← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 161

Sashe 140

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hajya hajara ta saki baki tace wann ma maganan banza ce, ke kuwa mai tuwo yarinyar nan fatima har nawa take? inbanda ma karya da kika dinga shera ma mutane fatima fa a yar shekara 16 tazo cikin gidan nan ko kin manta ne? har yanzu fa yarinya ce atata ace anbata shekaru arbain da hudu zuwa da biyar ba toh wallah in zaki mike tsaye ki mike bawai kawai anzauna ana ta cutar yarinya ba duk anbarta da juyi a gado me sanyi kullum ruwan sha'awa na taruwa mata amara, tunda dai addua bai yi ba ai munjira, ynxu kawai mu hada kai munemar masu mafita.. yau kiga dai inda taje ta lallabo miki shi yaxo har gabanki ya durkusa ya baki hakuri, shin ita wancan balamar matar tasa tay miki hakan ne?shegiya mummuna banda gulma bata iya komi ba tunda nazo gidan nan ko ruwa banga tazo ta aje agabanki ba taje can tana yawo da sakakken duwaiwaka tana jin gulma awajen safeera toh wallah baxaiyu ba, inke yar kungiyar izala ce ni nariga na wuce nan sabida haka xanje
duk inda xanje wallah sai an cire yarinyar nan a azaba an aura mata mijinta ke kuwa maituwo wann uban mugunta har inaaaa kema fa da lefinki akanbyaran nan dan fatima ba yar cikinki bace shiyasa baki damu da halin da zatana shiga ciki ba shekararta nawa babu namiji aikekuwa kya tausayawa rayuwarta

jan ajiyan zuciya mai nauyi hajiya mairo tay tace "kune fa kawai kuke ganin kamar bana tausayawa fatima amma har raina bana tsammanin inada wata a duniyar nan danake jinta kamar yar cikina kamar ita, fatima fa tasha wahala dani. kedai tunda kince zakiyi wani abu akai toh ki gwada mugani nide inhar sihirin nan ya kunce ko yau yaune zan iya sawa a daura musu aure kowa ma ya huta..malamin nan cewa yay fatima zata mutu in akay auren ba a karya asirin nan ba, yanxu so kuke na mata auren da zai kasheta inta mutu ai ni aka cuta

hajy hajara tace yanxu naji magana toh yanxu dai kibani nan da wani lokaci in sha Allah wann aure sai anyishi nan bada jimawa ba, koma waye tay asirin zanje can kauyen mijina na, kinsansu ai kabilar jukunawa ne, dole ne muma mu tashi tsaye mu gwada musu muna da yadda zamuyi haba cutarwan yayi yawa....

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[13/12, 19:36] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.

⏯️4️⃣6️⃣
tunda hajiya hajara ta gama tsige aminiyarta hajiya mairo akan batun maganan auren zaidu da fatima sai bata sake cewa komi ba, suna zaune anan suna yan hira har ammi karama ta kawo musu abin taɓawa albarka suka saka mata da har zata wuce dakinta taje tay wanka hajya hajara ta zaunar da ita ta dinga mata nasihohi masu ratsa zuciya da shiga jiki, nauyi da kunya duk yabi ya hana hajy mairo cewa kowa ba har hajiya hajara ta sallameta ta fita.

ata fannin bappa zaidu kuwa gabaki daya daren ranar juyi yakeyi akan fankacecen gadonsa da tunanin yadda zai iya bullowa al'amarin aransa saida yasamu cikakken nitsuwa yay tunani me zurfi snn ya iya sake ransa yayi hakuri.

washe gari da safe as usual suka fita sallahn fajr ibaad ya jasu bayan an idar suna shigowa cikin gidan ya kirawo shi sukaje private palonsa acikin sashen sa. ibaad yana daga kasa shi yana sama.

kai tsaye yafara sanar dashi abubuwan da ya farun jiya, dan yasan da wuya ne inyana da masaniya dake tun asubah jiyan ya fita kuma bai dawo ba saida yamma lisss.

har saida ya gama fayyace masa halin da ake ciki snn yay masa nasiha, ya kuma sanar dashi bada son ransa bane daya zo yana dawo masa da wnn maganan. su dauka kawai duk wannn abun qaddara ce dan haka umarni yake bashi da yay hakuri ya amince ayi auren, inyaso daga baya in komi ya lafa sai ya aure duk wacce yakeso ya hadasu su biyu.

tunda bappa zaidu ya furta masa wnn maganan saiyaji kamar iska ya dauke masa baya shaqar numfashi ganin yakasa amsawa yasa bappa zaidun yace masa yaje yay tunani zuwa yamma ya bashi amsa yay masa nasiha ya kuma bashi hakuri sosai..

jikin ibaad a sanyaye ya tashi ya bar wajen bai masan sanda yakai kansa dakinsa ba he laid on his bed for a while yanajin kamar baya duniyar ne gabaki daya, sai can ya jawo wayarsa yafara kkrin danna lambar mum dinsa ganin bata dauka ba kawai ya miƙe ya shirya kansa duk sonsa da tsafta yau ko kula wanka baiyi ba, karfe 7 dede saigashi ya shigo cikin gidan idonsa a rufe kai tsaye dakin amminshi ya nufa hanklinsa a tashe sosai...

tana gama gyara koina kenan zata fito ta shiga kitchen yay sallama ta amsa masa yashigo gani tay kawai ya zauna kasa jikinshi a mugun sanyaye yayi shiru baice komi

throw pillown dake hannunta ta aje ta karaso wajensa tace "rayyan ya naganka da sassafe haka lafiya kuwa? ko bakajin dadin jikinka ne...

