← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 161

Sashe 149

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hajiya bata daddara ana daf za'a kira magrib ta sake dawowa ta mata. harsaida sukayi haka na tsawon kwana uku snn ta kyale ammi karama, ta dawo kuma yamma zata dama mata nonon rakumi da wani gari aciki ammi ta tsane abun nan ammi haka zata tsaya aknta tace mata wallah sai tasha. bata wasa da ita.

wani bin har taji kmr zatay amai amma haka zata sha tun tuna guje ma abun harta hakura ta sake ranta hajy mairo tace mata daga tay aman jini maza maza tazo ta gaya mata tace toh amma haryau dai batay aman ba tukuna

ana kkrin shiga sati na kusa da karshe kafin aure ayaana suka gama exams aka musu mini walima agidan as usual sai yau uncle moh ya shagala ya fara nuna zumudinsa a fili
irin reaction din kallon tsana da haushi da anty safeerah tay ma ayaana yasa ana gama hidimar da yamma suna zaune da anty safeeran a falo ta shigo da duk wani kyautarsa daya bata yau din ta dauko ta dawo masa dashi agaban matarsa tace masa ta gode amma bazata iya karba ba

tambayar duniyan nan yay mata agaban matarsa ammi taki ta amsashi firrr haka ta kama hanyarta ta fita

anty safeera tana jinshi ya dinga bambami yana daurawa ibaad laifi kan kace wani abu suka fara musu da matarsa

tace masa karya wani lakama ibaad, kowa yasan ibaad has travel ba a ma samunshi awaya kawai de yarinya ta gajine da haukar da yakeyi kawai inzai bari ya bari, tace masa ga dansa mujaheed yana son ayaana kuma next week zai dawo auren zainab gida what if mujaheed yazo yace yana son aurenta haka kenan zai cigaba da wann creepy bvhrs din bayan yarinyan ma bataso amma sai yana cusa mata kai yake?

yadda tay maganan da zafi da kuma gatse yasa ransa ya balain baci sai baice mata komi ba kuma yana gani ta kwashe gift din su abun wuyane da atampopi da su takalma kaiwa dakinta tay tay kasonsu da sunan yan uwanta,yay zuciya bai kwana a dakinta ba ita kiwa sasafe ta kyauyar ma yan uwanta komi dake ciki.

akan wann abun saida yay kwana biyu baya mata magana abun sosai yay mata zafi...

bayan komi ya lafa su ayaanna angama secondry tunda ibaad ya tafi saudaya ta samesa awaya sukayi hira me tsawo har yau bata sake jinshi, bappa zaidu ma sao yazo yay tafiyan shima haryau dai basu dawo ba gashi anata shirin bikim nan saura kwana goma sha biyu ya rage musu kacal

bayan komi ya lafa ranar wednesday tsakiyar sati amarya zainab arifah ta dawo gida ita da babanta da babban aminiyarta nala sabida su shirya ma biki atare., her weding dress wanda zata saka shi a ranar daurin aure nd everything komi is on the processs week din auren zaa kawo mata komi.

already kayan da suka siya kuma acan kasar wajen suka bari masu aiki zasu jera mata su a new closet na agidan mijinta a UK

nan shirin aure kawai sukeyi, she still on her drugs amma tuni ta katse shan kwaya mai bugarwa dan iyayenta su tabbata lafyarta kalau, kowani dabian banza duk ta rage, dan kar ace bata hankli har yanzu wani abu ya kawo cikas ma aurenta she is still deeply scared maganam rukky
tana Allah Allah ayi auren ya wuce kar maganan rukky na cewa bazata aure ibaad ba ya zamo gaskiya..

bayan dawowartan ne garin kuskus hajiya hamida tajiyo wayar da prof yakeyi a falo da mamansa, yasata a handfree yanamai jadadda mata cewa ya gayyaci manyan mutane dan Allah kar azo a kunyatashi kuma wallh inhar ibaad ya saɓa dokokinsa ya kara cutar masa yarsa zai musu haukan da basu taba gani ba, mita ya dinga mata yana gaya mata uban kudin daya kashe wajen jinyar zainab yace ai likita yace yanxu abu kadan ne zao iya dawowa mata sa ciwo dan haka dole ne ibaad din yay hakuro su zauna har sai hanklinta ya dawo jikinta kafin duk wani abunda zai biyo baya yabiyo baya...

she have no choice face ta gaya masa toh de auren nan bana yarsa shikadai bane kaninsa karamin ma zai kara mata duk kuma a llco daya zaayi auren gabaki daya. yace shi bai damu ba kawai de lafyar yarsace damuwrta kar sake ayi wani drama da zai maida jinyar zainab baya musmn ma da likitoci suka yi gargadin bata gama warwarwa ba. shikansa baisan zainab din bane ta biya aka harhada masa wnn report din dan ya matsa ayi komi cikin sauki..

hajiya hamida najin hirar tazo ta samesa sukay maganganun banzansu akan auren uncle mohd dinsuka gama,

prof yace ai duk zuciyar kuruciya yan uwan nasa suke dashi hakama babban yayun su marigayi mustapa yaje ya auro yar kwaila, shide haryau wnn maganan auren ammi karaman da baban ibaad din yatsaya masa a wuyarsa sosai

bayan kwana daya da wann maganan ranar friday ana gab za'a shiga week na hidiman aure anty safeera ta kira hajiya hamida akan batun waliman gida da za'ayi na kawayen hajiya hamidan a mansion din su zainab bayan daurin aure

tana yatsina tace ita
wallah bazata iya gayyatar matan gidan su waliman zainab agidanta ba ita din kawai tazo ya isa.

