← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 161

Sashe 38

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hajy mairo da ba akasa da ita ba, nan ta tuma ta cafe zancen tace sam sam bata aminta da wann hukucin ba, inde har zata kwashe inata inata tabar tudu r yadda yakeso, saidan inshi ibaad din zai amince ya zama guardian in ayanaah, snn ya wuce da ita cikin kano ayau ta zauna agaban fatima kafin itama tagama parking din tadawo ta samesu acan.

ibaad yay shiru yaki cewa komi ba, duk rakin da hajy mairo tayi, taawure tace musu ita zata wuce wani kauye acan jigawa dan batason matasan garin majiya susan me tay bare azo a dauketa anan tudu aje kasheta a majiya. dan haka zataje can yankin jigawan dama tana da yan uwan mahaifyarta awajen, su irin fulanin tashin nn ne suna yawan zuwa kiwo zata nemesu tazauna awajensu kafin komi ya lafa...

haka sukasha kukan rabuwarsu agabansa da hajya mairo har gwanin ban tausayi...duk kudin ajiya dana jinya dake wajenta hajy mairo tace mata ta rikesu kawai halak malak taje tanemi tsira.

jikin taawure amatukar raunane ta juya, da shirin komawa cikin asibitin dan tay sallama da aayanah, ibaad yana gama shanye hawayensa daya kusa zubo masa ya bi bayanta anatse ya tsareta, saida suka koma can gefe inda babu idon mutane akansu ya tabbata she feel safe with him, snn ya mata bayanin duka duka manufarsa akan hajiya da kuma ayaanah, sosai ya zage ya nuna mata cewa ya fahinceta ya gane halin datake ciki kuma karta damu, yay mata alkwari zai tsaya mata akan yarta har tasamu tay karatun, he will be her quide, snn ya ciro wallet dinsa duk ya rasa inda zaisamu paper, sai ya rubuta mata number wayarsa kawai ajikin sabon dubu daya, snn ya kara fitowa da sabbi sabbin 1k notes din masu yawa baima kirgasu ba ya damka mata su duka ahannunta batare da ya sake hannuntan ba yace mata "Dan Allah kartace masa a'a, tay amfani da kudin duka tay kudin mota dashi, taje duk inda zataje tanemi tsira daga juma snn duk abunda takeso kawai ta kirasa he promised her dat yarta will be in safe hands with him in sha Allahu..

yana maganan nan kawai kuka taawure take masa kamar zata cire ranta, dan bata taɓa samun wani wanda ya iya karantar duka turirin damuwa da baqin cikin dake yawo aranta ba kamar shi..yaro ne, amma gashinan da hankali da tausayi da halin manya atattare dashi.

cikin nuna mata tausayi da girmamawa ya tausasata da kalamai masu sanyi ya kuma lallabeta har saida ta amshi
kudin, fadin irin albarka da godiyan data masa ranar bazai kiyascu ba, ganin lokaci na tafiya yasa tay marmaza ta karasa ciki dan tay sallama da ayaanah

babu wani bata lokaci
tadagota suka rungume juna ta masa nasiha masu ratsa jiki tare da jadadda mata cewa mutuwar inayah ba shine karshen rayuwarsu ba, su hada hannu sucika manyan burikan su, tay mata hakan, dan tasan inayah zatafi jindadi in rayuwarsu tay kyau ba muni ba,
..,snn umarni tabata akan da tay ma ibaad biyayya, ta kallesa a a matsayin dan uwanta kuma yayanta karta saɓa masa..tare damata alkwarin wata rana inkomai ya lafa zatazo har kanon ta nemesu...

gabaki daya ayaanah ta raunana sai tanajii kamr magangnun sun mata tsauri da mugun nauyi dan bama ganewa take ba dan bakaramin kukan rabuwa da mamantan taci ba, haka kuwa tana kallo taawure tabar asibitin taje waje tasamu ko magana ibaad basuyi da hajy mairo ba.

sai fushi take dashi wai yaki karban ayaanah, taawuren tana zuwa ibaad ya mata sallama sukayi bankwana sai yawuce ciki yabarta da hajiya.

anan ne ta sanar da hajiya duk yadda sukayi dashi tabi ta nuna mata kudin daya bata, duk mamaki saiya rufe hjya, suna hawaye ta rakota har waje ta tsare mata abun hawa har saida taga tay nisa snn ta dawo.

dawowarta kenan tazo ta samu har ibaad ya gama biyan kudin jinya da duk wani abu da ake binsu ita sai tawuce ta dauko ayanahn suka fito, tun da suka kama hanya, basuyi wani magana ba har saida suka isa gidanta nan ma sharesu yayi ya hada ruwan zafi a heater yayi wanka yazo ya samu hajya ta sa anhado masa break fast mai nauyi yazauna yana ci itakuma ayaana aka kaita wajen wanka

hawaye duk yaki tsayawa a idonta dan duk inda ta zaga a gidan saitaga kamar zataga addanta da mamanta, she was seriously ill, nd grieving. gabaki daya memories dinsu yanata dawowa mata kai...

dakyar ta shirya adayan dakin hajy mairo ta sakata dan dole taci abinci snn aka kawo mata riga da zani brown colour na coté d' ivoiré kayan yama mata oversized ma amma haka ta saka tana gama cin abincin bacci me nauyi ya dauketa awajen..

tsakanin ibaad da hajiya mairo dakyar suka sauko sukafara magana musmmn data fara tsokanoshi da batun alherin da yay ma taawure, ya hade ransa tamau, yace mata aidqma can ta daukesa mugu ne shiyasa bata yadda dashi ba, dan haka karta damesa kawai tunda zai wuce kano da yarinya ta gaya masa exct ranar da zata gama tattarawa ta dawo gida itama.