jin kamar idan ya budi bakinsa zaiy kuka yasa ya sunkuyar dakansa can kasa gwanin ban tausayi baice komi ba saida yadan samu nitsuwa taciki. shirun dayay yasa atake jikinta ya bata, waje ta nema ta zauna kusa dashi akasan da sanyin murya tace rayyan pls talk to mummy, kunyi magana da bappanka ne ko?

yana dago kansa taga idanunsa yay jaaa zai magana cikin katsesa tace "honey, Its for the best" Dan Allah kayi haquri none of us wanted this for u. musmn ma kawunka wallh jiya ya bani tausayi dan inda anbita nashi da ya gwammaci hajiya mairo ta tsine masa akan daya maka wann auren..pls look at it as ur destiny...kay hakuri...

cikin girgixa kai hawayensa tsilli daya ya sauko murynsa na rawa yace "Ammi wallah bana kaunarta, kuma bappa bai taɓa bani umarni akan wani abunda banaso ba sai wann karon, iyakan zamana da shi a gidansa he always defended me har sama da farin cikin matarsa, ni ynxu bansan me zance masa dan banason saɓawa umarninsa kuma harga Allah banason na aure zainab sabida bana kaunarta kwata kwata banajin zan iya kallonta a amatsyin matata..

da tausayinsa a idonta tace "nasani..dama kuma ba auren soyayya muke nema agareka ba rayyan...inada yaqinin cewa zainab wata bangare na jarabawa da kuma qaddarar kace, hala wani gwaji ne da Allah ya aiko maka dan ya jarabce rayuwarka snn karkamanta tun tana karama sosai ta fara wann abun. gashi har yanxu ta girma dashi yaxo yanaso yay sanadiyar rayuwarta, toh da ace ka bijire ka wargaza zumunci akan rashin haquri kuma zaonab tazo ta rasa ranta sanadiyarka gara ace kay musu biyayya kay hakuri ya zamo kaine aka zalunta bakaine ka zalunce kowa ba..if ure patient Nothing evil will ever happen to u addua ta kullum yana tare da kai, nide hakuri nake dada baka dan Allah ka rufa mana asiri yazamo nan gaba baza'a a kalleka ace kaine kayi sanadiyar tarwatswer zumunci da kimar gidan al-mansur gabaki daya ba. pls dont think as her a matsayin zainab da baka kauna, just look at her as a fragile life dat needs ur company to be able to dream nd breath again, nd i know my son wudnt be the reason for sumones grieve, or life lost..u wont be the reason to tear this family apart, kaduba girman abunda zakayi a idon Allah, this is a huge secrifice for the entire family nasan mahaifinka zai yi alfahari dakai..pls keep ur desires aside rayyan, nd do this for sake of Allah... besides babu wanda zai hanaka auren wacce kakeso anan gaba
...kawai kay hkuri ka ansa wa kawunka, shima ya samu nitsuwa kaima ka samu nitsuwa gidan nan duka a samu kwanciyar hankali...inda mahaifinka na raye you know he will prefer to keep the peace too, kuma shima da abun da zai roka awajenka kenan.. duk wani walwala da farinciki da zumuncin gidan nan yanxu haka yana wuyanka ne, be the bigger person pls nd think abt it..amma koma miyene nidai dan Allah karkace ma kawunka a'a zaka kunyatar dashi, just let it go..nd let god see u throu. inma taruwa akayi agidan nan duka aka cutar da kai kabari kawai Allah zai saka maka. kuma in sha Allah zaka cinye wann jarabawar

hawayen dayake zuba a idonsa yasaka hannunsa yashare ahnkli muryansa a sanyaye yace toh shikenan ammi tunda kema hakan kike gani bakomi zanje na sameshi in sanar dashi na amince zan aure zainab din..

kusan dede nan kalmomin nasa suka dira acikin kunnen ayaanah datazo kofar dakin da sauri da niyyar zata gaisher da ammi dan yau exams na IRS zasuyi karfe 9am dai dai tanaso ne taje tafara shiri dan tuni tagama duk wani bitan karatu da zatayi.

tana dada jin muryansa aciki ta tsaya cakkkk dan har wani yaam yaam taji kunnuwanta na neman toshewa tafara jin jiri jiri ne ko faduwar gaba ne duk ta rasa me takeji, she instantly frozed har ta gama jin conversation dinsun na karshen yadda yake tabbatar ma mum dinsa zai hakura kawai ayi aure. ita iyaka nan kawai taji..yau yaa ibaad din nata ne dakansa yake cewa zai aure anty zainab arifah??

batasan how many minutes tay a daskare ba ita bata bude kofar ta shigo ba ita bata iya jan jikinta daga shock in datake ciki ta koma room inta ba, jim kadan sai taji inuwar mutum agabanta,

kirjinta na bugawa da balain karfi ta daga idanunta sama taga shine har ya fito, suna hade ido dashi hawayen da batasan daga ina suka taho ba suka fara sauka a idon ta jikin ta na rawa rawa ta juya da uban gudu zata koma daki yay saurin biyota yana furta "ayaanah, ayaanah..
...amma inaa bata tsaya ba tana shigewa dakin idonta a rufe kamar mai aljanu tanufi bayan gidan tay sauri ta kulle kanta aciki tareda rusunawa akasa da wani irin mtsanancin kuka me daga hankali sosai, hanklinsa a mugun tashe ya shigo dakin yana kirar sunanta safiya tay marmaza ta sauka akan gado ta fice basu waje.
Chapter 140 · 0% Book details