← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 121

Sashe 11

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya fara magana "Rimsha bappa Hosain ya yi kuskure, ba laifin Saif bane, laifin bappa Hosain ne, tayaya zai yi irin wannan furuci a gare su? Bari na fahimtar da ke wani abu, ki sani tsawon Wannan lokaci da baku tare da bappa yana tare ne da su ne fa, yana gidansu na Washington DC, ya zauna da su, wlh tun kafin su zo nan idan muka yi magana da Areef, ba zai yi magana biyu bai kira mani sunan Musharraf ba, yana matukar son daddynki, haka zalika shima Aseef, wannan son da suke yi wa daddynki yasa Saif ya fara kaunarsa, ki sani wlh ko tsuntsuwa bata isa ta sauƙa a gidansu Saif ba, basu son baki ko kaɗan, amma Allah shi kaɗai yasan dalilin da ya sanya ya sa masu kaunar daddynki a ransu da har suka sanya shima Saif ya fara son shi, sun kula da bappa sosai, sun kyautata mashi, yasan halinsu mai kyau da mara kyau, meyasa zai zo ya yi irin wannan furuci akan su na cewa yasan turawa basu da hankali, basu da hankali suka kula da shi haka? Ai ko dan saboda Aseef da Areef tun da bai san Saif ma yana kaunarsa ba, ko dan Areef bai kamata ya yi wannan magana ba, kuma na ƙara gaya maki Saif yana kaunar bappa saboda yadda ya rinƙa sanya Aseef farincikin, mawuyacin abune ki iya gane idan Saif yana son wani abu, amma su Areef sun gane yana kaunar Bappa, to kinga bappa ya yi kuskure, yes ke ƴarsa ce, yana da kyau ya nuna irin haka a kanki, amma baga mutane irinsu Areef ba, yakamata ya tausasa kalaman shi ne a kan su, ni da ban zauna da su a cikin gidansu na Usa ba ma, nasan cewa wallahil azim su ba manema mata bane, ke su dukka da kike ganinsun nan basu da lokacin mace, harta Areef da kike gani mai sauƙin kannan, yanzu da zaki kawo mashi maganar aure in a serious matter, dariya zai yi ya mai daki baki san me kike yi ba, babu zancen aure ko neman mata a ransu, saboda suna ganin ɓata lokaci ne, kawai ni na yarda wani iko ne na Ubangiji da yasa suke kaunarki, daga Areef har Aseef, Allah ne kawai ya sanya masu kaunarki, to su ba mazinata bane ,basu neman mata, amma bappa ya zo ya masu magana a gatse haka, wai turawa mazinata ne, basu ɗauki zina a bakin komai ba, kinga kuwa dole Saif ya ɓata rai, wlh ina mai tabbatar maki Saif ya yi maku hukunci mai sauƙin daga ke har bappa, kuma ya yi hakan ne saboda ni, dan ni ya sassauta maku hukuncin, to dan haka ki godewa Allah ma da hakan, sannan magana ta karshe ina son ki sani Saif ba mugu kamar yadda kike tunani bane, kawai haka yanayinsa yake, kuma bappa ya ɓata mashi rai ne, dama sai anyi laifi yake yin hukunci, baya hukunta wanda bai yi laifi ba, ina da tabbacin idan ya sauƙo zuciyarsa ta yi sanyi, shi da kansa ba zai so kina mace ƴar musulma kuma kina shiga ɗakin su Mark ba, ba zai so hakan ba, kuma zaki gani, zai dakatar da ke daga yin hakan, ni nasan waye shi fiye da yadda kike zato, amma dai kafin ya sauƙo ya waiwayeki ɗin shi ne aiki, zaki sha wuya kam, da ya sauƙo kuma shikenan zai dakatar dake daga yi wa su Mark aikin, sai dai fa rabaki da bappa kam ya riga da ya yi, an wuce wajen, shi ma aikin abin da yasa na sanya a raina zai dakatar dake, saboda shi musulmi ne, yasan haramcin hakan a addini, ke dai ki yi addu'a kawai, amma ki daina ganin laifin Saif". Ya kai karshen maganar tare da shafa kanta ya gangaro da hannunsa izuwa saman face nata ya goge mata hawaye.

Suna cikin haka Areef ya lallaɓo ya iso wajen ya same su, jikin nasa Alhamdulilah, ya sami kulawa daga wajen ɗan uwan nasa sosai, cikin ƙanƙanin lokaci ya sami sauƙin ciwon nasa.

A É—ayar kujerar dake fuskantarsu ya zauna yana tambayar Imran me ya yi wa Sarauniyar Triplets É—in su, ya yi maganar yana zarewa Imran É—in idanu.

Imran bai san time da dariya ta subce mashi ba, ji yadda Areef ya zare mashi waÆ´an nan dara daran idanun nasa, ai sai ya sa mutun ya gudu, ita ma dai Rimsha ya bata dariya kuma ya bata tsoro, domin kuwa, idan baku mance ba, akwaisu da dara daran idanu kamar ball, zarosu da ya yi kuwa, ai kunga za su kara girma.

Ganin ta yi dariya ne yasa shi ma ya saki cool murmushi. "Our Queen dariya yana yi maki kyau sosai over". Ya faÉ—a cikin sanyin murya. Kasa ta kara yi da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

Kai ash eyes nasa ya yi saman hannun nata, wani irin tausayinta ya ji lokacin da ya kalli hannun nata, har lokacin sunanan wasu iri da su, sun É—anyi wani baki bakin ciwo, alamar wajen yana son warkewa.

