← Book details Triplets Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 121

Sashe 78

Triplets Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun kammala cin abincin Areef ya riƙo hannunta yana kallon jakar bayanta, suka nufi waje, shi kuma Aseef sai da ya koma bedroom nasa ya ɗauko wayarsa da key ɗin mota ya fito, a cikin motar ya iskosu zaune suna jiransa, sai hira suke zubawa kamar wasu kawaye, mazaunin driver ya shiga, bai kai ga tada motar ba sai ga Imran da jelly su fito, gidan baya suka shiga, Areef na ya kirasu akan su tafi tare, suna shiga Aseef ya yi wa motar key, gaisuwa Rimsha ta fara ɗagawa Imran, da fara'a sosai a kan face nasa ya amsa, tare da tambayarta ya take, ita ma sai murmushi take yi ta amsa.

"Aunty jalila ina kwana?" Ta É—agawa jelly gaisuwa, cikin mutunci Jellyn ta amsa mata, da alama ta natsu ne, tana bala'in tsoron TRIPLETS, bare ma kuma da taga Rimshar na zaune kusa da Areef É—in a kujerar gaba, sai ta kara natsuwa sit kamar bata a wajen, shi kansa Imran sai da ya sha ruwan mamakin me yasa ta natsu sit daga shigowarsu cikin motar, kamar zai yi magana sai kuma ya danne, sai wani kankame shi take yi tana satar kallon Areef da tamkar bai san da zamanta a cikin motar ba, idan ta kalli Areef É—in sai ta sake juyawa ga Aseef ta kasa banbance waye ne a cikinsu ya yi yunkurin marinta rannan.

Sai hira Areef da Rimsha suke yi suna dariya har suka iso school ɗin, shi kam Aseef yana tuƙi yana latsa waya, Heartbeat na kashe shi da love, tana kudundune a cikin bargo ta lafe a gado sai zuba mishi iya shege take yi, duk ya birkice mata, da kyar ma ya iya tuƙa motar har suka isa. A parking space na makarantar suka tsaya, dawo da kallonsa kan Rimsha Areef ya yi cikin sanyin murya ya fara magana "Ki kula mana da kanki sosai, zamu dawo mu ɗauke ki idan time ya yi, ki je class mu bari mu duba shigaban makarantar naku".

Da yake ba da wannan motar ta saba zuwa ba, sai Anaya bata san ita aka kawo ba, motar Imran Anaya ta sani, tana class, amma kafin ta shiga class É—in taga tsayuwar motar, sai dai bata kai kallonta wajen ba, dan tasan bata san motar ba, da alama ita ma Anaya bata shiga abin da bai shafe ta ba.

"Yaya Areef zan yi kewarku sosai". Ta faɗa a ɗan shagwaɓe, leƙo face nata ya yi, cikin zolaya ya ce "Za'ayi kewarmu ne ko za'ayi kewar Saif?" Rufe fuska ta yi da hannayenta tana faɗin "A'a dukkanku dai". "Au ashe dai shi ma Saif za'ayi kewarsa kenan?" Cewar Aseef, shi ma cikin zolaya ya yi maganar, "E mana yaya Aseef, zan yi kewarsa sosai, dan ma na ganshi ɗazun kafin ya fita". Murmushi suka yi a tare har da Imran, a nan ne kuma jelly ta fahimci ita Rimsha ba son Imran take yi ba, tana da wadda take so kenan, gabaɗaya sai ta ji babu daɗi abin da ta yi mata, dama an ce rashin sani ya fi dare duhu, to ita jelly abin da ya faru kenan tsakaninta da Rimshan tashin sani.

Sumbata Areef ya yi mata a lallausan kumatunta yana faÉ—in "Nima zan yi kewarki sosai, ina jin kamar ba zan iya wuni guda ban ganki ba". Wani irin kunya ta ji, su kuma kun sani ba sai na sake faÉ—a ba, sumbatar mutun or kiss ba wani abu bane a wajensu ga koma waye, shiyasa ma ya sumbace ta É—in.
Ganin ta yi shiru ne yasa ya ce "Ba zaki sumbace ni ba nima? Haka zaki tafi mu rabu?". Bata da zaɓi, dole ita ma ta juya ta sumbace shi a kumatu, tana kokarin cewa Areef ya fita bari ita ma ta fita dan ita ce a ciki, sai ta ji saukar wani sumbata a kumatunta na Aseef, juyowa shi ma ta yi tare da bashi sumbatar, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe kofar motar ya fita yana faɗa mata ta kula musu da kanta sosai.

Kusan a tare mazan suka fita daga motar, dan su je office ɗin shugaban makarantar, ita kuma jelly tana ciki tana jiransu, Rimsha na ƙoƙarin fita jelly ta riƙo hannunta tare da ce mata "Ki yi hakuri da abubuwan da suka faru kin ji Rimsha?". Cool murmushi ta sakar mata kafin ta ce "Babu komai Aunty Jalila, ni daman ban riƙe ki a cikin zuciyata ba, nasan rashin fahimta ce". Rungumar juna suka yi kafin nan ta saketa ta fita tana yi mata bye bye, da ido jelly take binta da shi babu ko kyaftawa, yau taga Rimsha ta yi mata kama da daddynta, Allah sarki bata san ƴar uwarta bace, dole akwai kama ta jini.

Class nasu ta nufa, da sallama kasa kasa ta shiga, wani ihu Anaya ta yi tare da tahowa da gudu ta rungumeta tana dariya, "Dama na ce yau In Sha Allah zaki zo". Ita ma dariyar take yi, Æ´an class sai binsu da kallo suke yi, dan sun san halinsu a tare, Anaya na bala'in Kaunar Rimsha haka ita ma Rimshar.

