← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 121

Sashe 110

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umarni ya bata a kan ta buɗe idanunta, ba musu ta warosu a hankali, kai tsaye dai kan zobben ta sauke idanun nata, da sauri ta mayar da kallonta kan face nasa, cool murmushi ya sakar mata tare da ciro ring ɗin ya kama hannunta ya sanya mata a yatsanta na kusa da babba na tsakiya, wani irin sihirtaccen kyau hannun nata ya kara yi, kai hannun nata saitin ɗan bakinsa ya yi tare da sumbatarta, wani irin shock suka ji dukkansu biyu, miƙewa ya yi tare da jingina da jikin motar yana lumshe idanu.

"My shagwaɓati ka kawo naka ring ɗin na saka maka mana?". Ta faɗa tana kai hannun nata kusan bakinta ta sumbaci zobben, "No ni bana sanya ring ai, amma zan saka na auren mu, a kasarmu idan ka saka ring yana nufin kai mai aure ne, abin da ya sanya kema na saka miki, dan naga ku a nan kuma sawa ne, naga akwai a hannun our Rimsha, to shiyasa kema na saka miki, amma ni a'a bana ma sanyawa, baya burgeni, chain kawai nake sakawa, shi ma da ne yanzu bana sakawa sai na mummynmu ne kawai a wuyana". Ya kai karshen maganar tare da fito mata da sarkar mum ɗin nasu dan ta gani, zubawa sarkar idanu ta yi tana kallon shi, tabbas ta taɓa ganin irin wannan sarka sak, babu banbanci ko kaɗan, to a ina? Shiru ta yi tana tunani, shi kuma mayar da sarkar ya yi yana faɗin "Ina su Prof?" Suna ciki ta bashi amsa yayin da take ƙoƙarin tunani wai daga ina ta taɓa ganin wannan sarka, sai ya yi mata kamar a hoton kakansu Naurat ta taɓa gani, yes tabbas a wuyar Naurat ta taɓa ganin wannan sarkar, akwai wani hoton Naurat ita da kanwarta autarsu, so dukkansu ita da kanwar nata suna sanye da irin sarkar nan.

"Okey muje bari na gaishe da Ammie sai nazo na koma ko?" "Koma wa kuma?" Ta tambaya tana turo baki, hannu yasa ya shafa lips nata na kasa yana faɗin "Wai ke bana ce ki dai'na turo mini ɗan bakin nan ba? Very soon zan sha kayana ki cihaba", Kama hannun nasa ta yi tana kallon kyawawan fararen yatsunsa, ga farcensa sai kyalli suke yi farare tas, ga wani kayatatcen brawn ɗin gashi kwance a saman yatsun nasa, haka zalika hannunsa, gabaɗaya kyawawan kwantatcen gashi ne sosai a wajen, "My shagwaɓati wlh yatsun hannunka suna yi mini kyau over". "To meyasa zaki wahalar da kanki wajen cewa suna yi miki kyau bayan mallakinki ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da sumbatar yatsun nasa tana murmushi, wannan sumbata har cikin ransa ya jita, lumshe idanu ya yi yana mai sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

"Muje ko?" Ta faÉ—a tare da sakin hannun nasa ta yi gaba, zura hannayen nasa ya yi a cikin aljihunsa ya bi bayanta yana kallon yadda take tafiya a nitse kamar bata son taka kasa, ta kara tafiya da imaninsa ba kaÉ—an ba.

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin palon, zaune ta isko Ammie, Imran, Akil suna hira, iso ta yi mishi tare da wucewa kusa da Imran ta zauna, karisowa ciki ya yi, Imran ya fara miƙawa hannu kafin Akil, da yake shi bai san al'adar Hausawa ba sai nasu ya sani, sai ya miƙawa Ammie ma hanu dansu gaisa, bata yi mamaki ba, suma su Imran basu yi mamaki ba, sunma ga kokarin sa da bai ce zai rungumi Ammien bama, dan su runguma a wajensu kamar nuna murna da ganin mutun ne ba wani abin ba, Akila dai ta sha mamaki, kuma ta yi nadama da bata gaya mishi yadda zai yi wa Ammie ba idan ya shigo.

Ba musu Ammie ta miƙa mishi hannu suka gaisa dan ita ma mijin nata Baturen ne, duk kanwar ja ce, Bismillah ta yi mishi da ya zauna saman sofa, zama ya yi kafin su fara ƴan tattaunawa, a haka Abba ya sauko kasa ya same su, ya yi shirin zuwa office, Umaisha tana kitchen Jelly tana barci, Umaishar ta ce lallai sai ta taya Ammie aiki, shi ne ta shiga tana ɗan goge goge.

Ganin Abba yasa ya miƙe ya bashi hannu, ba musu Abba ya miƙa mishi hannu suka gaisa, ɗan rungume Abban kaɗan ya yi kamar yadda suka saba yi a kasarsu, shi ma Abban mayar mishi da martanin hakan ya yi dan duk ɗaya ne, da gani ba tambaya, komawa ya yi ya zauna abinsa yana kallon heartbeat nasa, sai murmushi take yi.

Abba ne ya tambayi Imran a ina suka samo Bature ruwansu mummynsu wato Na'urat kuma? Dan duk ɗaya ne, kai tsaye Imra ya ce mishi saurayin Akila ne, shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce " Saurayin Akila kuma?" Jinjina mishi kai Imran ɗin ya yi ba tare da ya wani damu ba. "Akila kam ai na riga da nayi mata miji". "What?!!" Imran ya faɗa tare da miƙewa, ita kan ta Ammie sai da ta miƙe, Akil ma dai tambaya ya yi akan miji kuma,? Shi ma Aseef miƙewa ya yi da yake da turanci suka yi maganar.

