← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 161

Sashe 67

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan was quiete babu motsin sultana bare na ammi babba dan tunda ta amshi kudin ibaad ta biya zinariyar mace kudinta sai taji sakat, yau wuni tay a dakintan suna waya da babbar kawarta hajiya ramatu banda zage zage da kulle kullen makirci gameda tafiyar da mijnta yay da ammi karama babu abunda sukeyi..

wani irin zugata Hjy ramatun tay akan karta sake takyale fatima ta cuceta a banza duk tsiya ta sake karban million goman nan ahannunsa kota halin kakane dan ta huce takaici.

bangaren su ibaad kuwa tunda suka fita wajen abokai ba su da dawowa gidan ba sai can wajajen karfe sha biyu saura na dare, they all came back very tired nd glad they went out dan spending time da sukay da abokan nasu awaje sosai yadan rage musu wani family tension acikin zukatansu...

washe gari da sassafe tun kafin aje sallahn fajr
sultana tay sneaking ta dawo dakin ta samu ayaanah nakan bacci sai tay maza ta cire kayanta tashiga bayi tay alwala bayan ta fito ne tazo ta tasheta akan tay sallah, kafin ayaana ta gama sauka daga gado taje tay alwalah tafito tazo ta samu har sultana ta fara nata sallahn sai kawai ta jonata itama bayan sun gama ne sanyin Ac ya buga ayaanah sosai ta fara wani irin tarin sanyi dayaki tsayawa, tun suna matsewa har sultana tafara jera mata sannu sannu dakyar ayaanan tasamu ta kwaco numfashinta tace mata ita ruwa zata sha ta kawo mata ruwa..nan kuwa sultanan ta fito da uban sauri danta neman mata ruwan dumi duba da anriga anhanata shan ruwan sanyi musn da sassafe.

lkcin daf ana fitowa daga sallahn fajr ammi babba daga farkawan ta dinga kwadawa layin bappa zaidu kira akai akai kamr yaqi amma sai ji take akashe, wani irin baqar kishi take taji duk ya cika ta taciki ta kasa tabuka komi sai juyayi dan tun batason tasaka zarginsa aranta na kasancewa tareda fatima har abun ya fara samun waje acikin zuciyarta,

sallan ma yau a daddafe tay shi tabita zauna akan sallayar ranta a mugun dagule tanata rubuta masa text message akai akai akan ya kirata tana son magana dashi.

bayan sallanh fajr maheer ne yafara shigowa gidan da sauri sauri akan zai haura sama yay wanka yafara shiri dan yana da 8am on d dot test yana kuwa shigowa ya hango sultana da flask din ruwan zafi ahnunta tana sauri sauri, gyaran murya yay abazata tatsaya cak tay freezing musammn ma da suka hade ido dashi saidai
ganin shidayane anan taji gara kawai ta fito fili tagaya masa gaskiya akan case dinta da ayanah inyaso shi sai ya ma yaa ibaad din bayani gameda abunda ta aikata ma ayaanahn jiya na boye asalin gaskiya

karasowa tawajen sa tay da mugun sauri tun kafin ta fara gaishesa yafara tuhumarta me zatay da flask din ruwan zafi da sassafe, tuna masa tay cewa an hana ayaana yawan shan ruwan sanyi ne da safe shiyasa taje kitchen ta kawo na zafin.. cikin gamsuwa da hakan ya juya zai wuce ya haura dakinsa sai tayi caraf takira sunansa."ya maheer can i talk to you??..da mamki ya juyo ya kalleta ganin ta sako fuskar tausayi yace"..ke kuma meyene badai zakice min bazakije schll yau ba? cikin i ina tace a'a yaa zanje,i iii just want to talk to u abt sumtin, nd i promise it wont take time

..dawowa yay one step back kusa da ita yace ehen inajinki

dede nan ibaad ya shigo gidan shima basu lura ba da tunanin kar ya katsesu saiya tsaya ata can bayansu batare da yay motsi ba, sultana ta sunkayar dakanta kasa ahnkli tace yaa maheer, zan gaya maka wani abun amma dan Allah don't judge me, ya mata kallon go ahead, tace..toh dama jiya ne nace ma ayanah muje waje musha iska sai naje kitchen sai naga soyayyan turkeyn da mummy ta ajiye shine na dauki guda uku nazo na bata guda daya nasata dole itama taci dan muyi hira, itafa batace ma zataci naman ma nine na dingace mata sai taci.. nd. and...it was bcos of me she also came to fetch water,shine kawai naji wai mummy ta kamata tanata ce mata barauniya, yaa maheer ..its totally my fault, wllh bata daukar ma mummy komi ba,..

dedenan ta fara hawaye ahnkli
tace "kuma ai naga yaa ibaad ne aciki shiyasa naji tsoron nagaya ma mummy asalin abunda ya faru a lkcin...can you pls tell him da it is not her fault?i feel really bad for putting her into dis mess.

