← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 161

Sashe 89

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan zainab arifah ta cabe magana tafara zaginta da turanci 'are u stupid?mani xaki na gayawa wann maganan dan nace ki kawo mana ruwa akan ban isa na aike ki bane komi
..baku san matsayina agidan na ba ko? toh ko wanda yake daure miki gindin a karkashina yake, inadan ibaad ne yasa kike ganin kamar kinfi karfin kowa..by the time kikasan matsayina awajensa u will know ure nothing kiwuce kije kideba mana ruwa...nala ta zugereta tanan, arifah ta tureta tacan..

ran ayaana ya baci sabida jan jan hannun ta da sukey da karfi ta fauce hannunta tace niki sakeni bazan je ba.

tace fada dani zakayi did u knw who i am..? u dont knw who i am i bet..toh kije ki tambaya ibaad din zai gaya miki i am his future wife
nd u ure just a village girl dayake taimakawa agidan nan

ayaana tafara kuka idonta a rufe tace Eh din yataimekeni wnn ba karya bane kekuma ai kowa yasan matsayinki
bakice kikace kinason shi ya tsumage ki? ni ai bansan wani matsayinki wajensa face haka ba..

da tsawa zainab Arifah tace kikace mene?

da bacin rai kulthum tace anty zainab stop shouting at her wai meta miki ne zakixo kina zaginta kina ture ta???

nala takai ma kulthum mari atsawace tace you...just shut up. ana magana kina saka magana kiga min yaran nan fa

sultana tasa ihu tace wallah kufita mana a daki inba haka sainaje na gaya ma hajiya uban waye ne bawanku da xa'aje adebo miki ruwa baza a debo din ba ai gaskiya ne yaya ibaad bayasonki, bamusan matsayinki ba sabida baki dashi..nd we dont care... toh wai ma ina ruwanki da ayaana kuma meta miki?

xuwa nala tay xata mari sultanan ita da kulthum din duka suka wani irin tureta akasa sai datay rolling suka tumu akanta suka fara kai mata duka..

ayaana ta razana sosai
tasa kuka me kara cikin firgice zata fita taje ta kira su ammi wani caraf zainab arifa ta riketa abkin kofa ta shakureta ayaanah tafara ihu tana cewa "kisakeni"..wani muryan makirci zainab arifahn tasaka tafarace mata ki memeta abunda kika gaya min...inke kin isa marar kunya...

tunda safiya takai sakon kan ibaad ya daure, yanata mamki meye kuma zai hada zainab arifah da ayana da zatace zata bugeta, da har kamar zai share tasharsu yaqi zuwa dakyar mujaheed dayasan zainab arifah bata kaunar ayanaah yay convincing dinsa suka taho sashen wani irin ihu da tirka tirkan fada da sukaji ya cika sashen yasaka safiya zamewa da gudu taje kiran su hajy mairo

da sauri suka haura sama zuciyar ibaad kamr zai fashe dayaga irin matsar da zainab arifah tama wuyan ayaana kamr wacce xata kasheta mujaheed yay sauri ya raba su ya ficcike zainab din ayana tafadi kasa tanata kuka

saiwani fixga xainab arifah take tana ɓarin karya tana cewa "wallh saikin memeta abunda kika gayamin" .mujahd yana riketa tana turashi tana cewa mujaheed let me go..inta cika marar kunya ta memeta abunda tagayamin can you imagine? har rainin yaran nan yakai su gaya min haka kawai ta fashe dawani irin makritccn kuka

ibaad tunda yaga haka yagane koma miye ne karya takeyi

he remain calm yaki sam yay ma kowa tsawa, dakin ya shiga direct ya samu su sultana har sun yaga ma nala riga cikin daka musu wani irin mugun kallo yace musu maza su fito waje..dakyar suka bambaro ajikinta kowa na hawaye suka fito daya bayan daya...jiki a sanyaye ayaana ta mike itama ta bisu suka sauka

kowa jikinshi a turmushi zainab arifah sai wani irin kukan makirci takeyi mujahedd yana riketa tana sake jiki ita da shi da kawartan da jikin ta duk yay tsami suka sauko kasa tare..

suna saukowa falon duka ibaad ya saka su ayana dukansu uku kneeling atsakiya..dede shigowar su hajiya kenan da ita da ammi babba da anty safeera

meye ke faruwa anan?
sultana? kulthum..kee ayana..me kukayi haka mezan gani

anty safeera tay sauri taxo jikin zainab arifah dake kan rabza kuka kamr ita aka taro aka daka

ammi babba already harta yanke hukuncin hakan ne ma
suka yanyane zainab arifah

anty safeera tace arifah what happen? meya hadaku fa yaran nan kike kuka haka.

da wani irin kukan makirci ta nuna ayaana tace anty safee kawai yarinyar nan nagani a falo tana kwance bata komi nace ta kawomin ruwan sha fa nida nala..shine taja min tsaki taje daki, shine fa nagaji muka bita saman dan muga whats taking her soo long daga tambayar yaran nan duka suka hargitso suna xagina...dede nan ta kara fashewa da kuka..

anty safee daga tambayar ruwa meya kawo maganan wai ibaad baya sona ya bugeni? kawai suka kama kawata suna dukanta..kuma wallh laifin yarinyar nan ce, ita bakuwa ma amma wai itace me bakin zagina su sulthana kuma suka goya mata baya mena taba musu...was i ever bad to u guys??

