAH KASA DUK MASU KARANTA BOOKS NA, SU KASANCE NA KIRKI DAN KA HAƊA MU A ALJANNA, IDAN MA AKWAI WANI HALI MARA KYAU DA SUKE YI A ƁOYE, YA ALLAH KA YAFE MASU, KASA SU GYARA DOMIN MU KASANCE A TARE A ALJANNA, INA SON MASU KARATUN LITTATAFAINA💘💋❤️.

STORY💋

Sai da ya ga ta fara yi mashi barci a jiki sannan ya ce ta tashi su je su yi wanka, make mashi kafaɗa ta yi, cikin shagwaɓa da magagin barci ta ce "Ni barci nake ji daddy".

Shafa kanta ya yi yana faÉ—in "Babyn daddy, ki hakura na yi maki wanka sannan ki yi barcin ko? Bana son ki yi barci da najasa a jiki, Annabi ya tsawatar akan hakan, ya hanemu da hakan, domin hakan babbar barazace ga lafiyar É—an adam, idan bawa yana cikin najasa fa to komai yana iya faruwa da shi baby, ciki kuma harda asiri, tsafi, aljanu, shaiÉ—anu, da dai sauransu, dan haka ki daure daddy ya yi maki wanka, in yaso sai ki zo kiyi ta barcinki har sai time da kike so, ni kuma zan yi zaman jiranki har sai kin tashi daga barcin sannan mu fita unguwar ko?".

Duk jikinta ya mutu da jin nasiharsa, hakan yasa ta miƙe, jikinta duk a mace saboda barci, haka ta diro kasa daga saman gadon, sannan suka nufi toilet.

After some minutes, ya fito riƙe da hannunta suka nufi gaban mirror, dukkansu suna ɗaure da towel, da alama dai a tare suka yi wankar.

Lotion ya shafa mata kafin nan ya sanya mata kananan kayanta tare da fesheta da perfume nasa masu daɗin Kamshi, sannan ya ruƙo hannunta suka wuce saman gado yana faɗin. "To jeki kwanta bari na shirya na zo mu kwanta sai zuwa anjima mu fita ko?".
Chapter 7 · 0% Book details