anty safeera tafara rokonta tace gaskiya bazai kyautu ace ita daya kawai zatazo waliman auren zainab ba....

hajiya hamida tace ke safeerah bari kawai na fito na gaya miki akwai wata tsinanniyar bazaura agidan nan naku mijina babu sanda za'ayi maganan gidanku bai ambace sunan ta ba kinga kuwa maganin bari karma afara

wani irin tuntsirewa da dariya anty safeera tay tace haba haba anty hamida meyayi zafii? to wallh ki ma kwantar da hanklinki bappa zaidu yariga yay marking territorynsa kuma ma soyayya sukey auren ne kawai baiyu ba da anjima da yi bakiga shiyasa basa jituwa da ammi babba ba

hajya hamida tace what ever..kawai dai bazata kara zuwa min gida na bane..kinsan ai dama zayyan da zaid yan biyune mai yuwa suna da abun maitarsu na son abu daya, gara na datse tun yanxu shi mijina yana gane cewa yana son abu toh wallah sai ya samu koda kuwa kashe dan uwansa zaiyin

anty safeera ta kyabe baki tace toh ba damuwa anty hamida i understand nima ai bazanso amiki kishiya ba

hajyy hamida tace hmm shine ke kika bari za'a miki kwanan nan? wallh safeera kin ban mamaki da kyanki da iliminki zaki zauna namiji har ya miki kishiya kuma it seems like ure even happy abt it..ni banga alaman kinma damu ba ,ke ko irin kishin matan nan baki dashi

kirjin anty safeera ma bugawa tara tara tace tsaya anty hamida bangane za'a min kishiya ba..ni din?? anya kinji da kyau kuwa..ni wallh mijina bai taba mafarkin zaimin kishiya ba i use to go tru his phone sumtimes baida wata budurwa ma

hajy hamida tace hmm safeera kenan, it seem like ure abt to be shocked!! nide ba abaki na zakiji gulma ba amma wallh uwar mijinki ne jiya ta gaya ma alhaj cewa aure biyu za'a daura dana zainab dana kaninsa muhammadu

wani kalar dariyar mahaukata mai karfi anty safeera tay kafin nan ta fashe da kuka abazata batace komi ba ta katse wayar cikin sauri

hajiya hamida tay kwafa tace hmm yanxu sai ace na hada waje kenan ko???hehehe toh Allah ya raba lafiya

****
wani irin haukataccen kuka anty safeera tay for a moment in shock, dan tasan dai hajya hamida bazata taɓa mata wasa ko karya ba...saida tay kukan sosai dan shock din ya fice ajikinta snn ta share hawayenta ta fita tana jan zuciya luckly enuf tana sharoro kwana kuwa taji muryansa a daki yana kan maganan auren da wani abokinsa ta labe a bakin kofa taji yana kyakyatwa da dariya harma maganan ma anko sukeyi na abokai..

lokcin wani hajijiya ne ya fara juyi da ita dan batamasan awani duniya take yawo ba dan tay kamar bata sama bata kasa bata tsakiyar kamr a iska kawai take yawo kirjinta yay nauyi kamar an daure dutsi a haukace ta shigo dakin tana huci suna hade ido yay maza ya katse wayar ya mike tsaye yace "lafya kuwa Safeera what is dis zaki shigomin babu sallama u cud run into my private conversations

ɓari gabaki daya jikinta ya farayi maqudaan hawayen datake kkrin dannewa suka watso mata a lokaci daya akan fuskarta suka sauko baja baja tana kallonsa kamar zata kasheshi the call has already confirmed everything to her

muryanta har yana amo tace "i cud run into ur private stupid cnvrsation ko kuma wani munafurcin kake kullawa abayan ido na bansani ba

adan rude yace meye hakane kam safeerah pls what is wrong with you ne

wani dan uban mari ta daka tsalle ta watsa masa da ihuu tace "you are what is wrong with me muhammad...how dare u..how dare u ...how dare u plan ur weding behind my back, dama sau yaushe ne zaka gaya min? bai gama farfadowa daga marin ba tay wuff ta cakumo wuyarsa a borance tace sai ranar auren ne zaka tozarni a bainar jama'a sann ka gayamim cewa zaka min kishiyya. what wrong ive i ever done to you da zaka saka min da irin wann walakancin

dakyar ya fincike hannunta da karfi ya riketa muryansa na rawa rawa guilt ya gama rufeshi dan yama rasa me zaice yafara bare bare yana cewa "safeera is not what u think...i was going to tell u bansan ya zan gaya miki bane
..you knw i love u..i care about how you will feel shiyasa ban gayamiki

kara fashewa da kula tay a mugun haukace tafara cewa "so, now you care abt how i will feel..amma da banji awani waje ba wallah da bazaki gaya min ba...kai durun uwarka, inka sake cewa you care about wallah saina kasheka, banza
..munafiki kawai,, wallh i dont deseve this frm you.., ranta a mugun bace ta fara kai masa duka tana cewa wallah baka isa kayi auren nan tunda ata hanyar munafrci zaka yi..u want to embrass me...inkaga kayi auren nan it will only mean i am dead. wallah wallh ka gwada kagani..
Chapter 149 · 0% Book details