← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 121

Sashe 65

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ma kaÉ—an ya gutsira ya fara tauna, sai murmushi take yi, ya sake kai mata bakinta ta gutsira, da haka haka ya yi ta bata a baki har ta cinye tas. "In karo miki wani ne?" Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, jinjina mata kai ya yi tare da manna mata sumbata a goshinta yana faÉ—in "Muje yawo ne baby?" "Daddy yawo kuma a ina?" Shiru ya É—an yi kafin ya ce "Gidan yayana Hassan da kuma yawo a gari, wajen hutawa, wajen wasanni da sauransu". "Daddy dama kana da wani yaya ne bayan Abbi?" GyaÉ—a mata kai ya yi yana faÉ—in "E ai Abbi ma ba shi bane babba, baban Imran shi ne babba, shi ma kafin shi akwai wadda ya rasu Abdulkarim, sai Abba sannan Abbi, bayan su ina da yayyu biyu, Hassan da Hossain, bamu san in da Hossain yake ba, ya guje mu, shi kuma yaya Hassan gidansa na nan Kaduna, bana son zuwa gidan ne, amma yau dan saboda ke zan je, zan kai ki wajen shi, sai dai kuma duk abin da matarsa zata ce miki, ki yi mata shiru kawai, akwai ta da surutu da baki kamar Sadiya". Ya kai karshen maganar cikin zolaya, dan shi da kansa yasan Aunty tana da halin kirki, idan yana son tsokanar tane sai ya ce ta cika yawan magana da shisshigi.

Ƴar dariya ta yi. "Daddy ai ita Aunty bata da yawan magana". Shafa face nata ya yi tare da miƙewa ya ɗauko mata wasu kaya masu shegen kyau, doguwar riga ce da mayafinta, da kansa ya sanya mata tare da riƙo hannunta suka fita, shi dama already a shirya yake, palon Abbi suka nufa, sun yi kyau sosai sai ramar nan da suka yi ne ta so ta ɓata musu kwalliyar nasu.

Aunty ce kaɗai a palo tana shirya musu breakfast, ganinsu yasa ta saki wani ƙayatattacen murmushi tana yi musu barka da safiya, ita kuma Ommu tana can bedroom nata dan bata bar gidan na, duk da Abbi ya saketa, tana nan bata motsa ba, shi kuma Abbi bai sake bi ta kanta ba, bai sake kula ta ba tamkar bai san tana nan ɗin ba.

"Sadiya É—auko mini key É—in motar yaya bari mu fita, daga nan ki sanar mishi na tafi gidan yaya Hassan". Da mamaki Aunty take kallon shi "Yaya Hassan kuma?" Ta maimaita a filli, gyaÉ—a mata kai ya yi, "Waye yaya Hassan É—in? Ko dai yaya babba ne?" Girgiza mata kai ya yi yana faÉ—in "A'a yaya babba daban, yaya Hassan daban, yaya Hassan shi ne ai É—an uwan yaya Hossain". Ba karamin ruwan mamaki ta sha ba, a ranta ta ce ko su nawa ne a wajen iyayen nasu Allah masani, wata kila ma akwai wasu da basu bayyana ba, amma to meyasa suka yi wannan uwar watsewa hakan? Ta tambayi kanta da kanta, tambayar kuma da bata da amsar shi.

Cike da tunani ta nufi sama dan ta É—auko mishi key É—in, shi kuma ya zaunar da babynsa a saman sofa dan kada ta wahala da tsayuwa. "Daddy palon nan yana wari". Ta yi maganar baiwar Allah tana toshe hanci, shi komai ta yi muguwar tausayi take bashi, Allah sarki kowa yasan ba halin ta bane, ita da ko magana bata cika yi sosai ba, daga to sai a'a, da wuya kaji ta É—aga murya tana magana, kusa da ita ya dawo ya zauna, cikin tsantsar kaunarta ya fara rarrashinta akan ta daure bari Aunty ta kawo mishi key É—in su tafi, ba dan ta so ba ta amsa mishi da to, haka suka zauna sai faman toshe hanci take yi har Aunty ta fito.

Tun bata kariso wajen da suke ba, ya miƙe cikin sauri ya nufeta, key ɗin ya karɓa bai tsaya ya jira abin da zata ce ba, cikin sauri ya zo ya kama hannunta suka fita, yana jiyo sautin muryar Aunty tana faɗin "Abbi ya ce ka gaida mishi da yaya Hassan ɗin". A waje ya amsa mata da to, baya son duk wani abin da zai ɗaga wa babynsa hankali har ya sakata amai, ita kuma Aunty komawa ta yi saman table ta cigaba da abin da take yi, ita ma tana fama da ɗan ƙaramin cikinta, sai dai ita nata babu laulayi, ta yi sa'a, sai barci da kasala da yake sakata, bayan haka babu wani abin, ko amai bata yi har sai idan bata yi sa'a ba ta ci ta ƙoshi sosai.

