← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 161

Sashe 52

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daf lokacin anata tuka tuwon rigima da bala'i da ammi babba da security a tsakar compound bappa zaidu kam tuni ya kyaleta da securities din yashige ciki da sultana abunsa ransa yau bakaramin baci yay ba...he was soo tempted to write a full blown divorce for her har ya dauki paper da pen a desk dinsa amma daya tuna cewa babu kyau yanke hukunci irin wannan acikin fushi sai bai rubuta sakin ba

suna shiga motar ibaad ya zauna da ayaanah agidan baya maheer ya shiga driver seat.

wani dan uban waina motar yay da mugun karfi yazo da gudu kamar zai kaɗe ammi babba ta ruga a guje tay waje tana ihu security sukay maza maza suka tsareta acan..

dura ma maheer din ashar ta dingayi harsaida sukayi nisa snn ta hakura ta kama hanyar gida...

6.54 am sharp suka isa harabar al-eeman privte hospital maheer ne ya tsaya a reception yay cike cike, tru transfer ya biya kudi while ibaad ya wuce emergency da ita direct aka fara bata taimakon gaggawa.

ciwon sosai ya tashi mata har aka fara tunanin akaita ICU ranar sosai ibaad yaga tashin hankalin da bai y tsammanin zai gani ba, duk suka tsaya a kofar emergency gwanin tausayi hawaye na zuba a idon maheer yanabi yana sharewa cos he dosnt even knw what he is feeling abt his own mother ryt now, dan sam bai san wata irin mahaukciyar mata bace ta kawosa duniya..

daga bangaren bappa zaidu ya dau lokaci yana tambayar sultana abunda ya asalin faru, toh dake itama ba duka tasan manufar mamantan ba iyakan abunda tasanin kawai ta gaggaya masa, word to word abunda ta dinga ce ma ayanah, har da zuwanta dakinsun jiya datay da daddre ta mata maganan tea,da komi daya faru saida ta fada ma babanta dalla dalla..

lallabarta yay yamata nasiha har saida ta dawo hayyacinta snn yace mata taje tay sallah tay shirin schll yau shizai kaita dakansa ba driver ba..

tana ficewa ya kira su ibaad a asibiti bayan sun gama wayar atake ya kira waliyyin ammi babba, dake ransa har yanxu a bace yake babu wani boye boye ya kai kararta tareda cewa gaskiya shi zai saketa dan yagaji da tijara da abun kunyar da take masa agida..bata barshi ba, bata bar yayansa, bata bar danginsa ba, bare baki, ransa a mugun bace yace gaskiya azauna ayi magana idan ba haka ba saki uku zai mata ya kawo wacce zata rike masa yayansa dakyau cos raihanatu is no more setting any good motherly exmple to his children ..

jikin waliyyin nata bakaramin sanyin yay ba dan bappa zaidu bai taɓa kiransa ya gaggaya masa magana masu tsauri da nauyi haka ba...tun awayan ya babbashi hakuri amma yay shiru bai amsa ba har ya katse wayarsa yanajan tsaki..

shikuwa waliyyintan baiy ƙasa a giwa ba ya kira mahafinta ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, wasu maganganun ma awajen matarsa yakeji na yadda ake gulman yadda raihanatu take zuba rashin mutunci agidan mijintan tunba yau ba ..
yace ma babanta gaskiya suyi zama da yarsu adau mataki akanta dan yaga da Alama wnn karon kamar dagaske bappa zaidu yakeyi zai saketa kuma baya tsanmanin saki daya ko biyu zai mata tunda ya kawo batun karo aure.

wayarna kunnensa tun baisauke ba yaji sallamarta da sassafen ta shigo gidansu da kuka

mahaifiyrta dake daure mata gindi ita tafara fitowa da uban carbi a ahnnunta suna haɗe ido tay salati tafara tambayarta ko lpya taganta haka ahujajam babu mayafi bare takalmi?

wani dan uban kuka ammi babba ta kara fashewa da shi mamantan ta riketa da tashin hankli

dede ta budi zata fara magana kenan sai ga babanta ya fito fuuu kmar iska daga falonsa dawani makaken wayar wuta irin cable dinnan bai wani tsayajin me zatace ba amugun harzuke ya cakumota ya hau chauda mata cable din ajikinta yana cewa tunda ke kin nuna ma duniya ke karamar yarinyace zakisan cewa kuwa baki karfin duka agidan nan ba..

wani dan uban ihu takey tafadi kasa agigice tana murkusus tana cewa wayyo Allah na baba dan Allah kay hakuri wallah ni aka cuta..baba nice me gaskiya

gashi dogon nity ne ajikinta mai tsantsi kamr satin innan ya dan kame dirin jikinta sai feywww fewww taji duka na shiga jikinta kota ina tsabar zafin datakeji
kamar zata suma haka take birgima ya hadata har da uwartan ya masifesu yace mata tay waje tunda ta iyayin rashin mutunci da hauka wa mijinta toh badai ta zauna masa agidnsa ba saidai tafita taje pyschtri wajen yan uwanta mahaukata tacigaba da rayuwa.

duk surutu da borin da mamanta tay bai kulasu ba...haka kuwa ya mata rashin mutunci ya koreta agidan yasa aka kulle masa gate dinsa..

karshe gidan kawunta wanda shine waliyyinta dayake da mugun zafin ta wuce wanda kafin ta isama zazzabi me mugun zafi ya rufeta, badon da taimakon saka bakin matarsa ba nan ma da korarta zaiyi dan wncn karon ma datay yaji shine yaje har gida ya bawa bappa zaidun haquri aka maidata...

