← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 161

Sashe 147

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da kukkuni safiyan ta miƙe tareda rungumo shoping bag din tafita tana cewa kai ammi kwana nawa kenan ayaana bata miki aiki ba kullum saikice ni ni kamar nidin na mutum bace

ammi tace zan ci ubanki safiya ina data fara ciwon nan kawai kika soma shiga kitchen din karki sake kibata min rai toh

batace komi ta fita tana tura baki...ficewarta bada jimawa ayaanah ta shigo tay kyau sosai sanye da highwaist skirt da white tucked in short ta daura vintage scarf kalar skirt din jikinta ma wani irin sanyi mai dadi.

tunda ta karaso ta rusuna agaban ammi take kallonta da mamaki tace ohh oh su ayaana wato har rayyan yaxo kin samu sauki ko? adan kunyace tace ammi allura fa yamin kuma har yanxu wajen yana min ciwo bai warke ba
..ammi karama tay murmushi tace ai naji dadi sa allura ne tunda dai ke baki kaunar shan magani toh bagashi nan kin warke ba to muje kitchen yau akwai abubuwan da zan koya muku..snn zamuje GRA nasarawa can after munyi breakfs ayi spa, pedicure nd manicure,gashin kanki ma duk ya sake ya fara bushewa, ku shirya yau awajen zamu wuni.

murna ayaanah tafara cos this ryt here is her favourite part of the fun dan tana mutuwar son xuwa gyaran jiki musn tare da ammi karama sabida bakaramin gyaran take sawa a musi ba har siracin turare dana gashi ga vaginal steam da sauransu yaranta are alwys clean nd healthy bazakaga wani kalar dischge ko bashi bashi na tashi ajikn su ba tunda suka kawo girma.

Da murna tabi ammi kitchen suka samu safiya anan tana kan wanke wanke karshe ma ayaanah ta krba ta karasa kuma tay shara da mopping kafin suka gewaye ammi tafara koya musu wasu kalar breakfast na yan gayu

safiya haryau bata iya yin tuwo ko miya ba saboda bata ci tafison ire iren wnn english food in itakam shiyasa take mutuwar muradin bappa zaidu yakaita kasar waje karatu tunda tasan yayanta acan zai zauna in yayi aure tattaunwrta akan haka da bappa zaidu yay nisa shiyasa bata damu ba, and she think inde anty zainab ce matar yayanta ai kakanta ta yanke saka anty zaina nada son kyauta bata da takuri duk da rainin wayon ta amma tasan inta zauna agabanta zataji dadi

dagata dayan bangaren
kuwa uncle moh yana fitowa sallan fajr baiy kasa a gwiwa ba ya taho sashen hajiya mairo, yau kwata kwata fuskarsa ba asake ba suka gaisa har ta dauka ma rikici suka kwana yi da safeera, tun bata tuhumesa ya tuma yafara bambami sosai ta inda yake shiga bata nan yake fita ba akan tarbiyan yaran gidan

yace ma hajiya wallah sudai a zuriarsu babu mazinata sai in acikin matayen yayunsu maybe watta acikinsu akwai mazinata a zuriarsu, dan ya lura da take taken wasu agidan nan gabaki daya basa kama kansu, suna yawo da kananan yara suna kaisu hotel da dakin abokaina suna jimawa tare da su aciki snn sai su rudesu da abun duniya...

maganan sai yay ma hajiya mairo wani bambarakwai har ihu ta kusa masa akan ya fito filo ya ambce sunan wanda ya kama suna xina...yace mata shi bayason tada fitina yaushe aka gama case na zainab arifa azo ace shima ya dauko wani gulma kawai yana gaya mata ne tasan cewa shaidan zai iya shiga gidan nan..kuma zaa iya lalata yarinyar data kawo gidan nan amana ta damka musu
..sai kuma yace "inma basu suka haife ayaanah ba barasu iya bada shaidar halinta duka ba, shi gaskiy ynxu dabiun ta ne yafara bashi tsoro

hajya tanajin hakan sai kuma taji hanklnta ya tashi tace kai muhammdu dan Allah ka gaya minene ayaanahn take yawo tana aikatawa dan ynxu haka nima a kwai case inta ahannu na dan a shagon abincina naji ana gulmam cewa ta hade kai da ruthy gashi ance wai ruthy ta xubda cikin shege kuma tana kungiyar madiqo ni wallah maganan nan ya dameni amma nasan ayaana bazatay hakan ba aiba haka suka taso agabanmu uwarsu ba

ransa yaji ya kara hargitsa cikin karkada kai yace hmm hjy kidai kara bincike dan yaran nan fa ba ashan bakin su wallah. to bari ma gaya miki nasha kama ayaana tana fitar dare ma agidan nan

tun be dire ba hajy ta dora hannu aka tace laaa ha ila ha illahi, muhammadu??? a'ina ka kamata haka??? yaushe? kuma dan bura ubanka shine baka gaya min naci ubanta ba

saukar da muryansa yay kasa kasa yace aah hajiya bafa irin wnn dakike zato bane, farko dai da mujaheed na taba ganinsu sunfita da dare batare da sanin kowa ba, ko ina ya kaita oho sainaga kuma sun dawo gidan har ya sissiya mata abubuwa...hajy dan Allah karki gayama safeera wann magana amma tsakani da Allah dabiun da suke ayyanawa da mujaheed ne yasaka ma na dagasa akassr nan nakaishi karatu can china karyazo suna fitan dare yaje ya danne yarinya bamu sani ba ya mata cikin shege kinga kuwa mutuncinmu gabaki daya ne agidan nan zai zuba

hajiy ta dafe kirji tace ma shigesu, mujaheed din danake kallonsa salla salla ashe ko alwala bai iya ba dan ubansa shine zaina yawon dare a idonmu da yarinya balagagga? toh ai kay dede da kamasa haka Allah ya isa kukan danayi da zai tafi chana, duk na dauka anzalunci an turasa waje me nisa nayita tausayi ashe abun kunyar da yay niyyar jawo min kenan?

