← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 161

Sashe 118

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunda su ibaad suka dawo ya dora idanunsa akanta yaji ya kasa nitsuwa gabaki daya dan bawai zallan kyaun datayn bane ya rikita shi,qamshin, kunyan, da kuma yadda take masa magana da shagwaba da kuma nitsuwa yasa with each passing minute yakejin jijiyarsa na tashi sosai, for the first time in his life yaji yana matukar shaawar wata ya mace a duniyar zuciyarsa da rayuwarsa har gangan jikinsa yafara jin yanajin sha'awar ayaanah.

waje guda suka hada musu chops din ita da kulthum, ayaana tana gefensa yanacin fatta lamp da flour bread din har yana lumsshe idonsa ji yake da sukadai ne a wajen baisan wani irin sakin layi zaiyi mata ba...

sun jima awajen maheer is unpolegstically showering kulthum da soyayya dan har wani dorata yay akan cinyarsa suna cin chop din suna hira acan gefe

tsakanin ibaad da ayaana kuwa bakajin me ma suke fada dan kasa kasa sosai yake yabon girkin nata, dadi kamar zai hallakata murmushi kawai take zuba masa tanajin kamr ruwan shauqin soyayyarsan har cikin jininta yana malala kmr zai hadiyeta, sun jima a falon kafin nan shida ayaana suka fita waje suka bawa su maheer waje...cikin motarsa ya bude mata ta shiga shima ya zago ya zauna ya kullesu da tinted aciki, dan kadan ta jingina ajikinshi suna kallon reels daga wayarsa, which is mostly abt medicals nothing fun in it but she like it this way atleast baiya kallon yan mata

tay tay ya sakar mata wayarsan tarike dan yasan damuwarta shine kawai tay masa bincike taga ko yana kan magana da zainab arifah tanayi tana basarwa amma sosai ya fahimce shagwabn tan sosai. dada narke masa take ajiki har abokinsa jamal ya kira, jin yace masa yana tare da ayaana, jamal din ya dawo da call din video suka gaisa, da mamaki taji yana bawa jamal labarin dadin abincin data masa, she was so happy acikin ranta musn yadda jamal yake cewa very soon zasu zo tay musu me dadi suma agidan ibaad din suci..

hira me dadi sukayi daga nan ya hadata da matarsa mufeeda suka gaisa cikin aminci she was just gushing akan irin kyaun ayaanah..ita direct take tambayarta yaushe xakuyi aure muxo shagali ayaana saidai ta kalleshi tay murmushi, shine kawai yaketa cewa "soon!! but she dont knw weda he is serious ko kawai yana biye musu ne.

bayan sun gama call din ne ya bude gallery din sa yanuna mata project dinsa na gidansa can United Kingdom, very sleek country classic mansion ne me aji,fully energy effecient ga water pond ga garden ga kuma kids backyard ga pools guda biyu daya a sama daya awaje snn za'a musu glass walls a katon kitchen dinsu, just 4 bedroom, daya nashi daya na matarsa, sai na yara dana baki. plan din gidan mace daya yay which make her heart beat faster dan bata san ya al'amari zai juya ba, she is desperatly hoping ace itace akayi wa wann gidan ba zainab arifah ba, even tho he is asking for her gunuine suggestion awasu abubuwan still dai tana cikin fargaba sosai. while suna nan mota daga cikin gidan ammi karama ta nemesu sama da kasa ta rasa, kawai sai ta share.. kowa saida ya taru a falon anty safeera aka yanka cake din uncle mohd aka masa abubuwa gogan naku he was just pretending to be so happy da irin romantic suprises din da anty safeera ta masa mai ban sha'awa kuma ta kashe kudi fa sosai ta masa gifts na kece raini har dasu agogo masu matukar tsada..

ibaad da ayaana na mota basu gama tattauna sauran plan din gidansan ba har saida aka kira sallahn azhar snn suka gama, lura da fargaban dayake idon ta na kokonton samun shi a matsayin miji yasa ya dinga mata dariya kasa kasa yana dan tsokanarta cewa in yatafi can ma da wuya ne ya dawo

da sanyin shagwba tace yaa yanzu dama saika tafi can kabarni anan? yadan ja cheeks dinta yace inace zaki koma can U.K din dai tare dani?but is totally ur choice madam, i cant force u inkince baki son zama dani ai shikenan..tana kallonsa kamr zatay kuka tace kai bakason zama dani kenan? cikin kyabe baki yace"who wudnt??ahnkli ya dan rankwafo fuskarta nmfashinsa na gogar nata yana mrmshi cikin lumshe ido tare da budewa da kasallaiyar murya yace 'u're beautiful, smart,..sexy...cikin jan numfashi yace "but...