badon son ranta ba hakanan suka warware maganan, aka sa ranar, 14days lissafin ranar da zata gama parking da kudin sallamar wasu wokers intan, da wanda zata basu incharge dan su cigaba da mata sana'ar abincin anan tudu dan akwai katon gidan almajirai datake ciyar dasu atunaninta inhar tabar tudu gabaki daya wazaina ciyar da yaran nan. duk suka gama lisasafi, taso ya bata tsawon wata guda amma ibaad yace sam sati biyun kawai ya isheta tunda tana case da yan ta'adda. shi zai gaya ma bappa zaidu da uncle moh ranar tahowarta inyaso za'a kawo mota kawai azo a dauketa da tarkacenta gabaki daya.

ganin babu yadda ta iya dashi yasata kyaleshi, ibaad ne kawai yake iya mata haka tayi shiru saboda sosai take kaunar sa aranta duk dama koyaushe acikin fada zaka same su, jim kadan bayan sun yi hirar karatun sa yace mata shi zaiwuce kano yanxu sabida zai kai ayanahn asibiti adubata acan

wajajen karfe 10:30am saura nasafiya aayanah ta farka duk baccin bai wani isheta ba, haka haj. mairo ta sakata agaba tay mata nasiha mai shiga jiki, duk kusan irin abunda taawure ta gaya mata ne dazu akan tay ma ibaad din biyayya sann ta sani cewa mutuwar inaya ba shine karshen rayuwarta ba, nn ta hadata da ibaad din ta musu atare akan suy hakuri su zauna lafiya tunda qaddara ne ya hadasu. shide baice komiba harta gama surutun ta within few minutes ya fita yabarsu, yagoge motarsa tsaf, yana shigowa yadau jakarsa yace mata kawai su tashi shizai tafi yana da practicals karfe 2 na rana..

daga ayanahn har hjy mairo kuka sukeyi rungume da juna tazo tasakata a mota harda sakamata seatbelt yana sallamar kakansa ko kallo daya bai kara ma ayanah yasa kai ya kunna motar suka kama hanyar kano.

tafiyar kurame sukayi banda kukan da ayanah takeyi babu abunda kakeji, baison yace mata tay mai shiru ba dan yariga yasan abunda takeji is alot to carry, ga zafin mutuwa gana abunda yake faruwa da su, iyaka da abun ya ishehi ya kunna karatun qur'ani ya dan kure musu volume tun tana cigaba da kukan har zuciyanta yay sanyi tafarabin sautin karatun da zuciyarta tana tuna addanta inayah, her fav thing in this world was qur'an ..sai kuka mai zafi take tana tuna irin murnan da sukayi ranar da inayahn tay sauka har bacci me nauyi ya kara daukarta.
ABUNDA KE ƁOYE
SURAYYAHMS
08060712446

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[07/11, 20:04] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ⏯️1️⃣7️⃣Abunda ke ɓoye

bayan tafiyarsu hjy mairo na shiga gidanta ko aje mayafinta batay ba matasan majiya suka diro kofar gidantan yuuuu wai sunzo neman taawure haka hajiya mairo tabirkice da ihu tahau sauke musu bambalastar ruwan bala'i ta tara musu taron jama'a tabi tajuya maganan kaf akansu tace sune suka sace mata yar rikonta taawure dan haka kawai ace musu su fito mata da yarta ko kuma hukuma ne zata rabasu, haka akayi ta hatsaniya tsakanin matasan majiya da hajiya mairo, can dai da sukaga ta fisu bori tanace musu akan su susuka sace taawure tabita laka musu harda sharrin da ko shaidan bai isa ta ciresu aciki ba ahaka ahaka abanza aka bar maganan suka koma garin majiya batare da sun cimma komi ba, ga dumbin zargin su na tunanin taawuren tazo nan duk ya gushe, basusan kuma ina zataje bayan nan din ba, yau dayakamata ace ranar farinciki da samun daukaka ne awajen juma sai ya zamo masa tamkar wata baqar rana dan bakaramin muguwar asarar dukiya taawure ta masa ba,

shikansa dakyar ya tsira da ransa, sanadiyar wasu fatake masu fitowar jeji da sassafe da sukaga wuta na tashi a rumbun abincinsa suka kawomai dauki yau kaf garin majiya sai da aka tashi da labarin abunda ya faru da juma masu tausayinsa suna yi mahassadansa masu masa dariya suna kai, yau tsabar baqin cikin ganin konewar dukiyarsan kurmus koda aka kwanceshi ya fito sarari suma kawai ya dingayi ana yayyafa masa ruwa...

yarasa meke masa dadi, gashi yafi kowa sanin cewa da akwai kakkarfan aikin tsarin jiki na usalin fulanin daji ajikin taawure da yayanta, yasan koda zai dau fansa ta hanyar musu sihiri ko sammon da zaisaka rayuwarsu ya lalace bazai iya ba saidaima abun yadawo kansa..

iya ka dabbobinsa ne kawai tabar masa su araye ahakanma waidan bataso ne tay ma abu me rai azaba da wuta yasa bata konasu da ransu ba.

ranar gabaki daya duniyar juya masa ta dingayi yanata suma ana dagashi yana komawa musmn ma da aka dawo gida akacemai ba aga inda taawuren ta nufa ba duk anje har tudu suma can tudun nemanta akeyi har ansaka hukuma ajeji suna nemanta. yau ya kasance ma juma ranar tsananon bakin ciki da jimami wanda bazai taɓa iya mancewa arayuwarsa ba.
Chapter 38 · 0% Book details