← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 121

Sashe 74

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To na dai'na kema ki dai'na, amma kuma ai kece kika sakani kuka, na ce miki ki dai'na yi mini shiru idan muna waya, amma sai ki yi ta yin shiru, to idan kin yi shirun tunanin waye kike yi?" Sarkin kishi ba, ta faɗa a ranta, akwai shi da bala'in kishi kamar me, ko Imran ta kira a waya suka jima suna hira sai ya yi ta yi mata faɗa wai shi baya son ta jima tana hira da kowa sai shi kaɗai, baya son kishiya, komai nashi daban ne, kada ta haɗa shi da kowa, duk da Imran yake yayanta shi baya son su jima suna hira, idan kana son kaga ɓacin ransa cikin ƙanƙanin lokaci ka ce mishi ga Akila da Irfan suna waya, tamkar zai yi hauka haka yake zama, har kuka yake yi mata akan baya so, shiyasa ya hanata zuwa gidan Abbi kwata kwata, da Imran ya ce suje, sai ta ce mishi kanta na ciwo ba zata iya zuwa ba, haka Imran da jelly suka tafi, ita kuma ta kwanta tana shan hira da sahibin nata har ya iso gareta, a takaice dai yanzu ya hanata zuwa gidan Abbi ne dan kada ta haɗu da Irfan, dan kishin bala'i, ya ce idan ta cigaba da kula Irfan sai ya harbe shi da bindiga kowa ma ya huta.

Wayyo Allah soyayya daÉ—i, Allah sarki Irfan, da a harbe shi da bindiga ba gara ta hakura ta dai'na kula shi ba?, Shiyasa ta hakura ta dai'na kusantar shi dan ya rayu.

Idan muka koma ɓangaren gidan Lion kuwa, After some hours, a hankali ta waro dara daran idanunta da suke jawur da su, kai tsaye sai cikin tsakiyar kwayar Amber eyes ɗin Brady dake saman bed ɗin nata, a haukace ta miƙe zaune, haushi ya daka mata yana mai ɗaga kai sama, kamshin Lion ya biyo, idan baku manta ba ta taɓa ɗaukar rigar sanyin Lion a ɗakin Imran, to dama kunsan karnika suna bin kamshin mutun ne, rigar Lion ya biyo zuwa ɗakin nata, ihu ta kurma cikin fitar hayyaci ta diro kasa daga saman gadon ta nufi waje, da farko bai yi niyar binta ba, dan shi kamshin Lion ya biyo, neman ta in da kamshin yake a ɗakin nata yake yi, bai bi ta kanta ba, amma ganin ta watsa a guje ta yi waje yasa ya rufa mata baya da gudun gaske.

A haukace ta nufi palon kasa, babu kowa hakan yasa ta nufi waje, gidan shiru, sai kurma ihu take yi, daidai lokacin motarsu ta danno kai cikin gidan, saura kaɗan Mark ya bi ta kanta, ga hadiri sosai a garin, iska ruwan sama ya dawo da su, a zafafe ya taka birki wadda sai da ya sanya kan Lion buguwa da jikin kujerar gaba na motar, dan a baya yake zaune, cikin ɓacin rai ya ɗago kansa dan ya ga me yasa Mark ya taka birki haka, a lokacin ita kuma ta bugu da jikin gabatar motar tana ƙoƙarin zubewa kasa, rai a matukar ɓace ya buɗe kofar motar ya fito da nufin ya yi ball da ita, dan bai san me ya biyota ya sa ta shiga gabansu a haka ba, da shi ne ke tuka motar nan a cewarsa bi ta kanta zai yi dan bata da hankali.

Yana fitowa ya nufeta, cikin ɓacin rai ya damki gashin kanta tare da miƙar da ita tsaye yana ƙoƙarin yin wurgi da ita, dan tana yawan shiga harkarsa, daidai lokacin Brady ya kariso waje, haka zalika Areef da Aseef, daidai lokacin suka fito da sauri dan jin ihunta da suka yi, shi ne suka fito suga menene ya same ta.

Da gudun gaske Brady ya yi kanta da nufin cizo, a haukace ta damko kirjin Lion ɗin da hannayenta dukka biyu, ta kankame shi sosai tana ihu, wani irin yanayi mara misaltuwa yaji a jikinsa, daga kansa har izuwa tafin kafarsa sai da ta amsa, domin kuwa ɓul ɓul ɗin breast nasa ta damko bata sani ba, ta riƙesu sosai, ga shi sai faman cusa kanta a kirjin nasa take yi tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, cak ya ji duniya ta tsaya mishi, ya kasa dakatar da Brady dake ƙoƙarin cizonta, ya kuma kasa yin wurgi da ita da ya yi niyar yi ɗin, Mark dake cikin mota yana kallon me yake faruwa, cikin sauri ya cire wannan black glass ɗin nasa yana kara zaro dara daran hezal eyes nasa, duk sauran sojojin dake gidan ido suka zaro suna kallon ogan nasu, abin da ko a mafarki basu taɓa yin gigin mafarkin mace zata taɓa shi bai taketa har sai ta kasa motsi ta mutu ba, sai ga shi yau a zahiri da rana tsaka a gaban kowa, mace ta rungume shi har haka ba tare da ya yi wurgi da ita ba, Allah ne kaɗai yasan adadin mata nawa ya yi kwallo da su da suka yi gigin yunkurin taɓa shi, basu ma kai ga taɓa jikin nasa ba, yunkuri kawai suka yi, ya take su, babu macen or Namiji bayan TRIPLETS da suka taɓa yi mishi makamancin abin da Rimsha ta yi mishi, fusataccen fuskarsa mai raza mutane ne ma ke hana wasu kusantar shi, amma da alama ita wannan yarinya bata san waye ta runguma ba, duk wannan tunanin sojojinsa suke yi a cikin zuƙatansu.