"Abba ban gane ka yi wa Akila miji ba? Waye ka bata to? Ka yi mana bayani". Cewar Imran, yana magana yana kallon Aseef da ya tsaresu da idanu, yasan idan hakan ta tabbata lallai akwai yaki kenan, babbar magana.

"E Imran kamar yadda ka ji dai haka ne, kwana uku da suka wuce Deen da Maik sun same ni a office akan maganar Irfan da Akila suna son junansu, na yi murna sosai, na kuma bawa Irfan aurenta, Friday mai zuwa za'a É—aura aure, ranar Wednesday gabaÉ—aya iyalan gidan Deen zasu tattaro su dawo nan dan ayi komai waje guda, sai bayan biki zasu koma, Batula tana zuwa jibi, mantawa nayi ban gaya muku ba, amma an gama shirya komai ai". Tashin sense da ba'a saka mishi date, zube gwiwowinsa a kasa Aseef ya yi, nan take hawaye suka fara wanke mishi fuska cikin sanyin murya ya ce "Please Abba kada ka yi hakan, am very sure heartbeat bata son Irfan, ni ba zan iya rayuwa ba idan ka hana ni ita, please and please ka taimake mu, na san ita ma heartbeat ba zata iya rayuwa da kowa ba sai ni, wlh muna son junanmu over, ni kayi mini duk abin da zaka yi mini amma kada ka hanani auren Heartbeat, ba zan iya jurewa ba, ba kuma zan iya É—auka ba". Yana magana hawaye wani na bin wani, Ammie bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncinta ba ita ma, dan dole Aseef ya bawa mutun tausayi a yanayin yadda yake magana.

Zubewa kasa ita ma Akilar ta yi, tana kuka tamkar ba gobe, hawaye wani na bin wani "Abba wlh ni bana soyayya da yaya Irfan, ni Heartbeat nake so, dan Allah kada ka aura mini yaya Irfan, Allah bana son shi". Imran sarkin saurin kuka tuni ya fara yi musu hawaye, dan shi yasan menene soyayya, yasan wahalarta, ya kuma É—anÉ—ana, Akil kuwa tunani yake yi tun da Akila ta buÉ—e baki ta ce bata son Irfan to gaskiya bai ga dalilin da zaisa a aure mata shi ba, aure ba abin wasa bane, ba abu ne da ake yin shi shekara É—aya ko biyu ya kare ba, rayuwa ce ta har abada, zama da wadda baka so yafi komai wahala da azaba a duniyar nan, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku dai'na yiwa yara dole, zama da wanda zuciya bata so babbar barazace ga rayuwar yarinya, ya kan sakata ta yi abubun da kowa zai zo ya yi dana sani daga baya, to maganin bari kada asoma, ku sani dai Allah zai tambayeku.

"Abba dan Allah ka duba wannan magana da kyau". Cewar Imran. "Imran ya kake so na yi to? Deen fa nace maka, bappanku Deen fa!, Shi da kansa ya zo ya nemanwa Irfan aurenta, yana da damar da zai aurawa Irfan É—in ita ko ban sani ba, ba shi ya É—aura muku aure ba? Nasan time da ya É—aura muku ne? Ai ban sani ba, to haka ita ma Akilar zai iya aurar da ita ba tare da sanina ba, kuma bani da abin cewa, amma duk da haka ya wanke kafa ya zo ya nemi auren ta, na kuma É—auka na bashi, yau saura kwana takwas kenan a É—aura auren, kenan so kuke nace mishi na fasa bashi wani na waje zan bawa ne ko yaya?". Shiru palon ya yi, ban da shasshekar kuka Heartbeat and Heartbeat babu wani abin da yake tashi, su Imran dai sun rasa bakin magana, sun san ba ta yadda za'ayi Abba ya ce wa Abbi ya fasa bawa Irfan wani daga waje zai bamawa, hakan sam ba abune mai yiwuwa ba.

Suna tsaka da tunani basu ankara ba sai ganin Aseef suka yi ya sulale kasa sumamme, ihu Akila ta kurma ta yi kansa tana ambatar sunansa Heartbeat!! Heartbeat, kamata Akil ya yi ya rungumeta a jikinsa tare da bubbuga bayanta dan ta samu ta natsu.

Da gudu Umaisha ta fito daga cikin kitchen dan ta zo taga me yake faruwa ake ihu haka, Abba, Imran a zafafe suka yi kansa, sai kiran sunansa Aseef, Aseef Imran yake yi, amma ina shiru, ruwa Ammie ta ɗauko a fridge Abba ya karɓa ya tarbo a hannu ya shafa mishi a fuska, shi kuma Akil sama ya wuce da Akila dan kada ta karawa Aseef ɗin zafi a kan zafi, ga ciwo ga kuma kukanta, wucewa Abba ya yi yana faɗin "Ana jiransa a office tun ɗazun, bari ya je". Okey suka amsa mishi da shi, sauri yake yi sosai, kuma baya son tsayawa ne, dan baya son ganin halin da Aseef da Akila suke ciki, saboda yasan duk wuya duk daɗi ba zai canza magana ba, ba zai iya hana Irfan ya ɗauki Akila ya bawa wani bare ba, amma fa har can kasar zuciyarsa shi ma yana son bawa ƴar tasa zaɓinta, amma ba dama ne kawai, bashi da yadda zai yi, jini ba karya ba.
Chapter 110 · 0% Book details