← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 161

Sashe 88

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

⏯️3️⃣1️⃣
rayuwa na tafiya ne daban daban akowani bangare mafi akasari kusan kowa yana yin abubuwan dake gabansa ne wasu abubuwan ma ba a sanin faruwarsu sabida hajiy mairo da workers dinta duka yanxu ne suke ta kkrin suga sbwr wajen sana'arsu ya tsaya, sai tay sati bata dawo cikin family house ba musmn ranakun da take jimawa ashago toh a gidan bappan zaidu kawai take kwana wekdns sai ta dawo gida,wanda sanadiyar haka ya saka ammi babba samun kwanciyar hankli da sauki wnn kishin jigilar da bappa zaidu yakeyi a family house kwana nan yaragu mata sosai, ynxu kusan 50-50 akey, inba hajya mairo tana can ba sam ammi babba bata barin shi yana zuwa inda fatima take haka kawai batare da sunje tare ba dan haryanxu tanakan zargin fatima tana kan aikata wani abu ta hanyar bawa mijinta abinci dan ta kwace matashi.

daga bangaren zainab Arifa kuwa wannan tunanin yarantar dake yawan damunta na tunanin cewa mahaifinta zaisaka ibaad yajuyo ya fara asalin sonta cikin ikon da babanta yake dashi ahnkli komi yafara gushewa..

zatazo weknds din amma banda kwasar raini da iskancin su sultanah babu abunda take sha,kusan hardly ibaad yake samun lkcinta a wknds din ma musmn ma ayaana ta fara karatu, all the time tazo zata samu in one way or the oda lamarin ayaanah ne kawai ke gabansa, tun bata noticing cewa yana bawa ayaanah attention fiye da kowa har tafara ganewa sosai,wata rana in taga yana ma ayana tsauri akan karatu ko hira acikin mutane sai taji dadi ta dauka kmr yadda yake ma sauran itama hakanne.. but as time goes on, taga kmr komi yana canzawa ahnkli, sam sam ibaad baison ataba ayaanah,, but she neva tells, ko labari zata bayar tafi dauko wajen da babu dadi just to convince herself dagata fara bawa kawayenta labari yadda yake ma ayaanah tsauri wajen karatu dan su kara kwantar mata da hankli, sai kuma kawarta rukky tafara mocking inta tana cewa ai wann kulawa ne na musamman bawai tsanar ayaanah yayi ba.

tunda rukky tafara mata wann gorin abun ya dinga damunta, dake tana da ilimi duk yadda taso ta karyata abun acikin zuciyarta within few weeks datake zuwa gidan kowani wkkend tana lura dashi sai taga kamar batun rukayyan gaskiya ne kmr ibaad is over protective nd sensitive akan duk wani abu daya shafi ayaanah haka kawai sai taji hushin yarinyar datakeji aranta ya fara dawowa tsana me tsanani.

last weeknds datazo abun ya fara nunawa a fuskarta sosai...tafara kushe halin ayaana awajen mujaheed tana ce masa yarinyar bata da kunya bata nitsuwa kuma ana barinta tana aikata abunda taga dama ibaad baiya mata komi.

Duk yadda mujaheed yaso ya kare halayyar ayaana kuwa saita kusheta, ta dawo tana iya magana da kowa ayaran gidan amma koda ayana ta gaisheta bata amsawa, ita kuwa ayaana dataga hakan su kulthum suka kara zugata ta dena gaishetan me gabaki daya, this week datazo weknd da haushin hakan takoma gida, monday tana zuwa schl takasa gane komi kawayenta suka ce mata ai yanxu ne daidai takai kararta wajensu hajiya ko ta hada mata wani mugun sharin da zai ɓatata awajen ibaad snn ta nuna ma yarinyar matsayinta awajensa. abudai sukayi a shirme da yaranta tanata Allah Allah asabar ya sake zagowa.

ata fannin uncle moh kuwa
duk dama yasaka ayaana a list dinsa na future wife amma babu abunda yake sakashi duba lamarinta face sai yaga wani abu dabazaizo dede da ra'ayinsa ba yake saka baki,

sai aukin janta ajiki da abun duniya idan sunzo su da kulthum gaishe sa tare da anty safeera, haka zai bata kudin wankan kowani juma'a da su kayan kwadayi kowa ya dauka tausayi ne da sassauci irinna manya

saidai haka kawai bai taɓa suggesting wani abu babba na kawo cigaba a rayuwarta ba,saidai ya zuba ido, idan bappa zaidu ko ibaad sunyi yaga abun bai masa saikaji yafara korafe korafe yafara burgan zai kara kudi ayi har abunda baima yaran cikinsa ba saikaji yana mgn ama ayaanah

yana balain jin haushin da ibaad yake da cikakken iko akanta, wanda ko anje gaban hajy mairo sai yaga tabi bayan ibaad din. gabaki dayansu basu gano uncle mohd ba duk sundauka kawai kowa yana iya bakin kkrinsa sbida rike amana da biyayya ga hajya mairo basusan uncle moh kkrinsa makansa kawai yakeyi ba.

dakyar da wahala ya dena wasu abubuwan, yaji haushi ya fita a sha'anin rayuwar ayaana yafara saka karfi da karfe wajen neman kudadensa sabida manya manyan construction contract din hanyoyi da gidaje yake yawan samu na qwmanti bakaramin millions yake dauka ba...