da wani irin bacin rai kulthum tace wallah karya kikeyi, kiji tsoron Allah kisan zaki mutu anty zainab wallah karya kike mana..sultana ta fashe da kuka sosai...ayaanah bata ma iya dago kanta ba tay shiru tana hawaye sosai....

surutu ne ya cika falon ammi babba ta dau xafi ant safeera ma tafara ma kulthum questions but only to judge her with it..

majazen basuce komi ba dake duk sunsan waye me gaskiya, shide ibaad mamaki ne ya fara rufesa da fargaba dan bai taba kawowa cewa zainab arifah zata fara saka ma rayuwar ayaanah zuƙa ba..

yau yafara sanin cewa dolene akwai wani abu aran zainab gameda ayaana wanda bai sani ba nd he must find out sabida ko da wasa bazai sake haka yafara shiga tsakaninsu ba

hargitsi da cece kuce ya kaure sultana da kulthum babu bayanin da basuyi ba haka safiya ta karyata su ta gaskata zainab arifah tace ai komi agabanta akay, ammi babba ta inda take shiga bata nan take fita ba tace ai dama ta lura da su ukun nan banda gulma da iskanci da raini bau abunda suke koya ynx

wani baqar magn ta dinga gasa ma ayaana akan batun zainab arifah da ibaad tana ce mata ita asuwa? ina ruwanta da wnn magann inba raini da gulma yaushe tazo cikin su dahar zata buga kirji ta gaya ma zainab arifah maganan banza inba gulma ba..

saida kowa yagama musu iya fadan da zai musu kafin nan ibaad yace musu subawa zainab arifaah din haquri

..bakaramin kuka su kulthum sukayi ba wanda badan ibaad bane dakansa yasa baki da wallah bazasu taba bada hakurin ba haka kuwa kowaccen su tace mata anty zainab kiy hakuri...kafin zuciyarta yay sanyi.

wani dan uban dadi taji da ya musu fada akan karsu sake fada ko cacar baki da wani ko wata babba agidan idan ba haka ba zai dauki mataki akansu.. bai wani zafafa ba yace musu su tashi su tafi yana furta hakan shima ya fita

sultana da kulthum kowacce ta hau dokin zuciya da tsananin bacin rai da fushi suka haura sama kmr iska

ayaana ce bata koyi motsi ba tana tsugune tana kuka sosai hajy mairo sai surutu take mata akanta tamata fada sosai ...

Ammi karama batace komi tana shigowa wajen tazo ta daga ayaanahn akasa tare da kama hannunta suka bar falon. hjy mairo ta bisu abaya tana masifa duk lefi tana so ta dora shi akan ayanahn sabida duk abunda safiya tafada,
mujaheed yay sauri ya tsareta sukaje sashenta tare dashi aka bar ammi karamn da ayaanah..

daga nan falo kuwa wani sabuwar tantin sharri suka bude anty safeera ce kawai bata gane komi ba, ammi babba kuwa sai kara ma sharrin wuta takey zainab arifah tace musu ai ta jima da gane cewa ayaana tana da raini da baqin hali shiyasa jininta bai hadu da yarinyarba kuma tay ta gaya ma mujaheed sai suta karyata ta toh gashinan yau asirinta ta tono.

ammi babba tahau bambami tace ai ammi karama ce take daure mata gindi..kuma ibaad yana tsoron ya batawa mum dinsa rai shiyasa basa hukunta ayaana ita dama ta jima da sanin yarinyar bata da hankali.. haka suka ta murda maganganu kowa yana fadin nasa har sukasa anty safeera ta soma yarda da su..

maheer yana dawowa ya samu mujaheed yana kan fada ma hajiya akanta dena saurin yanke hukunci kowa yasan ba haka halin yaran nan yake ba kuma bazasu taba zagin zainab arifa akan wannan maganan ba sabida dukansu suna tsoron ibaad...

tace sam ai safiya ta bada shaida ita yar uwarsu ne na jini ai bazata musu karya ba

harsaida ta maimata ma maheer magann snn ya nitsu ya warware mata karyan dake ciki dalla dalla kafin nan ta yadda har tay shiru..

Ammi karama ta dinga rarrashin ayaanah ita duk tsoron haduwar su da ibaad takeji sosai, bataso ya tuhumeta akan maganan sabida tasan ta furta ma zainab arifah hakan kuma bazata iya masa karya ba
..ahaka har ammi ta rarrasheta tay bacci

6:pm ibaad ya gama lailaya abunda ya farun aransa ya fito waje zai yi alwala knn sai ga nan zainab arifah da kawarta nala tun daga nesa yafara jin converstion dinsu suna magana kasa kasa suna dariya "i just cant wait to tell rukky ur one billion dollar story..suka kwashe da dariya" tace "kinga next time none of them will mess with me "nala ta kara kashe murya tace..amma kin bani mamaki how did come up with that story sharply nd babe u need to get that safiya girl a gift, she relly help dan naga gogan naki kamr fa bai wani yarda da storyn ba saida safiyan nan ta saka baki..
"tace'yeah ai dama bazai yarda ba, haka yakeyi akan yarnyr baya ganin laifinta, but i cant deny her back up was really useful." kinga muyi sauri muje gida kar wani yajimu cos ur cloth are even torn yarannan fa sun jibge ki wallah...tsaki nala taja bakiga cixon da dayan tamin bane dole naje nayi tetanus ai naji dadi da aka sa suka baki hakuri marasa kunyar yara kadan sukagani dahaka zaki koya musu hankli
Chapter 89 · 0% Book details