Shi kuma Aseef da ya ga da gaske Brady cizonta zai yi, sai ya daka mishi tsawa da turanci, munafukin kare mafaɗaci, yana jin tsawar Aseef ya yi wani irin girgiza tare da daka tsalle ya haye jikin Lion ɗin, ya sauƙe mata bindinsa a bayanta, a lokacin kuma Lion ɗin ya daka mata wani mahaukacin tsawa a kan ta sake shi, ya yi maganar tare da yakaceta daga jikin nasa ya yi wurgi da ita gefe guda, wani irin wahalallen ihu ta saki dan ta bugu, da sauri Brady ya diro kasa daga jikin nasa ya nufeta, dan a nasa ilimin tun da Lion ya yi mata hakan to mai laifi ce ita.

Ganin Brady ya yi kanta yasa ta kurma wani razanannen ihu tare da miƙewa ta watsawa a guje ta nufi waje, ita da kanta bata san in da ta nufa ba, taku biyu Areef ya yi ya riƙota, dan ya lura ta fita a hayyacinta sosai, kankame shi ta yi idanunta a datse gam, tamkar zata fashe su, sai kuka take yi, abin gwanin ban tausayi.

Ganin Areef ya rungumeta yasa Brady ya dawo jikin Lion ya ɗane abinsa yana wani girgiza, wucewa Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake juyowa in da suke ba, ya shige cikin palo, har lokacin kuma Brady na jikinsa, rarrashinta Areef ya fara yi tare da bata hakuri, ba ƙaramin tausayi ta bawa Aseef ba, da sauri shima ya kariso wajen suka haɗu suna rarrashinta, da kyar suka samu ta yi shiru tare da lafewa a kirjin Areef ɗin tana shasshekar kuka, gabaɗaya sojojin dake gidan burinsu ɗaya, shi ne su san wace ce ita, dan kansu ya ɗaure sosai, me yasa su Areef suke rarrashinta har haka? A iya saninsu da TRIPLETS kwata kwata basu son mata, basu son kowa, to wace ce ita? Shi ne abin da kawai suke son sani, Mark ma fitowa ya yi ya nufi cikin gida.

ÆŠaukarta Areef ya yi suka wuce zuwa palo, har lokacin baiwar Allah jikinta sai kerma yake yi, suna shiga palo kuma suka isko su Lucky da suka fito daga bedroom na Areef yanzu, kara kankame Areef É—in ta yi sosai tana sake sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

"Aseef ka ɗaure karnikan nan, kuma ya kamata a dai'na kwancesu tun da tana tsoronsu, a bari a hankali hankali har sai ta dai'na tsoronsu, sai a rinƙa sakesu". Cewar Areef, Okey Aseef ya amsa da shi, tamkar karnikan sun ji abin da Areef ɗin ya ce na a ɗaure su, da gudu suka watsa suka yi waje dan kada ya ɗaure su ɗin, sai kiransu yake yi suka ki kula shi, suma sun fi son a barsu su sakata su wala abinsu, su shiga ko'ina su fito, su yi ɓarna son ransu.

Binsu wajen ya yi, da kyar ya samu ya yi musu dabara ya ɗauresu ya dawo, da kyar ta yarda ta rabu da jikin Areef ta koma saman sofa ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, "Our Queen ya kamata ki dai'na wannan tsoron naki, dan kinga matar GAR muke fatan ki zama, bai kamata ace kina da tsoro har haka ba, kuma shi Brady da kike gani, ina mai tabbatar miki da cewa Lion ba zai taɓa rabuwa da wannan karen ba, sai dai mutuwa ta raba su, shi ya reni kayansa, yana son shi fiye da tunaninki, to is better ki daina jin tsoronsa".

Shiru ta yi tana tunanin wai shin waye ta rungume da farko ne? A tunaninta Areef ne, sai kuma yanzu ta fara tunanin tamkar jikin ba É—aya dana Areef ba, wancan jikinsa tafi cika sosai, sai yanzu abubuwan suke dawo mata.

Shiru suka zuba mata idanu suna kallonta, shi Aseef ma daga barci ya taso, duk jikinsa a mace, a ɓangaren Lion kuwa, yana shiga bedroom nasa toilet ya nufa, har lokacin Brady na tare da shi, yaki barinsa.

Wanka ya yi tare da Bradyn, suka fito, duk in da ya saka kafarsa shi ma Brady sai ya saka nasa, kamar wasu twins, dama kwana biyu ai sun yi missed na juna, Brady sai Lion, Lion sai Brady, mutu ka raba.

Yana tsaka da sanya kaya ruwansa kamar da bakin kwarya ta kece, shiryawa ya yi cikin wani ɗan ƙaramin shot mai irin kama jikin nan, launin sky blue, sai ƴar singlet fara tas, ba ƙaramin daɗin ruwan saman nan ya ji ba, dan garin akwai zafi sosai, kwana biyu dama ba'ayi ruwan ba, da alama damunar ta fara ja baya ne, kun san shi dama da son tsayawa a balcony yana kallon zuban ruwan sama, yau ma hakan ce ta faru, bayan ya gama shi kai tsaye ya nufi balcony, sai tsalle Brady yake yi, da alama shi ma ya ji daɗin ruwan saman.
Chapter 74 · 0% Book details