← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 161

Sashe 157

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan yay shiru koda ammi tazo falon hajiya sosai tasha mmkin ganin bappa suna gaisawa har dacan zai fara tuhumarta da fushi sai tay saurin nuna masa wayarta da yadda ta dinga nemansa sosai tun ranar da abun ya fara faruwa..

batai kasa agwiwa itama tahau gaggaya masa ababen da ya faru baya rage masa komi ba ranta a dagule hartana hawaye, wanda hakan ya bala'in shan bambam da karyan da hajya mairo ta gaya masa in favour of her son muhammad,sosai ran bappa zaidu ya hargitsa ya baci har jikinsa yana ɓari ɓari yanajin wani irin balain mamakin son zuciya da rashin hankali irinna dan uwansa muhmmad da kuma rashin girma da hajya ta nuna acan case din gabaki daya

ammi karama tagama share hawayenta kenan saiga su hajyan sun dawo, ammi babba ne agaba da katon hijabi dan kwata kwata 20 min past 10 ne kuma 11:30am sharp zaa je masallaci a dora aure wanda anriga ance tun sassafe ma manyan bakin prof suka fara hallara anata shirin daurin aure.

ganinsu datay cirko cirko ganan fatima na goge hawaye yasa taja tsaki ahnkli tabar musu falon tawuce sama domin duba uwargida safeera

tun data barsu a falon case kawai akeyi tsakanin bappa zaidu da hajya akan batun auren ayaana, wanda sai yau ammi karama ta fitar da abunda yake ranta ta gaya ma hajiya cewa tana nuna ma ayaana warayya da rashin yarda da kuma zargi snn bata tantance magana inda akan ayaanah ne kawai daukawa takeyi.. suka fara jayayya kowa na hawaye bappa zaidu har yagaji da tsoma musu baki ya zuba musu ido kawai yay shiru ya kyalesu dan sugama fitar da abunda ke ransu kafin ya fadi abunda ke tafe dashi

fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan,tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa tsabr wayonta da kkarinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma anty safeera duk wani sirrikanta na cewa boka da ya mata aiki akansu tace har ta mutu agidan bappa zaidu baza a mata kishiya ba....

wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya

anty safeera ta share fake hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya

daga can kuma anata hayya hayya a falon hajiya can dataga fatima tafita gaskiya sai tafara musu rantsuwar cewa babu wanda ya isa ya hana yuwar auren nan. ita final decison dinta kenan. tafara ihu tana cewa wai duk an rainata inba haka ba ai rayyanu da safeera bazasu samu livern daga hannu su mata wani abu agidan nan ba.

ganin lokaci na tafy bappa zaisu yay gyaran murya
yace musu su nitsu su saurareshi shi ba wanm maganan bane ma ya kawosa.

bayan sun nitsun ne ya fito da hotonan ya rike a hannunsa, ya kalle hajiya anitse ya fara mata bayanin abunda uncle moh yace na cewa ya fasa auren

wanda tun bappa zaidu bai gama ba ta katsesa da ihu da bori tace sam sam laifin rayyanu ko kuma shine zaidun yaje yace ma muhmdu ya fasa shiru tay har saida tagama borinta snn ya dauki hoton yakai har gabanta yanuna musu da shi bai kalle video din ba ya bawa hajya suka kalla tare da ammi karama,duk jikinsu yahau rawa suka fara salati hajy ta rikito kasa ta kurma ihu tafara cewa ayaana ta tozarta....kusan wann ihun shi ya jawo hanklin ammi babba dan kuwa a falon anty safeera suka zauna suna kuma iyajin ihu akasa musmmn in yayi yawa.

a firgit ta mike da gurmi tace ke safeera bakiji hajya na ihu ba ne...cikin kyabe baki anty safeera tace "ihu kam ai dama ta saba sabida kuncacciya ce mahaukaciya in zakije kije nifa babu inda zanje ina nan, dama mujaheed kawai nake jira yazo in gansa tunda ban gayyace uban kowa awann taqadararen auren nasu ba

ammi babba tace hmm nikam dole najje toh sai na dawo...da sauri wauri ta fita ta nufi sashen hajy mairo har tana tuntuben dan kar ayi gurmi babu ita

tana fita anty safeera ta goge fake tears inta ta kwashe da dariya tace mahaukata...kadan kukaga gani..duk wanda yaci tuwo dani miya yasha..