...maraitaccen idon ta fixed acikin nashi ahlkli tace 'but what? yace "i dont knw if ure strong enuf to cook me as hot as d way u cook ur delicious food'..ahnkli tace "cook you??

shiru yay yana mai kure kwayar idonta da kallo yana murmushi me sanyi har saida brain inta ya fara harsasho mata meyake nufi da wani irin sacewar jiki ta rufe idanunta da duka tafukan hannunta yana murmushi ya jawota jikinshi ahankli ya rangwafo cikin kunnenta yace kin gane kenan ko?? ta dada boye fuskanta akan kirjinsa
..ahnkli ta gyada kai..yana dariya yace "good..go nd think abt that hard nd long. yana furta hakan yadaga ta ajikinshi ganin taki ta hade ido dashi yace "bakinki ya rufu ko?to kije ciki karki hanani alwala, we wll talk later, yeah?? kanta na kasa tana murmushi ahnlki tace yeah.. karamin kiss ya dora mata a hannunta daya rike snn yasaketa cikin nitsuwa ta bude motar ta nufi cikin gida da bala'in sauri..

tsabar kirjinta na bugawa batama lura da cewa babu kowa ba kawai ta nufi daki da shauqi ta wani irin sulalewa akan gadonta tanamai sauke ajiyan zuciya me karfi da kuma shauqinsa me balain yawa aciki dake mata rairayi ajiki, masifaffen qamshin turarensa daya gama mata malala a jiki hade da nannauyar kalamansa ke dirar mata acikin kunne da kwakwala yasa taji gabaki daya gabobin jikinta sun mutu murus...

wani irin shauqaqiyar juyayi take y akan gado ba acikin hayyacinta tana ji aranta kamata domin ita Allah ya halicce ibaad dan wani irin makahon sha'awshi taji yana dirar mata wanda damshinsa tuni ya fara kkrin jike mata panties, tajima akwance tana sauke ajiyan zuciya daga bisani ta cire kayan jikinta tay wanka tazo tay sallah

sai taga text dinsa akan ya fita amma baizai dawo da wuri ba ka inbe dawowa anjima kawai zasuy waya..

tana murmushi ta amsa masa, kafin ta jawo qur'ani ta cigaba da karantawa da tsakar rana dan gabaki daya bata gane kanta ba, dan daga tafara tunaninsa sai taji sha'awa me karfin gaske yana kkrin rufeta
ganin bazata iya jurar wankan tsarki ba yasa ta cigaba da karatun qur'ani har saida abun ya gushe mata aranta snn tay bacci.

uncle moh har yagaji da jiran yaga ayaana awajen birthday insa har ya cire kunya ya tambaye ammi karama
tace masa ita dai tabar ayaana tana girki ma su ibaad ne amma bata san ko ta gama ba

ransa sosai ya sosu da jin haka, wato ibaad haryau dai bazai daina shigewa hancinsa ba, sai yau yaji yana nadama dama a hannunsa ibaad din ya girma da duk wann rainin dayake masa bazai kai nan ba.

but now da dayekeji yayi karfi yay kato yana wasa da kudi yaron gani yake kamar shi sa'arsa ne.

da wasa wasa kuwa har akagama shagalin birthday ayaana na shekar bacci, sultana ta gama shagalin birthday snn taje tay hirarta awaje da ahmad ta dawo itama ta jonata suka sha bacci.

sai cahn yamma suka farka kulthum sun fita da yaa maheer dan haka a sashen ammi karaman suka cigaba da zama safiya kuma na kallonta a falon anty safeerah tana ta ciye ciyen cakes da abubuwan birthday

nan ne da sultana tafara bata labarin barin kudin da anty safeera tay sai ta tuno tace shit kice dai nikadaine banje bazday uncle ba, sultana tace ehh wallh ke da mutuminki yaa ibaad ba??? dama kuma ba ɗasawa sukeyi da uncle moh ba..
ayaanah ta kyabe baki tace "hmm,wallh ni mantawa ma nayi toh Allah ya karo masa shekaru masu albarka

...sultana tace ameen..wai ina kukaje ne da yayan? kefa yaa ibaad yana balain shagwabaki..

ayaana tay kwafa tace kai sultana bashi yaje ya dauko ni ya kawoni garin nan ba aikuwa dolensa ya kulani? suka fashe da dariya..tace "kai ayaana kamr wani zaki iya fadan ahaka agabansa aje dai a yana shagwbaki amma dai kinsan gayen nan baida dadi..in ya hade rai kamar mala'ikal mutuwa.. ke wallah ya ibaad is unbelivble ni bansan ya zasu kare da budurwansan can ba kiga dan uban wuyan dayake bata. wani cak dariyar ayaana ya katse da harara tace wa knn badai anty zainab arifah ba datake nace masa ba? Sultana ta fashe da dariya tace "Allah ya shiryeki ayaana wato kedai bazaki kyale matar nan ba ko?..

jan pillow tay kirjinta tace inhar ta kyale shi zan kyaleta..kwana biyu ma banga ta dawo ba hala karatu yay zafi

sultana tace eh amma next week kuwa zaki ga ta dawo kinsan kmr mayyace bataza sake tay missing birthday yaa ibaad ba, kinsan he is a november born ko??

ayaana tace "really? nov when? tace nov 18th. ayaanah tace whow amma ko sau daya bai taba furta min wani abun birthdaynsa ba

cikin sace ajiyan zuciya sultana tace "Dats bcos he lost his dad dat day ..nd you know what...ranar fa suna tare da babansan ya rasu, so i ques it bring back bad memories
for him..jikin ayaana atake yay sanyi tace "Allah sarki, Allah ya jikansa..i feel really sorry for him. sultana tace "yeah, lets call this lover gal yanxu haka zaki samu sunacan dakin yaa maheer a gida suna morar juna ni wallah bansan wani irin maganin mata ammi karama ta bata ba yarinya ta sake ma miji jiki ayita haƙarta bata gajiya?

dariya ayaana tay tace barta ta more abunta shima ai yanaso ne da baya so bazai nanike mata ba ni wallah abun ma tsoro yake bani...
Chapter 118 · 0% Book details