abun duniya ya taru ya mata yawa, saida aka kira nurse tazo gidan tasaka mata ruwa, duk iyayenta maza suka dau zafi sosai...matan ne suke zaune tare da ita...

wanda yake matsayin shine mahaifinta yace muddin ta bari mijinta ya saketa saiya tsineta mata dan haka tafa san yadda zatay tashawo kansa tun basu kai ruwa rana ba.

kawuntan kuma yace abarta agidansa har sai ya garata kafin asan me zai faru agaba. tunda ta kwanta a dakin kuka kawai takey tana dan danasanin faruwar komi gashi tabar wayoyinta duka a gida batasan taya zata kira aminiyarta ta gaya mata kalar iftila in daya fado mata ayau ba. ita ba magani ba, ga asarar million goma ga mijinta da yayansa sun dau zafi akanta sosai..

bangeren su ibaad kuwa har angama shirya ayaana za aikata ICU a dorata da ggawa akan oxygen sai kuma condition in nata yay subsiding miracously numfashinta ya dawo daidai..

dede lokcin bappa zaidu ya aje sultana a school, kafin nan yazo asibitin ya samesu nan aka sanar da shi duk abunda yake faruwa, after much talk with the doctor ya biya kudi for exra heart specialist consultancy da za'a iya samu agaggauce..

bayan bappa zaidu ya gama abunda zaiyi anty hauwa ce ta rakosa har waje snn ya wuce office abunsa dan gaba daya jiyake kamar he is not in mood for everthyn yau.

anan asibiti su ibaad suka zauna harsaida akai yan kwaje kwaje aka tabbar da komi lafya snn aka bata private room akan asibiti zasu riƙeta anan for some days for further observations.

sai wajajen 10:30 kafin komi ya lafa, maheer ya fita yaje ya siyo musu breakfast wanda kwata kwata ma dan kadan sukaci suka kyautar da saura, can sai ibaad ya tashi yafice da wayarsa a hannu ya kyale maheer din yana zaune akan kujera kusa da ayaanah datake kan bacci baiko gama karasawa reception ba suka ci karo da mahaifiyarsa...
#SURAYYAHMS
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[15/11, 17:52] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: https://chat.whatsapp.com/L0CT3df9pSP05pzRWvDHam?mode=wwt
Your go-to for beautiful, budget-friendly modest wear! Discover a curated collection of thrifted abayas, gowns, and dresses. Each piece is Grade A quality, ready to elevate your wardrobe.

⏯️2️⃣2️⃣
Abunda ke ɓoye💫#surayyahms
Da mamaki ibaad ya tsaya yanata kallon mum dinsa agaban hospital reception harta gama magana da wata mata snn takaraso ta wajensa fuskanta ba sake sosai ba,.

ahnkli cikin yanayin mamakin ganintan yace.."ammi ure here..ciki ciki tace yes surprise to see me huhn? ya dada kureta da ido yace "meya faru? hope ure okay maa ba dazun nan kikace min zakije aiki sabida kina da important meeting ba?

cikin katsesa da muryan fushi me hade da damuwa tace "eh, inakan hanyan ai aka kirani shine na dawo..kwayar idonsa daya dan fada ciki yay farau takalla cikin sauke ajiyan zuciya tace"so how is she? any major injuries??ko kun tsaya kuna kallo har an kasheta?

bai amsata ba saida ya jawo hannunta gently suka bar kan hanyan suka tsaya daga gefe snn ya girgiza kai yace ko daya'

wani irin shiru tay masa ta dan dauke kanta ganin batace mai komi ba sai yahau gaisheta, still taki ta amsashi..sai can kafin nan ta juyo muryanta wani iri iri tace"rayyan, wato mummunan abu irin haka na faruwa a gidan ku shine ni mahaifyrka bazaka dauki wayarka ka kirani ba ko??

....zai magana cikin masifa daya taho mata ido arufe tafara masa fada tana cewa "fisabillah what is the meaning of this rayyan?wai meyasa kaida bappanka kukemin haka ne?what are u ppl protecting me from.. nifa bance muku ina tsoron matarsa ba..,dont mistake me keeping my distance frm her as fear, sabida na lura da cewa kmr raihanatu batasan meke mata ciwo ba har ynxu. nd you guys have no ryt to keep this away frm me, that young gal is also my sole responsiblity, she cant beat nd bully her like dat kuma yatafi abanza kuna kallo, gaskiya nide ko kadan baku kyauta min ba ynxu da ankasheta da dukan fa kunyi ma uwarta adalci kenan? snn me zamuzo mucewa hajiy mairo after she trusted us with her..

zai magana ta kara daga mai hannu fuskarta a dore while her words are still calm cikin nuna bacin rantan a fili tace"please be quiet it is too late for your explanations young man. bana son jin wani uzurinku..muje ciki kawai in duba me jiki.

...gaba tay walking calmly and confidently like a queen jikinta sanye da wata hadadden all black designer dubai abayanta dayaji stones, her golden heels nd bag marar hayaniya to match da irin stones din dake jiki,

ibaad yafara binta abaya baya while tana dan sauri sauri tana jan ajiyan zuciya mai nauyi, wanda kallo daya kamata zakasan ko kadan bataji dadin labarin dataji game da abunda yafaru da ayaanahn yau ba...

she have a very important meeting on call saidai tunda anty hauwa ta kirata ta tsegunta mata abunda ke faruwa atake take tay cancelling komi tafasa zuwa meeting in tajuyo da mota tazo asibitin batare da ta kira bappa zaidun ba.
Chapter 52 · 0% Book details