tana daga zaune awajen jira take taji ance am fasa daurin auren kafin ta tura ma alhaji sauran balance her secret alhaj ba wani babba bane yaro ne dake mata aikin spy tun lkcin datake zargin mijinta ma shi take aikawa shago yana leka mata ayaanah yana kawo mata information...they change his name to alhaj sabida deals inta, bata so konan gaba asiri ya tonu kwata kwata a gane cewa itace ta siya deal da ruthy, tafiso a maida tunanin ga cewa wani namiji ne daban yake kkrin tona ma ayaana asiri dan ya tarwasa auren ta, alhajin ne ya kawo mata duk wani labarin rayuwar ruthy da case inta ma jim haushin ayaana da ruthyn takey abboye da tarihin gang dinsu har da bashin da ruthy take fama dasu, so she made him to do the deal on her behalf, yanxu haka ita kanta ruthy batasan cewa anty safeerah bane behind eveything duk ta dauka wani alhaj ne mai kudi.

daga falon hajya kuwa dakyar aka daga hajiy mairo akasa tana birgima tana ihu tana zagin ayaana, kowa jikinsa sai yay sanyi musn ma ammi karama da abun ya mugun daure mata kai cos ranar ayaana ai da ibaad ta dawo gida yaushe kenan har taje ta hadu da yan iskan gangs haka har tay a rayuwarta irin wnn illar?jin kamr bazata iya gane komi yasa tay shiru taja gefe tana tare hawaye...dakyar hajy mairo ta zauna akan kujera bappa zaidu ya kwace shaidun duka hannun ammi babba
snn aka zazzauna ana zama ya hade rai ya ja musu kunne baison yaji maganan awaje,

snn yace dole ne aji ta bakin ayaana dan haka ammi karama taje ta kirata amma kar wani acikinsu yace zai mata wani abu anan har sai angama mata tambayoyi.

hakan kuwa ya faru ammi karama taje dede ayaana ta gama bude windon ta jefar da kullin kayanta waje tana Allah Allah tajawo kujeran gaban mirror ta haura sama ta dira tafita ta backyard ta zille har ta fara jan kujerar taji ana mata kncking a mugun tsorace ta sake kujera sai taji muryan ammi karama daga kofa a raunace tace "ayaana kizo bappanku yana son ganinki nd pls be fast"..da fargaba ta amsa sabida jin kuka kuka muryan ammi datay she stood still for while, dan tasan is eida a mata adalci ko akara dulmuya ba but anyway ko an daura auren nan tariga ta gudura aranta cewa guduwa kawai zatay tunda yaa ibaad yace zaizo yanemota daga baya bata damu ba.

daukar red bridal veil din tay ta lulluba akanta tay wani irin kyau duk dama ba kwalliyar arziki ammi n ta mata ba but will the jan lalle da gyara da qamshin dake tashi ajikinta bakaramin haskawa tay acikin jan kayan ba.

cikin sanyin sallama ta shigo falon taga daga ammi babba sai ammi karama sai hajy mairo kusan bappa zaidun ne kawai ya amsa mata

mummunan fadi gabanta yay dataga irin walaknattcen kallon da ammi babba ta mata hajy mairo kuma ta wani dauke kai ta watsa gefe tana hawaye tana karkada kafa da tsananin fushi ayanayin jikinta

cikinsu ammi karama ne kawai bata dago kai ba amma hawayene ke zuba a idonta sosai na tausayin ayaana

kirjin ayaana na dukan tara tara ta tsuguna da ladabi ta gaishar da bappa zaidu ya amsa bayabo ba fallasa..

ganin basu da time ya fara mata bayani da tambayoyi tanajin shi tana amsawa ahnkli
she truly cant rembr anything bayan ganin ta datay ta farka a kasa ranar, tana maganan sai yay kamr raina musu hankli kawai takeyi hajya duk ta kara kufuluwa dataga ayaana bata amsa laifin ta ko daya ba.

kai tsaye bappa zaidu ya nuna mata shaidun jikinta da hannunta duka na rawa ta karba ta kalla tun alkcin taji kanta na juyawa bata dawo cikin hayyacinta ba har saida taji dirar kalaman bappansu na karshe...

(Recap page 1, wanda suka karanta page one basai kum nanata nan ba except akwai few abubuwan da zaku oya tsinta aciki wanda bansa acan ba) cigaban labarin nabayansa keep reading💋

Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar doguwar red colour bridal veil dinta daya rufeta rass har izuwa kasa ,A hankli jikinta yake rawa rawa koinanta yadau kyarma tsaban takaici da wata iriyar matsanancin ruɗani dake famar cinta acikin ranta wanda bazata iya fasalta yawarsa ba, wasu maqudan hawaye ne kawai suka shiga gangaro mata akan fuskarta yuuu wanda daga ganinsu kasan bata shirya musu ba.

yanayinta mai cike da jin tsoro da kuma tsananin tashin hankali tadada sunkuyar dakai ayayinda take agurfane a tsakiyar babban falon
Chapter 157 · 0% Book details