uncle moh yace toh ai bashi kadai bane mama...yo ba gara shi ba..jiya ai da kinji ina dukan ibaad agidan nan..

tace tooh?? me shikuma yay maka nide harga Allah batun dambenka da rayyanu ya fita abakinka wallah bana son nayi asarar haihuwa

yace hajiya kenan bakiga abunda yayi da yarrinyar nan bane jiya da ko bacci bazaki iyayi ba

tace meye ne dan Allah kadena samin fargaba kawai ka fito fili ka gayamin shidinma danneta ya tashi yi?

uncle moh yace "toh ni ina zan iya bada shaidar zina bayan a idona yakaita wani quest house suka shige ciki tare me gadin kuma yamin rashin mutunci yahanani shiga bare ma naje na musu fatata na dawo dasu gida

tace innnalillah wa inna ilaih rajiun kace kagansu ido ido

yace tabbas nifa har wajen nabibiyesu jiya nazo zan gayamiki ai nasamu kina tare da fatima karnafadi hsky agabanta kice na ci mata fuska na kira danta mazinaci amma tsakani da Allah hajya kiga ibaad yadda yay kato ya girma ya mallake hanklin kansa harshine zai dauko baligar yarinya yaje wani quest house sukebe acan kuma da dare shin menene zai gaya mata acan wanda bazai iya gaya mata anan gidan ba inbanda son ya lalata ta quest house ai baida maraba da hotel hajya..

kuka ta fashe dashi tace yanxu ina ayaanan take? amma wann yarinya ta cuceni daga wann sai wann ita ashe bazata aje gindinta awaje guda ba saota siyar, yarinyar nan bata da mutunci bazata kama kanta kamr na kulthum ba kaga dao
yarinyar nan har akayi aurenta da mahir bata san ya ake rike hannun namiji ba wayyo Allah na shiga uku..

ganin zata birkice masa marmaza ya katse sauran maganan dake ransa ya fara cewa a'a hajiya ni fa bangaya miki wann maganan danki tada wani rikici ba..inda rikcin nake so da agaban kowa zan hukunta mujaheed kafin na turasa china amma tunda banmasa haka ba kema babu ruwanki dan bada shaida akan zina fa babban abu ne tunda bankamasu ido da ido ba, kema sai kiyi musu kyaakkwan zato amma kan gaskiya abun babu kyan gani dan sai tsakar dare ma ya dawo da ita.

sake kwaroro salati tay tace kai muhammadu shine bansan haka na faruwa ba.

da muryan yaudare yace yanxu daiki kwantar da hanklinki ni na riga na yanke mana hukunci na kawo mana mafita wanda zamuyi shi acikin rufin asiri da kare martaban gidan mu dana yaran mun duka, dan yanxu in aka fito da maganan nan kinga kowa mutuncinsa zai zuba toh kenan babu amfani ba kar azo mutanen waje amiki gori ace akwai mazinata acikin gidan ki kinga an anzubda ma gidan nan mutunci

tana share hawayenta da bakin hijabi tace wallah kuwa hakane muhammadu yanzu kai meye ne shawarararka

tana fadin haka ya gyara zama wani nannauyar ajiyan zuciya ya kufce masa abazata....yace toh nide nay nazari da tunani me zurfi, naga iya abunda ya dace muyi nidake dan mu ceto mutuncin yarinyr nan da kuma gidan nan baki daya shine, tunda ibaad aure zaiyi, mujhed kuma kinga karatun bai shiga jikinsa bama tukuna bare ya samu aikin yi gashi yay nisa da ace dukkansu basa nan gidan ayaanah tafara fita da maza awaje nace mai zai hana saini in rufa mana asiri duka in aureta kawai, kinga zanma fi kulawa da tarbiyanta tunda yanxu duk watsewa zasuyi bayan auren nan, ayaana tana gabana tana gaban ku koba ba nanan agidan nan nasan dai zaku samin ido akanta kuma ke shaidace zan iya kulawa da ita sosai..amma bansani ba ke yakikaga?

dan jimmmm tay jin maganan yay mata nauyi ganin age dinsa da kuma cakwaiyr da hakan zai iya haifarwa da har zatace mishi aa sai kuma ta fara tuno maganganunsa witou thinking it tru tace "ai shikenan ma wannan shawara naka muhammadu yayi sosai
dan wallah bazan iya da abun kunya ba kaga ranar auren rayyanun d sai ahada da naku ayi duka awuce wajen, kai amma nagode nagode muhammadu Allah ya maka albarka yanxu inba kai kacika dattijo na gari ba uban waye zaiji wann magann akan ya mace snn yace zai kwasheta...
toh aure kam kmar anyi an gama

wani dan uban dadi yaji aransa yace nagode hajiya ai dama nasan ke zaki fahimceni, abu da zubda mutunci da lalacewa ai gara a katseshi da wuri sedei wani hanzari ba gudu ba hajiya wallah bansan ya zamuyi a sanar da safeera ba

cikin kyabe baki taceb"haka dai zaka daure ai hakuri zatay ataru a rufa ma juna asiri yo ayaanan ce bata san halinta ba? yarinya data taso agabn idonta ai banajin ma yakamata tay kishi da ita wnn ai kamr yarta aka kawo mata hakuri zasuyi su zauna da juna
Chapter 147 · 0% Book details