Sorry ya yi mata tare da gaya mata kalamai da za su sanyaya mata zuciyarta, ya kuma yi mata alkawarin ba zai sake bari ayi mata makamancin haka ba, komai wuya komai daÉ—i zai yi kokari wajen ganin ya cika alkawarin da ya É—aukarwa Uncle Hosain É—insa na kula da ita.

Amma fa da ni da ku munsan sone ya jawo hakan, ita da Imran ne ba su sani ba, ba wani alkawari, kawai sonta yake yi yana dannewa saboda Saif take so, kuma a zahirin gaskiya shi ya fi su Saif sanin menene so, domin kuwa shi ya fi su yawan shige shige, Saif bai san menene so ba, dan kunsan baya shaga irin wannan layin, shima dai Aseef yanzu ba za'a yanke mashi hukunci ba, domin yanzu a sabon mutun yake, yanzu yake tantance daidai da ba daidai ba, Imran da yake wani gaya wa Rimsha su basu son mata, to ga dai Areef ya kamu da soyayya, sanin basu son mata or aure, sanin baya ya yi masu, sai dai auren ne har yanzu bamu sani ba, shin suna da niyar yi ko yaya, ko kuma muce Areef yana da niyar yi, domin shi kaÉ—ai ne ya san me soyayya ma a cikinsu.

Kalamansa yasa dukkansu daga ita har Imran É—in sun ji daÉ—i, sosai Imran ya yi mashi godiya, girgiza kai ya yi alamar baya son godiya, daga haka suka shiga hira, ta saki jiki sosai, ta mance komai ta biye masu sai hira suke yi, sun É—auketa kamar wata babbar mace saboda hankalinta da natsuwarta, shiyasa basu damuwa suke sanyara a tsakiyarsu suna hira, ba zata rainasu ba, haka zalika tana da kamala sosai.

Suna tsaka da hira Aseef ya kira Areef a waya, wani daɗi na daban Areef ya ji ganin kiran Aseef ɗin, domin kuwa yana zargin Aseef ɗin, yana ji a jikinsa akwai wani abin da yake damun ɗan uwan nasa, ya yi mashi tambayar duniyar nan yaki gaya mashi, sai dai ya ce mashi Exam ne yasa ya shiga damuwa, baya son ya faɗa ne, kuma duk wata hanya da Aseef zai bi dan ya ɓoye damuwarsa ne ko menene Allahu aalam, to fa sai da ya bi wannan hanya, idan ba su da suka yi mashi muguwar farin sani ba, ba zaka taɓa cewa akwai abin da yake damun shi ba dan ya ɓoye.

Ɗaukar kiran Areef ya yi yana mai sakarwa ɗan uwan nasa cool murmushi, zaune yake saman irin waƴan nan manyan baloon na gym ɗin nan, ba bu riga a jikinsa, sai dai wata shegiyar ƴar short da bata gama sauƙa zuwa cinyarsa ba, ga shi wandon ta matse shi sosai, ta roba ce, irin dai wannan ɗan short da mafiya yawan masu motsa jiki suke sanyawa, to shi, waƴan nan santala santalan cinyoyin nasa a waje, ga gashin kansa sai kara tsawo yake yi, sai kara komawa sak kamanin su daddy yake yi abinsa, ya kara wani sihirtaccen kyau da sheƙi irin na addinin musulunci.

Satar kallon Rimsha Areef ya yi domin kuwa yau da ta ga Aseef a irin wannan shiga, da ta yi suma sau bakwai, ranar ma ba riga kawai ta gan shi, amma sai da ta razana, ina ga kuma yau mai kankanta da har zanen komai nasa ana gani, ai sai suma idan suka yi ido biyu.

Dawo da kallonsa ya yi a kan wayar. "Aseef kana buƙatar aure fa". kasa kasa cikin zolaya ya yi maganar.

Kin haɗa ido da shi Aseef ya yi, kuma Areef ya lura da rashin son haɗa ido da su da Aseef ɗin yake yi, dan baya son suna mashi kallon kurillah. "My Areef ina kewar kane fa yasa na kira ka". Sake maimaita maganar ɗazun Areef ya yi "Aseef kana buƙatar aure fa".

Sai lokacin ya É—ago kai suka kalli juna "To ai sai ku yi mani auren ko?". Jinjina kai Areef ya yi yana faÉ—in "Ai ko baka faÉ—a ba, zan sama maka mata a Nigeria in taho maka da ita".

ÆŠaure fuska sosai ya yi yana faÉ—in "Ni bana son matan Nigeria, ni ka bar wannan shirmen ya jikinka?". "Am good now, hope kaima everything yana tafiya yadda kake so?". Girgiza kai ya yi alamar a'a ba komai yake tafiya yadda yake so ba.

"To me matsalar?". Shiru ya yi, tamkar shi da kansa bai san me matsalarsa ba, abin mamaki take bawa Areef, wai yau Aseef ne da jin kunyarsu, sai wani kau da fuska yake yi, anya lafiyarsa kuwa? Abin al'ajabi kunya a cikin jinin William jacop, suda kwata kwata ma basu san menene ita ɗin ba, kunya Hausa fulani suka santa, ba turawa ba, abin ya ɗaurewa Areef kai, da yake basu san kunya ba, shi ne suke ganin kamar wani abin Aseef yake ɓoye masu, a zahirin gaskiya kuma kunyarsu yake ji yasa yake kasa haɗa ido da su, shi kansa ya rasa me yake damunsa da yasa baya iya haɗa ido da su ɗin. TO FA BABBAR MAGANA, ME YASA ASEEF KE JIN KUNYA KENAN?.
Chapter 11 · 0% Book details