← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 161

Sashe 48

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tasaka wankakken atamfarta na jiya ajikinta tsaf tahau kan sallayansa tanakan biyan sallolin dake kanta ahankli cikin nitsuwa. cikin sauke sihirtaccen ajiyan zuciy ya dauke ido akanta snn ya karasa kan table dinsa yabude ledojin ya hau rarraba musu abinci ya ware mata nata daban snn ya dauke nashi dana maheer yabar mata zallan natan awajen tanakan sallah tajishi daf da ita yana cewa inkin idar kizauna anan kici abincinki sabida ki samu kisha magani..

daga fadin haka ya fita da nasu abincin direct dakin maheer ya nufa ya bude kofar ya zauna akan couch jin yadda gajiya gabaki daya yarufesa, cikin bude ido da lunshewa yay bisimmilah snn ya bude zallan fruit salad din yafara ci ahnkli

bai wani jima da faraci ba kirar maheer ya shigo wayarsa, ya aje salad din akan table snn ya dauki kirar ya sanar dashi cewa harma sun dawo gida, abakin maheer din yakejin labarin cewa wai fushi ma ammi babba takeyi dasu shiyasa tabar gidan batare da tay komi na abinci ba kuma yau ta hana mei aikin su zuwa, shide ibaad baice komi ba iyaka daya sanar dashi cewa ya riga ya saya musu abinci.

within some min maheer ya dawo gidan lkcin daf ana kkrin kiran sallan magrib ya samu ibaad a dakinsa azaune, iyaka fruit salad din kawai ya iyaci daga nan bai kara taba komi ba,

shima sama sama ya zauna yaci rice nd chicken din suna dan hirarsu akan mujaheed da already ya sanar dasu cewa jiya ya tafi as fan club nawani football club dinsu acan south africa sai nextweek zai dawo.

maheer yacinye kazan duka yaci rice din kadan snn ya aje spoon ya miƙe aggauce ya shiga bathrum da niyyar watsa ruwa ajikinsa kafin nan su wuce masallaci..

yana wucewa bathrum ibaad shima ya tashi ya fita ya wuce dakinsa,yana turo kofar ya samu aayanah a tsaye duk ta rasa nayi jikinta na rawa rawa ganin aman data masa a tsakar daki gabaki daya tabata masa gogaggen floor dinsa sosai da amai.

kallonta yay tun daga bakin kofa sann ya kalle aman fusknsa a mugun harde ya karaso kmar mai aljanu "yace "Kee...waimeye kikayi min anan kenan kike nufi?

kafin ta bude baki cikin daka mata tsawa yace" kimin shiru da Allah, akan baki san hanyar bayi bane da zaki min amai anan?are u insane...

hawaye tuni ya fara sauko mata a fuskarta zirrr kamar ruwa,

acikin yanayin masifa ya fixgota tadawo gefensa ya kara kashe mata sound warning, tanata kuka batace mai komi ba har ya gama masifeta snn ya koreta tashiga bathrum din taje ta kunna sink ta fara wanke bakinta tanata kuka ahnkli.

tana fitowa tazo ta samu har ya goge wajen tass har yasaka qamshi me dadi, baice mata komi ba ransa adan bace ya wuceta yaje yay alwalansa still ya fito baiko kulata ba ya fita, jim kadan da shida maheer suka nufi masallaci, ahanyane maher yake tambyar ya jikinta wani shiru yamasa yay kamr baijishi ba dan sosai yawan kukan ayaana yafara kular dashi.

bayan sun idar da magrib ana jiran isha'i saiga nan bappa zaidu yadawo, daga haraban masallacin kofar gidansun duk suka rusuna suka gaishesa, bayan sun tattauna jikin ayaanah kadan saiya umarce maheer akan dayakai ayaanahn dakin sultana sudinga kwana acan atare. bayan nan dukan su ukun suka koma masjid domin gabatar da sallahn ishai

immidietly suna fitowa daga isha'i bappa zaidu yadauki motarsa yakara ficewa da alama can family house dinsu na rijiyar zaki zaije...

ibaad kuma har ynxu yana cikin masallaci yana amsa wayar mum dinsa, duk ta daga hankli tana so ta bar duk abunda takeyi tazo kawai fa amshi ayaanah, toh already bappa zaidu yaki mata sam yace harsai ayaanahn ta warke tass agabansa snn akai musu ita

she knows yana hakane dan kar ya bada wata dama da matarsa raihanatu zatajji aranta kamr ta kai, ko ta isa ta yanke masa wani danyen hukunci agdansa bisa akan abunda taga dama.

yaki sam ya bar kowa yazo inda ayaana take, duk yace musu subari sai tawarke kafin za'a kai musu ita can gida but for now dolene kawai agidan san zatay jinya, anty safeera dama bawani son rike dan wani takey har ranta ba shiyasa lamarin zuwan ayaanan bai wani darata ba iyaka ammi karama ne kawai ta damu da lamarin ayanahn sosai.

maheer ne kadai ya shiga gidan after isha, direct ya nufi dakin ibaad yana tura kofar ya samu ayaana tana kan sallah jikin ta na rawa rawa at same time tana hawaye sosai..

zama yay abakin gadon yana jiranta har ta idar tay sallama da mugun fargaban tunanin ko ibaad ne ya dawo ta juyo sai taga ashe maheer ne,suna hade ido dashi tabi ta sunkuyar dakanta can kasa tana kara tulowa da hawaye akwayar idonta.. tahowa maheer yay har inda take da sanyin murya yace "hi pretty one..kina lafya..?ya miƙa mata hannunsa yace taso muje..kin miƙa masa hanun tay tamasa shiru, yay murmushi ya zauna agabanta da muryan lallashi yace"kiyi haquri kinji??fadin hakan dayay yasa takara fashewa da kuka. dagota akasan yay cak suka koma kan kujera ya dinga lallashinta yana cewa "komi zai wuce pretty, kuma zakiji dadin zamanki anan duk abunda kikeso in sha Allah bazaki rasa ba kinji? duk yay magana bata amsashi..