Idan muka koma ɓangaren Hanan, sosai take jin daɗin zamanta a gidan Abbi, yanzu shirye shiryen sakata a makaranta ake yi, har wani fresh ta kara abinta, Abbi ya saya mata waya, dama da suka je Katsina ta karɓi number Yusuf wadda ya kasance shi ne kaɗai mai waya a gidan, shi ɗin ma bai jima da saya ba, daya ga ya sami riba sosai a shagon nasa ne, sai ya sayeta, irin waƴan nan Tecno nan ne, masu babban kai ɗin nan, shi kam Sadiq ko a jikinsa, bai wani damu da sayan waya ba, shi dai burinsa yaga ya ginawa mahaifiyarsa gida ta bar wannan gida na amarya gidan gori kullum, ko kayan sakawa bai damu da ya saya ya saka a jikinsa ba, tara kuɗinsa yake yi ba ji ba gani, shi dai ya yi gini su fita daga wannan gida ko hankalinsa zai kwanta, da yake niyarsa mai kyau ce, Allah yana dafa mishi, yana samu ba karya, ko wace rana yana iya samun 2000, or 1500, or 1000 haka, idan ka ganshi ya kashe kuɗi, to Mahaifiyar tasu ya sayawa wani abin, ita kuma Hanan babban waya mai kyau da tsada Abbi ya saya mata, tana kiran Yusuf su gaisa da su maman Sadiq har shi kansa Sadiq ɗin, a hankali hankali Aunty ke koya mata ƴadda zata yi amfani da wayar, ita kuwa Ommu kamar yadda kuka sani ne, bata fita waje kwata kwata, idan kunganta a palo, to ko dai zata ɗauki abinci, ko kuma zata fita ta tafi unguwa, bacin haka kullum tana maƙale a cikin ɗaki kamar wata mara gaskiya, haka zalika kullum sai ta kira Umaisha a kan batun kuɗin nan, dan tana son komawa in da ta fito, tana son ta je ta kwaso mafi soyowar ƴaƴa a gareta, ita kuma Umaisha A'afia ta hanata ɗaukar kuɗin, ga shi Ommu ta takura mata, baiwar Allah ta rasa ya zata yi, har ƴar rama ta yi, shi kuma Akil ya zuba musu idanu yana kallonsu tun da taki gaya mishi abin da yake faruwa, bai tuna mata ya sani ba, dan idan ya kuskura ya nuna mata ya sani, zata fahimci kamar yana biniyarta ne, abin zai zama kaman zargi a tsakaninsu, zata daina yarda da shi, haka zalika ko magana take yi da ƴan uwanta, zata rinƙa shiga ruɗu da damuwar ko dai yana kallonta, ko dai yana jinta, bazata sake yarda ta saki jiki ta yi magana da wani nata ba, dan zata tunanin zai ji ta, hakan ba karamar matsala zata haifar musu ba, shiyasa ya yi shiru, kuma yana son fitar da ita daga cikin damuwar da take ciki, yana son ta faɗa mishi da bakinta sai ya bata mafita, amma ita kuma ta kafe ta ki faɗa, dan Ommu ta ce mata idan ta faɗa zai yi mata gori, shi ne ta adana sirrinta kada ya yi mata gori.

A ɓangaren Irfan kuwa, har yanzu yana fama da dakon soyayyar Akila, sai dai ya fawwalawa Allah komai, baya kiranta a waya, dan ko ya kira ba zai same ta ba, kuma kunsan bai isa ya ce zai je gidansu ba, Hjy Umaiya ba zata yarda ba, kullum yana Sallah yana roƙan Allah da ya zaɓa mishi abin da yafi zama mishi alkhari a rayuwarsa baki ɗaya, wani kayan haushi, kullum son Akila ninkuwa take yi a cikin zuciyarsa, bawan Allah duk ya rame, bai cika zuwa aiki bama, ya barwa Abbi companynsa, shi kuma Abbi bai kawo komai a ransa ba, ya yi tunanin abubuwa ne suka riƙe ɗan nasa, dan ya ce yana son ya cigaba da karatu, a tunanin Abbi shi ne yasa ya shiga busy kwana biyu, bai san cewa ɗan nasa faɗa yake ta faman yi da zuciyarsa ba.

Idan muka koma ɓangaren gidan Lion kuwa.

Sai dariya Rimsha take yi musu, abincin ta ɗebo a cikin spoon nata ta kaiwa Areef saitin ɗan bakinsa tana faɗin "Yaya Areef to ni tun da yaya Aseef ya cinye mini first spoon ɗin da ka bani, ni bari na baka nawa". Buɗe ɗan bakin nasa ya yi yana ƙoƙarin karɓa, da sauri Aseef ya matso ya karɓe yana faɗin "Kowa a cikin gidan nan ni ne zan rinƙa cin first spoon na shi, shi ma Lion ai ni yake fara bawa, dan haka kema ni zaki fara bawa". Duka Areef ya kai mishi, da sauri ya kauce yana dariya "Areef wlh idan ka taɓa ni yanzu ina da mai rama mini, zata shigar da kai kara court na gaya maka, dan ba zata yarda ko kuda ya taɓa ni bata yi mishi hukunci ba". Turo ɗan bakin nan Rimsha ta yi, a shagwaɓe ta ce "Yaya Areef buɗe baki bari na baka second spoon to, rabu da yaya Aseef ɗin nan, mun ɓata da shi".

Ba musu ya buɗe baki, ɗabowa ta yi ta kai mishi sai tin bakinsa, karɓa ya yi tare da karɓar spoon ɗin nata, a hankali ya fara taunar abincin, ɗebowa ya yi shima ya kawo mata saitin bakinta, bata kai ga karɓa ba, Aseef ya tura mata nashi da ya ɗebo yana faɗin "Nawa zata fara ci". Haushi kamar Areef ya kifa mishi mari, Aseef ba dai neman magana ba, ya iya kamar me, bayan ya zuba mata a bakin nata ne ya zare spoon ɗin ya sake ɗebar wani abincin tare da miƙewa ya nufi wajen Lion, binshi da idanu suka shi, shi Areef yasan in dai Aseef ne ya bawa Lion abu, to ko baya so zai ci, ita kuma Rimsha har ta fara tunanin yadda zai yi ball da spoon ɗin, bata san cewa Aseef pleasure sa bane.
Chapter 65 · 0% Book details