← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 161

Sashe 14

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan ya idar ne suka karaso kusa dashi suka samesa a inda yake zaunen kowannen su ya rusuna kai cikin ladabi yay gaisuwa cikin darajawa da girmamawa, bayan ya musu few question akan karatunsu ya kallesu duka sigar nasiha yace todai kunji abunda malam ya faɗa, mutuwa bata bar kowa ba, tsoho da yaro..kai ana iya haifar jariri ko minti daya baya karawa a duniya zai koma ga mahaliccinsa bare mu da Allah ya bamu dama muna raye dan mu bauta masa, cikin tuna wayar da sukayi da prof jiya yace" ynxu kune manya, kune zaku hade kan dukan yan uwanku kusani hannunku bazai ruɓe ku yanke ku yar ba. shi rayuwar duniya kamar bakonta ne, duk fushinmu da haushin mu da juna wata rana kwasam babu sallama zakuga mutuwa ya dauke wanin mu na har abada. toh dan haka duk a nitsu inaso kuma ku manyan ku daure ku karfafa zumunci a tsakaninku da yan uwanku snn ban cire kowa aciki ba

kai tsaye ya kalli ibaad yace ka dage da karatunka jiya professor ciroma yace nagaya maka cewa zai baka official call acikin group dinsa na young cardiology doctors sabida yaga practical points inka kana da enuf skills for basic medical first aid. unbehalf of you dai nace masa babu damuwa zaka shiga, toh bansan dai ra'ayinka ba. kan ibaad na kallon kasa ahnkli yace badamuwa bappa duk abunda ka yanke min ai shine daidai i will just wait for his call..cikin gyada kai mai cike da apfahari bappa yace toh masha Allah. toh kuje ciki, ni zan gaisa da makwabta kuje ku fara shirin schl kafin na shigo. kai kuma maheer ka tabbata kabi schl dinsu sultana kaji min meyene matsalarta dayasa bata gane lissafi...aladabce maheer yace toh baba
daga haka bappan ya mike ya barsu kafin nan suka taso suma suka kamo hanya izuwa gida.

tafiyar kurmaye suke sai can suna cikin tafiyar snn maheer ya tsinke silence din dacewa ohh i hate going to dat schl. ibaad dake kallon gabansa yace kabari saida muka bar gabansa snn zaka fada min? maheer yace "hmm kai bazaka gane bane innaje they will waste my time ne so why not kai kaje min, kaga dama sunfi tsoronka, da sauri ibaad yace 'no please kawai kaje din ni yanzu haka ma inada 7:40am practicals a lab kuma nagaya maka na shiga wani reading group i need to be der on time. sai dai shawara inkaje ka fara lura shin matsalar daga itace ko na duka yaran ne dan kasan sumtimes gane karatun maths depends totally in the method of the teacher..maheer yace alryt good idea. inde kuwa daga wajen malamin ne kaga dole ne anema mata lesson teacher agida...bt do u have any idea why baba yake mana magana akan zumunci? atakaice ibaad yace "i dont knw..nd i dont care to know..kawai de nasiha ce me kyau.

maheer yace hmm jikina yana bani akan kawu babba ne, can you believe dat jiya ya kirasa da daddare bayan mun gama kallon ball?

adan miskilance ibaad yace and how is dat an issure..

baki bude maheer ya kallesa yace "a sudden call from prof after 7yrs of snubbing him kace how is dat an issure? hmm duk uban abunda ke faruwa wallah bai taɓa daukar wayarsa ya kira baba ba sai dai inzai bada sako kaga ya kira uncle moh kai tsaye amma jiya kawai wai saigashi ya kira.

.."dan shiru ibaad yay snn yace ohryt maybe ure ryt, akwai dalili, amma kuma dama ai shine baison ayi zumuncin dashi, maybe ya dawo hayyacinsa kenan. cikin kyabe baki maheer yace oho, but i dont think so, naji de ance yarsa ba lafiya. bansan masa ba but anyway sha mu aidama bama fushi dashi..ibaad ya saki umm sai baice komi ba har suka bude gate din gidansun suka shiga ciki daga nan kuma kowa ya wuce dakin sa domin shiryawa..

ibaad yana shiga room dinsa ya ciro wayarsa ya kira mahaifyarsa suka dan gaisa snn ya mike ya gyara koina a dakinsa, he rake care if his room kamar ƴa mace, kominsa sai ya kal kale ya gyara tsaf ya share tass, he is a very very neat guy. within few minutes wajen yay fess kafin nan ya wuce wajen wanka within 20 min shima ya gama shirinsa cikin sky blue fitted long sleeve shirt, da wandonsa baki sai gogaggen labcoat dinsa da system dinsa daya zubasu a jakar baya.

as usual he look mr neat and breath taking dake komi ya saka ajikinsa tana masa kyau dake Allah ya bashi kyau ne me daukar ido da hankali, 6:49am ya nufi kofa yana baza ssnyar qamshin turarensa na original dior souvage mixed with creed aventus na smart collection wanda inya wuceka dole ne zakaji kamar kabishi ka lasheshi..

