← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 161

Sashe 74

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ammi babba tace hakane kuma muje kawai musaka ido akansu inga me sukeyi ince dai kin ean tsara musu abunda zasu dafa, anty safeera tace ehhh ynxu dai breakfast ne akan wuta suna saukewa zasu saka abincin karban baki
..abbansu mujaheed yace around 11-30-12 dai hajiyan zata iso kuma wai da baqi zatazo

ciikin yatsina fuska ammi babba tace hmm can mata, ni wallh tsohuwar bawai burgeni takeyi ba zatazo ne ta ishe jama'a da saka ido da gulma dama kuma kinsan tana da yar gaban goshinta sai abunda aka kitsa mata akanmu zata ji.

anty safeera batace komi ba har suka wuce backyard suka samu wokers din sunata aiki har an tafasa kaji ana soyawa anware na ppr chicken dana stew agefe, anbada hankli sosai ga breakfast suna kan soye soyen irish da kwaiyaye ana xubawa a platters da minced meat sauce.

ammi babba tana zuwa wajen ko amsa gaisuwar su batay ba ta hade fuska tafara bada oder ayi nan ayi nan dan tafiso ne suyi abunda suma za'a yabe su yau sosai...

9.00 on d dot kulthum da sultana da ta riko hannun ayaanah suka fito sashen ammi karama sam ayaanah taki ta daga fuskarta sabida make up din da anty safeerah ta mata wani bambamra kwai takejin kanta duk da yadda kawayen nata suke haba haba da ita..

wasu mugayen dadadan qamshin soye soye ne ya cika sashen ammi karaman sunayin sallama a falo suka samu ibaad da maheer ne kawai a zaune suna shan tea dayaji kayan yaji da madara yana baza tashen qamshin su citta.

nan take sultana tay kifi kifi da ido kirjin aayana na bugawa da karfi kamr zai faso waje, kulthum ne kadai ta tunkarasu da normal looking face inta daya sha make up ita tafara rusunawa tace "good morning yaa ibaad,.. good morning yaa maheer..kafin ibaad ya amsa maheer yay murmushi yace morning ummi kin tashi lafya? adan kunyace tace lafya,ya gyada mata kai, sultana tafara gaida ibaad kafin ta koma gefen maheer ta gaishesa, kan ayaana na kallon kasa itama ta gaishe da maheer yace wow prettyna kinyi kyau sosai fa,..kara boye fuskanta tay batace mishi komi ba snn ta dawo ta gefen ibaad da sanyin murya tace mishi "ina kwana ka tashi lafya? tea din dake hannunsa ya aje akan table saida yadau minti guda yanamai kare ma sunkuyayyen kantan kallo snn ya kyabe baki yace i am good'..ya jikinki? kafin ta amsa a miskile ya dube sultana yace "ke,..i hope u dint give her any cold water dis mrn,..da sauri sultana tace "aa yaa ibaad bamufa ci komi bama wanka kawai mukayi da ruwan zafi...yace toh ya isa haka toh kuje ciki mungode da gaisuwa.

..idon maheer nakan kulthum harta tamike tsaye tay kitchen din sultana tay saurin binta abaya, ayaanah na kkrin binsu da sauri ibaad yace "not you" wani garas taji ahnkli kuma ta koma ta zauna agafensa akasa a slow motion tay shiru.

dan karamin shirune ya ratsa wajen kafincan maheer yamike yanufi kitchen in shima aka barsu su biyunsu a zaune

..daukar fresh clean tea cup yay ya zuba shayin ya miƙa mata, dan dago kai datay zata karba da suka hade ido yaji wani abu ya tsarga masa yay loosing balance wanda tuni tea din ya dan zuba masa ahannu, dan gani da yay gabaki daya ta canza masa da make up dinnan, yay saurin kyabe baki tana karba ya ciro hankynsa daga aljihu yana goge inda tea din ya zuba masa itama nan take kallo batakai tea din baki ba harsaida ya gama sharewa suka kara hade ido girarsa na sama a dage ahnkli "what are u waiting for, ko sai nace miki kisha? ko kuma nabaki abaki? its almost nine bakici komi ba kinsaya kinata fenta fuskarki ko??toh ko kyau bai miki ba

dan shagwabe masa fuska tay daya kara narkan dashi batace masa komi ba, kurba daya tay ma tea din taga ya zuba mata ido yanakan kallonta, ahnki tare da kara shawgabe masa fuska tace bani nayi ba fa ai umman kulthum ne tamin"
yace "uhmm ni nace miki wani abu ne?..shanye kawao, kema kibisu ciki. shiru tay ta cigaba da shan tea din ahnkli tana satar kallonsa while yanakan latsa wayarsa, basu kara cewa komi ba awajen ba har saida ta gama snn ya sallemta yace taje kitchen din ta kira masa maheer tace ya samesa a daki dan su shirya ynxu..tana shiga kitchen din kuwa ta kalli maheer tacemai ibaad yana kiransa a can dakinsa ..

dambun kaza da ammi karama tay ya deba ahannunsa snn ya fita ya kyalesu anan sukadai

...ammi duk ta yabe kwalliyrsu tace sunyi kyau sosai sunata jin dadi.