tambayar duniyan nan yayi mata akan abunda ke damunta da abubuwan datake ya saya mata amma komi yace amsarta a'a ne, dakyar yazo gq rudeta da kalaman haquri har tay shiru, snn ya fito da ita har main falo ya zaunar da ita.

yana ajefan ya kara haurawa sama dauko abincin da suka ragen musu can saiga sultana tana saukowa, ganin ayaanah a zaune a falonsu ita daya yasa tay saurin isowa gareta, kallonta ta dingayi harta zauna a daf da ita, tay shiru cos she was confuse on what to say,musmn yadda ayaana ta sauke kanta can can kasa witout flinching
tay tsamamnin hala ma bataji motsin shigowrta ba, can cikin tattaro makanta ntsuwa tay gyaran murya, aikuwa a dan firgit taga ayaanah ta daga kai da sauri ta kalle direction inta,

suna hade ido for the first time hawaye me matukar sanyi ya sauka a idon ayaana dan tun da safe data kalli yanayin sultana saitaji hanklinta yaki kwanciya dan fuskarta da yanayintan sosai yake mata kama dana addanta inayah...

ganin ta zuba mata ido tana hawaye mai ban tausayi yasa sultana tay saurin tasowa ta matso kusa da ita da muryan tausayawa tace "hey, meyasa kike kuka kuma...ta dafa kafadunta kadan tace "indan mummynmu ne kike jin tsoro dan Allah kiyi hakuri kinji?suna na sultana al-mansur..kefa??

ayaanah tay kamr batasan me zatace ba tana jan jan zuciya ahnkli cikin muryan kuka tace "ayaanah".
da murmushi me sanyi sultana tace "ayaanah? oh wow nice name..toh ki dena kuka mana kinji?you nd i can be friends, i can even be ur sister...cewan hakan da sultana tay yasa taji raunattacen kuka mai yawa yazo mata itakanta bata san sqnda takara fashewa dq kukan sosai cikin tunowa da addanta inayah ba,...

gabaki daya sai sultana taji ta rude tana shirin budan baki zatay mata magana caraf sai ga ibaad yashigo ya tsaya cak daga kofa yana kallon su da wani irin murdadden murya yace "whats going on here?

da bala'in sauri sultana ta miƙe tsaye muryanta harna rawa rawa tace "nothing yaya...kawai fa magana nake mata shine naga tanata kuka..ni wlh banmata komi ba, bansan meya faru da ita ba..

fuskansa kamar na wanda bai taɓa dariya ba yace ma ayaanah "ke zo nan..da mugun sanyin jiki ta tashi tanata kkrin controling tears dinta kafin ta iso yay wuf ya jawota gabansa yace"kewai so kike na wanka miki mari ko?
a mugun tsorace ta girgiza kanta da sauri tana hawaye

yace toh uban meyasa kike son yin kuka, are u trying to sabortage ur treatment or what? kinga ina binki ahankli shine iskancinki yake dada karuwa ko?

budan baki tay cikin kukan zata bashi hqri cikin zare mata ido yace da Allah kirufa min baki, bana son ji, snn ki goge wann shegen hawayen naki kafin in fasa miki bakinki ynxun nan..

da sauri tafara goge hawayen sultana tay shiru jikinta na rawa rawa saiga nan maheer yana saukowa da robobin abinci..

kallonsu duka yayi yanamai karasowa yace meyeke faruwa anan?..pretty one are i okay..juyowa tay helplesly ta dan kallesa yace gama share hawayenki ki zoki kuci abinci da sultana saikuje daki tare kuyi bacci..

kai tsaye cikin iko ibaad yace "she is not eating!! bacci kawai zataje tay yanxun nan...ya kalle sultana a dakile snn yace" take the food for yourself, nd take her with you. inta sake bare baki kizo ki gayamin, saina mata shegen duka.. very stupid girl, uban waya yace miki anason jin kukanki...

yana fadin hakan ya haura sama yana jan tsaki..

wani hawayen taji ya kara sauko mata maheer baice komi ba ya mikawa sultana abincin snn ya bi bayan ibaad din da mugun sauri, ibaad na shiga dakinsa ko zama baiy ba saiga maheer din ya shigo fuskarsa adan dore yace"kaikuma meye haka zakana ma yarinya karama tsawa kana tsoratata"..and why wud u say she is not eating ahakan ne zata warke maka kafin sati biyu???

da bacin rai ibaad ya kallesa yace "you dont get it do you??maheer wallah am tired, nagaji, tun jiya yarinyar nan take bani ciwon kai while i was busy tolerating her amma batagani, daga tamin fitsari a atsakr daki sai takicin abinci, in kuma aka tursasata taci haka zata yi amai ta ɓata koina da kazanta, wai ciwon hauka ne? nifa kaga banason iskanci da sakalcin banza, yanxu fisabillah me ake mata datake yawan yima mutane koke koke

cikin lumshe ido da budewa maheer yace "dude she is just a child, just take it easy on her ko kaine akace sistrnka ta mutu snn qaddara ya raba ka da mum dinka rana tsaka wallahi bazakaji dadi ba bare wnn yar yarinya karama...
Chapter 48 · 0% Book details