Wucewa suka yi suka je suka zauna a mazauninsu, dama kowa da kujerarsa, sai dai suna kusa sosai da juna, "Rimsha ya kamata ki je ki roƙi uncles su baki text ɗin da suka wuce daga na last Monday zuwa yau fa ki yi, dan kinga suna da yawa, almost text 7 fa". Cewar Anaya.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Anaya ni English and mathematics nafi ji, yanzu dai ki rakani office ɗin Mr Emmanuel bari na roƙe shi ya bani English na yi, wlh ranar da kika gaya mini anyi text na English da kyar na iya barci". Murmushi ta yi tana faɗin "Kai Rimsha saboda English ɗin kika fi iyawa ba? Dole ki damu ai, amma gaskiya ni ba zan je office ɗin Mr Emmanuel ba, dan kin san halinsa sarai da bala'i, yanzu idan munje mu biyu ma yana iya kin baki ya ce waye ya ce muzo mu biyu, kin san fa ba'a shiga mishi office bibbiyu, mutun ɗaya ne, kema ki yi addu'a kafin ki je, bakin mugu azzalumi, sannan kuma uncle Faisal na jiranki, ba idan ya kiraki baki ɗauka ba, zaki yi bayani". Guntun tsaki ta ja tare da miƙewa ta miƙawa Anaya ɗin school bag nata tana turo baki ta nufi waje, haushin uncle Faisal ɗin nan take ji, kamar ta yi ta kifa mishi mari, a wawa, wawa take kallon shi ma, dan kawai yana nan shiru shiru da shi.

Tana fita ta hango motar su Areef ya bar makarantar, ajiyar zuciya ta sauke tare da wucewa ta nufi office ɗin, a bakin kofa ta yi excuse kasa kasa tare da tura kofar ta shiga, wani irin mahaukacin birki ta ja babu shiri, zaro idanuwanta waje ta yi tana kallon abin da kwakwalwarta ya kasa ɗauka, Mr Emmanuel tare da wata student ƴar ss 2 ne ko 3 suna romancing na juna, ya cire mata rigar uniform yana wasa da breast nata, ita kuma yarinyar sai wasa da gabansa take yi, matashiyar budurwa ce wadda zata iya kai 19 to 20 years haka, gata kyakkyawa ba laifi, fara ce tas, kuma da alama musulma ce, dan kunsan hasken musulci baya ɓuya a fuskar bawa.

A wani irin razane suka É—augo kai jin an buÉ—e kofar, guntun tsaki yarinyar ya ja tare da É—aukar rigar uniform nata tana maidawa jikinta, da gudu Rimsha ta juya tana ruwan hawaye, to me abin kuka? Binta da kallo Mr Emmanuel ya yi, ita kuma yarinyar sai faman mayar da kayanta take yi, damko rigar uniform É—in nata ya yi, cikin murya mai kama da na Æ´an shaye shayen da turanci ya ce "Ina zaki je Fadila? Ai ban gama ba". Kara jan dogon tsaki ta yi tana faÉ—in "Mr Emmanuel ka bari sai an shiga class zan sato hanya nazo". Shafa breast É—in nata dake tsaye kyam ya yi tare da lumshe idanu, kamar wani tsohon maye yana wani lashe baki. Ba dan ya so ba ya barta ta fice daga office É—in bayan ta gama mayar da kayanta kenan.

Tana fita ya lumshe idanu yana tunano Rimsha a cikin zuciyarsa, tun ranar da ya ɗaura waƴan nan shegun idanu nasa a kanta ita da Anaya yake haɗiye yawu, ya yi ƙoƙarin jan Anaya da wannan shashancin, sai dai bai sami dama ba, dan kullum tana tare da Rimsha, kuma kullum suna cikin class basu cika fita sosai ba, yasan idan ya fara da Anaya zai yi nasara, dan da alama bata da ilimin addini sosai, kuma akwai yarinta sosai a kanta, ita kuma Rimsha ba sai na gaya muku ba, ta san komai dan mummynsu babu kunya babu ɓoye ɓoye ta sanar musu da komai, ta faɗaɗa musu ilimi dan gujewa irin hakan, shiyasa ake son uwa ta rinƙa jan ƴaƴanta a jiki, ya zama daga bakinta suka san komai ba daga bakin kawaye or wani waje ba, baya son idan ya tinkari Anaya Rimsha ta sani, ya fi son kafin ta sani ya rigada ya lalata Anaya ɗin, Shiyasa bai yi wargin tinkararsu lokacin da suke tare ba, ya bari yana jiran wata ƴar dama, lokacin da Rimsha ta daina zuwa school, kwata kwata baya samun damar ganin Anaya ɗin, sai ya zo class nasu karantar da su, bata fitowa, bata da abokiyar hira, da an tashi breakfast ko ya aika a kirata ba zasu ganta ba, a dokar makarantar kuma ba'a yarda wani malami ya kira ɗaliba lokacin da suke class ba, sai dai ita ɗalibar ta fita a sace, idan aka kamata kuma zata yi bayani, a takaice dai Mr Emmanuel Anaya yake son fara lalatawa kafin Rimsha, dan idan Rimsha ta san kudurinsa, zata zuga Anaya ta kuma tsawatar mata a kan kada ta yarda da shi, tsab ya gama karantarsu jira yake ya sami ƴar dama ya cinma burinsa.
Chapter 78 · 0% Book details