yana kammala daura agogonsa ya bude kofar room dinsan zaii fito kenan yaci karo da cousin dinsa sultana, she is fair and slender a shekaru ita kusan sa'a ce da inayah, da plate din abinci a hannu ta taho suna haɗe ido jikinta yadan fara rawa, cikin rike nunfashinta a mugun tsoroce tace "ina kwana yaa ibaad, .kallo daya ya mata snn yace "ke lafiya? muryanta na rawa rawa tace uhmmm dama mummy ne tace inkawo maka abincinka daki

saidai tay 2 mun yana kallonta har saida jikinta ya tsananta ɓarin sai baice mata komi ba anitse ya saka hannu ya karbi abincin baiko damu ya bude ba cikin sauri yaga zata juya yace "sultana..da sauri tace na'am. daga ido yay ya kalleta yace next time aka baki abinci ki kawomin just use d landline nd calll me zanzo na dauka dakaina..da sauri sauri tace toh yaa

..tana juya kusan cin karo da maheer tay duk basu san ma yaushe ya iso ba a mugun tsorace ta kalleshi shima tace "sorry yaa, gud morning, da kallo maheer yabita yace morning, uban mikekyi anan .

cikin nunfashi tace ai mummy ne tace na kawowa yaa ibaad breakfast dinsa nayau anan..

cikin katseta yace 'what?..nikuma ina nawa abincin..

tace ya na kan dinning ai tacema ince maka ka sauko kasa yanzun nn zamuci abincu.. yace its alryt, jeki ina zuwa..tana barin wajen ya karaso wajen da ibaad yake tsaye da plate ahnnunsa looking confuse yace dude did you tell her dat u want to eat alone??
cikin kyabe baki ibaad yace 'nop, but its fine..
maybe she have a reason
.. maheer yace wani reason? bayan baba ya sha hanata saka maka abincinka daban, we are all suppose to eat on the table..kawai kazo muje

a dan shashance ibaad yace "maheer, let it go, i am not even hungry sauri nake zan fita. cikin share sa maheer yace "kajika kuma amma ai zaka taɓa abincin koda kadan ne, ban plate din bari inga meye ne ma aka dafa mana, kafin ibaad ya hankara maheer har ya saka hannu ya kwace plate din yana budewa yabi ya fidda idonsa waje in shock ganin walakntcen dumame ne na miyan busashen kubewa daya kwana a fridge ya fara sakewa bama agidansun akai ba, wanda ta aika ne jiya aka bata daga gidan matar me gadinsu maman ummi

..atake maheer ya dago kai cikin yatsina fuska yace "what d hell is this ibaad??

ibaad yay rolling idanunsa a mugun miskile yace "tuwo, dumame." maheer yace oh fuck it..am not eating this, this shit is smelling awful..anya ma an dumasa da kyau kuwa
amma ai dazu naji ana soya irish ko ce musu kay bakaci??..ibaad ya masa wani irin kallo da alaman baison yama amsa wann maganan ahnkli cikin nemn wakansa nitsuwa yace "guy pls i need to take my leave, inada practicals karnay latti, kawai bani abincina ka kara gaba, zan kai na aje inna dawo inci. da wani irin ƙarfi maheer yace noo you cant eat dis
..baridai naje na nuna ma mummyn hala kuskure akayi kode abincin me gadin ne sultana ta dauko ta kawo maka" ibaada yace "ohh toh inme gadi zaici ainima zan iya ci kenan, just give me."cikin zare ido maheer yace "no, i wont,this isnt ur food". yana gama rufe baki sai ganan bappa zaidu ya iskesu tareda binsu da kallo yace what is going on here..da sauri ibaad yace babu komi bappa, da sauri still maheer yace baaba abincin me gadi fa aka kawo mai as breafst shine nace ko mummy tay mistake ne ta aiko nan
da mamaki bappa zaidun yace "abincin me gadi kuma? let me see it,

maheer baiyi kasa agwiwa ba ya mika masa yana satar kallon ibaad dake harararsa da gefen ido, bude abincin bappa zaidu wanda atake yaji ransa ya mugun baci ya dgo ya kallesu duka yace waye aka aiko da abincin nan?nd why did ur mother sent the food here? dama ana kawo maka abinci..kai ibaad banace maka kowa yanacin abinci a table ba"

ibaad ya sauke kai kasa ahankli yace "kafada, a mugun dake bappa zaidu yace "so, what is this nonsense then? ahnkli maheer yace baa dama sultana tace mummy ne ta aikota ta kawo masa nd she had been.. ransa a bace cikin katseshi. yace enuf, just go nd call sultana here my friend.. da sauri maheer yace yess, snn ya sauka kasa bappa ya kalli ibaad yace kai kuma ka wuce dinning table yanxun nan bana son naji wani magana, cikin ladabi ibaad ya amsa da toh snn ya sauka kasa. bappa zaidu baijira ba kawai yabiyosa kasan da plate din abincin a hannunsa, kusan lokci guda suka isa dinning da ibaad suna kkrin zama saiga ammi babban ta fito jikinta sanye da wata doguwar riga A shape ta atamfa a hujajan ta doso falon sultana nabin bayanta adan tsorace

wanu dan uban hade rai tay tana cewa uban waye yake neman sultana, toh nina aiketa gani nan sai agayamin lefi na. ina shi ibaad din dayake neman ta in dukanta ma zaiyi gani nan saiya fara dani..

tagama furta hakan kenan zata sharo kwana caraf suka hade ido da bappa zaidu wani rasss taji gabanta ya tsinke ganin irin kallon dayake mata gabaki daya sai taji ta mugun tsorata da tarin kwarjinin dake cikin kwayar idanunsa sosai...
Chapter 14 · 0% Book details