....baki a bude maheer ya dinga kallonta sai can yace ohh dama kece munafukar da kika dauki naman shine kikay shiru saida aka gama cin mutuncin yarinya zakizo kina wani min bayanin karya daga baya?

tana budan baki zata amsa taji taauuuu ya dauketa da mari batasan sanda ta sake flask din akasa ya fashe da karfi ba. lkacin kuma lekowar ayaana ta wajen kenan jin karar fashewar flask din yasata ta razana ta koma da baya tadan tsaya acan nesa tanata kallonsu.

ta inda maheer yake shiga batanan yake fita ba. daga kuma ta budi baki zata sake magana sai ya kara wanka mata mari, saida ya mareta sau uku, snn kuma yabi ya zare mata ido ya hanata yin kuka...

yace munafuka kawai me baqin hali, u had all the chance to tell me d truth tun jiya aike na samu anan kina kukan makirci kikaki min karya konima tsorona kikeji a lkcin? muguwa kawai ai sainaci ubanki kika sake aikata irin wnn halin nd ure very stupid for telling me not to judge u

ayaanah was teriffied dataga irin hukuncin da maheer yay ma sultana dan duk tunaninta ay shine namiji me tausayi da saukin hali agidan, sai taga kmr ma yafi ibaad masifa da mugunta, dan duk tsiya dai tasan ibaad saidai yace zai daketa intay wani abu amma haryau dai bata taba ganin ya aikata hakan ba.

cikin tsananin razana sultana take kuka at same time tabi ta toshe bakinta kamar yadda ya umarceta dan baison kukanta yajawo hanklin mamansu har sai yagama masifeta, masifan yake mata saidai tunda ta juya baya taga ibaad na tsaye ata bayansu atake tafara jin kamar numfashinta na tafiya tsabar tsoronsa datakeji kmr zata yanki jiki ta fadi ta suma

..shide baice komi ba harsaida maheer ya gama fafala mata mari ya masifeta tasss snn yazo ya karbeta a hannunshi yace masa yay mata uzuri
aima tay kokari ma datazo tagaya gaskiyan he shudnt dicredit her like this..

sama sama yace mata karta kara yin hakan, snn tana fadin gaskiyarta koda a gaban wayene, jin tsoronsa is not an ezcuse for her to hide things, and this shud serve as a lesson to her,..

haquri ta dinga basu, har ibaad din ya sallameta batare da ya mata wani zazzafan fada ba.
..wuce ayaanah tay da sauri tahaura sama ta wuce dakin ta zauna akan gado tanata kuka.

acikin ruwan sanyi ibaad ya fahimtar da maheer cewa is best sudinga sassauta ma sultanah hukunci,ayi masifar dai amma banda duka, sabida karda next time wani abu yafaru da ita kanta agidan tafara boye musu asalin gaskiyar halin da take ciki.

maheer baiy gardama ba kuwa ya fahimcesa daga nan kowa yaje room dinsa domin shiryawa...

daga dakin su sultanan kuwa ayaanahce tashigo da sanyin jiki ta tsaya agefenta da niyyar bata hakuri, sede tun bata bude baki ba sultanan ta riko hannunta tana kuka suka hade ido cikin magiya tace ayaana dan Allah kiyi hakuri kiyafe min kinji? i dint knw what came over me. kiyi hakuri bada son raina nay shiru jiya ba, what happen was wrong, nd i wll neva do this to u again..dan Allah ki yafe min karkiji haushina kinji?

tausayi yasa ayaanah tafara zubda hawaye ahnkli tace "aibabu komi ni banyi fushi ba, daganan sai sultanan take gaya mata irin tashin hanklin data shiga jiya, da tsoro, da guilt daya hanata zuwa cikin dakin jiya tamata bayani, sabida gani tay kamr bata kyauta mata ba. ayaanah taji tausayin sultana bana kadan ba, tagane cewa tana da zuciya me kyau. bayan sun fahimci juna... sultana only confuses her more akan yadda dacan take kallon maheer a matsayin me saukin kai da sanyin hali a idanunta

tace ma ayaanah ai duk da murdadden halin yaa ibaad gara mata shi,baya daukar hukunci da zuciya da zafi sai yay bincike, amma ya maheer he will alwys act rarshly before even thinking abt the consequences..
...duk hakan da sultana take fada mata sai ya bala'in rage mata wnn shauqin da duk wani karfin amincewa da ta dauke maheer mai saukin hali acikin idonunta dashi...

after a while bayan sun gama surutunsu suka shiga wanka sultana ta fito tafara shirin schl sai ta bawa ayaana wasu sabin kaya ta karba ta saka ajikinta nan da nan wani sabon fahimtar juna yafara fara shiga tsakaninsu.

ata bangaren ammi babba kuwa dakyar ta bar kan sallahya taje tay wanka, badama taji dan motsi ko kara sai tajuyo da sauri ta kalle wayatta, tana tsaka da saka dankunne agaban madubi taji karar bude kofa ahankli.

maheer ne ya shigo all dressed up in pure black zagner suite da yay masa matukar kyau sede fuskansa ba sake ba, ya rusuna cikin ladabi yace ina kwana mummy...tana kan kallonsa tace lafya kalau ya naga har ka shirya da wuri haka?saddiqa ce fa zata muku breakfast yau.. dan wallah bana jin dadi jiya ai kuna sane babanku ya dauki budurwarsa suka bar kasar nan amma cikinku aka rasa wanda zai iya gayamin hakana na lalata kudina da lokaci na shirya masa abinci abanza..

da karamin rashin tsoro a idanunsa yace" munyi waya dashi jiyan sauri yakey lkcin shiyasa bai gaya miki ba, kuma daya kirani da daddare ai yace ya tura miki text messg ko baki gani ba?

..."da mugun mamaki ta juyo tana kallonsa tace "ohhh hmm, dama yana da lkcin kiranka jiyan amma ni shine text din kawai zai iya turamin? cikin karkada kai tace hmmm lallai ina ganin walakanci agidan nan, gashiku sam bakujin tausayi na upon duk wahalar danakey dan na nuna muku cewa zaman lafya nakeso agidan nan amma dolene dai sai an tunxira ni...
Chapter 67 · 0% Book details