Karfe 9am na cikawa duk aka fara hallara cikin main falo domin karyawa, da wuri ammi karama tace duka yaran nata sufita suyi gaisuwa kafin itama ta fito. dukansu hudu suka wuce main palon safiya ce ta fara sallama dake bata fiye son magana da su sultana ba, lkcin anty safeerah ce kawai mace a falon tana tsaye tana bada masu aiki su biyu oder ana jera breakfast din akan dinning ita kuma anmi babha tashiga dakin anty safeera canza kaya, daga bappa zaidu sai uncle moh da already kafin su ayaanan su shigowa falon anriga an kirasa a waya yafice cikin gaggawa dake shikam ma bai wani damu da yasan waye yarinyar ba existance dinta agidan baidamesa ba dan kwata kwata baison wani abunda zai takura ma rayuwarsa ko kadan

Dukansu yaran haka suka tsuguna suka gaishe da bappa zaidu cikin girmamawa, 10min past nine kowa ya fito aka zauna ammi babba ta wani cakare da jan atampa ta baza dauren ture kaga tsiya tana shan qamshi duk a tsammnta yadda suka ci kwaras hakama ammi karaman zata fito ta dau wankaz sai kuwa tabasu mamaki ta saka normal moroccan jallabiya dayaji dinkin zaren hannu golden colour all thru da mayafinsa
bata kuma yi kwalliya ba tabar natural beautynta a fili.

cikin girmamawa aka gama gaggaisawa kowa nakan table din face uncle moh da damsa mujaheed da already yake plane frm S.A.to nigeria bai iso ba tukuna.

lafya lafiya aka ci abinci karyawan, banda ammi babba dataki su ko irin gaisawa na fatar bakin nan da ammi karama, dan tana ganin irin kallon da bappa zaidu yake mata asace abunda yafarun jiyan ne kawai ya dinga fado mata arai tana jin tsananin kishi da kokontonsu akan ambatarta ta da mijinta yay da sunan fatima akan gadonsa jiya datake shafashi.

ana gama break fast bappa zaidu bai kula kallon kishi kishin da ake jefawa akansa ba ya fice, maheer da ibaad kuma suna cikin gida basuje koina ba suka zauna a dakin ibaad din suna kan wasu abubuwan dake gabansu time to time suke zagowa suzo su duba ammi karama a kitchen dan ita daya take abubuwanta ko yaran ma tahanasu su tayata

daga waje kuwa wani jiji dakai da iko ammi babba ta dingayi ma workers din, idan suka saka maggi tace sam su rage yay yawa, hakama zata bulbula ma abincin wuta fall fall yama ci tayita masofa tace wai sauri sukeyi ba sime sime ba...ta matsu sugama takoma daki ta sake canza kaya kafin hajy mairo su iso.

gidan yay shiru kowa na indah take, kafin 10:30am ammi karama tagama komi datake shiryawa nan tay packaging
dinsu drinks da chops din so lovely a wasu shegun bottles, classy glass, dispensers da wasu expensive luxury cheffing dish data sayasu duka ahannun uwargida collection tun daga garin kaduna...

tana gamawa ta bar komi anan kitchen din snn taje room inta batay wata wata ba ta fada wanka after a while ta fito ta ciro wata peach colour applique lace doguwar rigace me celeopatra neck ta saka
tay daurin daya rufe mata duka gashinta kanta sosai tay kyau bana kadan ba...

dacan har kamar zata fita ta duba ya su anty safeera suke ciki da girke girke sai kuma tafasa tay zamanta a daki dan tasani sarai ba wani abu me wuyane bane ammi babba ta gasa mata baqar magana acikin mutane.

har saida 11 yay kafin su ammi babba suka bar wajen girkin lokcin rabi ran masu aikin ya baci sabida yadda ta dinga kwaba musu aikin su da yawan bada oder. kai tsaye aka fara packaging abincin dana baki, dana hajya da nasu duk aka kai ciki, anyi coloured rice kala kala har guda uku, difrent kind of sauce da egg stews, ppr chicken da manyan manyan turkey da alalle daya ji cray fish, masa da miya, da kunun gyada dana tamba. ayayinda su ammo baban sukaje dakin anty safeera sake shiryawa nan wokers suka karasa kawo abincin babban sashen hajya mairo aka fara jeresu a kan dinning in falon within minutes harr angama komi gidan saiya dauka da wani irin shiruuu.

Da misalin 11:40am Wasu manyan manyan SUV jeeps guda biyu bakake kiriin masu fidda wata uban sheki suka shigo harabar gidan sukayi parking ayayin da driver yay saurin saukowa kasa ya bubbude musu kofofinsu Yana mai rusuna kansa akasa cikin yanayina tsantsar girmama wa, Wata dattijiwar mata ce wacce bazata wuce 60+yrs ba tafara sauka kasa cikin shigarta na mutunci tasha brown hijabi daba atula mai tarukucen design ajiki ba babban aminiyar hajya mairo kenan hajiya hajara wanda itama da safen tay sammako taje har tudu domin tadauko babban aminiyarta tadawo da ita gida dan tasan bazaimata sauki barin tudu ba yadda aka saba da taimkon bayin Allah datakey acan kowa baison hajy mairo tabar wajen..

tana sauka sauran baki guda uku mata da yarinya yar 12yr suka sauko suma amma su mataye ukun duk matasa ne basuda wani shekaru

driver su ne ya Taho da gudu ya amshi jakar hjy hajara ya rike mata har suka karaso Gaban dayan motan wanda har yanzu hajy mairo ce aciki amma bata sauka ba, tana karasowa gaban murfin motar taja ta tsaya tana kallonta kafafunta da hannunta Duk sunyi nauyi idanunta sunyi ciki ciki saboda tsabar gajiya, Wani dankareren medicated glass ne ta toshe kwayar idanun nata dashi Itakuma leshi ne ajikinta nata purple colour an mata dinkin buba da zani kafarta cikin wata flat shoe mai kama da Dunlop da kyar ta motsa jikinta sabida tana da Dan kauri.
Chapter 74 · 0% Book details