Daga haka ayaana ta fara samun sauki daga fitinarshi saboda batajin dadin yadda yake ware yan uwanta harda yar cikinsa wajen mata kyauta, ita kuma yayta bata kyautan kudi da kayan kwamulashe wanda har yau bata sake ibaad yasan da haka ba sabida tanajin tsoronsa masifarsa sosai.

washe gari asabar wanda monday me xuwa su ayaana zasu fara exams akwai tulin pressure akanta na son taga taci exams dinann gashi ita atsakiyar session din dama ta datsa kuma she need to pass bfr she fully gain her seat in her class,iyaka farin jininta a schl yasaka ta samu masu sanar da ita abunda aka musu abaya intazo gida sai tay ta koya da taimakon lesson teachernta mr samuel sede wasu abubuwn duk da lesson teacher yana mata amma dake a kuraren lokcine kuma akwai anxiety na fear of failure sai bata ganewa sosai

daren jumaa dakyar tay bacci huge space ne tsakaninta da safiya dan haryau kamar wuta da auduga suke zama wani baya taba kayan wani kullum safya ta kalle fuskar ayaana sai taji duk duniya babu wacce ta tsana kmr ita dan gani take sanadiyar ayaana ne yaa ibaad yake yawan zuwa gidan
yake casata

babu abunda yafi kona mata rai kamar rabonta da kallon series ynxu takai wata guda kenan sai dai tay aboye sai ta dawo batama gane komi, dum lefin rugujewar jin dadin rayuwarta agidan ta dorasa akan ayaanah, duk takuri da masifar yaa ibaad kuma bata taba ganin ya taɓa jikin ayaanan ba, sai tana ganin kmr fifita ayaanan shima yakey akanta kmr amminsu shiyasa ko kadan bata kaunar ayaana ita kuma ayaanah ko ajikinta sabida kulthum tana yawan dauke mata kewa in basu komi

sassafe ranar sartuday din kowa ya hallara a family house, saidai wnn wknd din was very boring nd quiet hatta
mujaheed yana kkrin yin exam ne kowa kansa yay zafi dake gidan duk guraye ne kowa na takansa anata karatu a dfrnt spot manyan ne kawai suke ciki sashen hjy mairo

hidiman shago was very overwhelming musmn ma da yanxu aka fara tadashi, ammi karama ma tuni ta koma bakin aikinsu na foundation kowa dai kansa yay zafi.

as usual kusan bayan asr wann karon zainab Arifa taxo amma bata tashi zuwa ita daya ba sai tazo da kawarta nala dan tafijin dadin harka da nala dake kusan ita tafi bata shawarar masu tsauri ita kuma rukky wata rana takan gaya mata gaskiya koda bata son shi musmn akan ibaad shiyasa sam bata fiyeson yawo da rukkyn ba.

sunsha kwalliyarsu na kece raini sunyi kyau kamar ba yaran scndry ba, suna zuwa kuwa cikin cin sa'a suka same su safiya a waje tana wanke fuskrta a famfon waje babu yabo babu fallasa ta gaishe su suka amsata da sakin fuska kamr basu ba, kai tsaye suka tambayeta ina ibaad tace musu ai yana falon amminsu shida yaya mujaheed yana koya masa wani abu tace mata toh shikenan, yau ko sashen hajy basu leke ba sabida dressing inasu kawai suka wuce ashen anty safeera

falon babu kowa face book din safiya da alama ita dayane anan zainab arifah ta kalleta tace safiya pls kije kiramana yarinyar kauyen nan ta kawo mana ruwan sha ynxun nan

itakanta safiya ta sha mamaki da request din amma dake abu ne dazai walaknta ayaana sai ta amsa da toh ta haura sama da sauri taje daki ta samesu dukansu akan gadon kulthum kowa da book dinsa agabansa dakin yayi wani irin shiru sunata karatu..

motsinta kawai sukaji abayansu sukajiyo suna hade ido ta bata rai tace ayaanah wai inji anty zainab arifah ki sauko ki kawo mata ruwan sha taxo da bakuwa..

da dumbin mamaki kulthum tace what? wata ayaanan

..sultana tace bar fitinniya wallh zaki samu karyatake ita aika taxo tace ayaana

safiya tace shikenan kiyi tazama Allah yasa taje ta gaya ma yaa ibaad ankiraki kinki xuwaz hala munafurcin dakike min ne yaukema zakiji irinsa ajikinki Allah yasa ya miki shegen duka aikinsan budurwansa ko??

ayaana tay kamr zata sauka taje ta gani ma idonta sai kulthum ta rigata sauka da sauri taje ta leke tagansu zahiri tanaji safiya tana ce musu anty zainab arifah nagaya mata amma zagina tay tace min munafuka wai kuma ace miki bazata kawo ruwan ba baki da hannu ne ko bakida kafa...

da sauri kulthum ta dawo tace 'guys ashe dagaske ne...gashi sultana taje tanata gunduma miki wani mugun sharri wai kin zageta kince bazakizo ba..

sultana tace to sai me? dama ayaana ta saba debar mata ruwan sha ne? ai akwai masu aiki agidan nan,..ita safiyar mesa bataje ta debo musu ba
abeg ayaanah stay here koma miyene kin fada din..itade ayaanah batace komi ba.

daga falon kuwa safiya tasha mamaki dataga zainab arifah bata dau zafi ba, cemata tay kawai taje kasa ta kira yayanta ibaad tace masa he is needed urgently here karta dake ayaanahnsa yaji haushi

safiya tana fita suka haura sama ita da nala sukayi kane kane abakin kofar kulthum

ayaana ta mike tsaye batace musu komi ba su kulthum ma basuce musu uffan ba kawai nala tana shigowa ta fixgo ayaana tana cewa kece ayaanah ko? waye sa'anki acikinmu da har xamu aike ki kice mana bazaki xo ba
Chapter 88 · 0% Book details