← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 161

Sashe 134

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mota guda aka turosu maza sunkai sha biyar suka tunkare su bappa zaidu

"bappa zaidu yace officers lafya naganku haka dayawa a gidana?

cike da girmamwa babbansu yace "lafiya kalau sir. nan ya ciro papern arrest warant ya mika ma bappa, yana maicewa sirr we are directed frm above to come nd arrest ur son person of Dr ibaad almansur with immidiete effect...

cikin katsesu da tashin hakali bappa zaidu yace and on what charges...arrest kuma? dis is abslutely ridicoulos!! me yayi?

nan babban cikinsu yahau ma bappa zaidu bayanin wai charges ne akan Intentional Infliction of Emotional Distress (IIED), he is also going to be held in detention for infliction of emotional trauma to zainab arifah leading to self harm..

its just a protective custody detention, some interrogations nd detntion for some hours.

wani officer yana kkrin sakama ibaad handcuf bappa zaidu ya daka mai tsawa yace heys dont u dare... barawo ne, ko kuma kisan kai yay da zaku taru masa

ibaad ya kalle bappa zaidu yace bappa karka damu i will go with them ku kuje gidan

bappa zaidu yace Dats not ur decision to make young man...

driver ya kira aka saka su ammi babba da sultana zuwa family house hanklin sultana yay bala'in tashi tun a mota take kuka ammi babba kuwa Allah Allah take su isa ta bada kanun labarai

daga nan kuma bappa zaidu bai sake an saka ibaad a motar polisawa ya daukesa dakansa suka bisu police station din, ya zauna a waje suka shiga da ibaad ciki

fadin irin tashin hanklin da family house ya shiga da ammi babba taxo ta gaya musu antafi da ibaad an kulleshi tareda bappa xaidu bazai kiyastu ba hankalin kowa saida yay mummunan tashi

abubuwan suka taru suka ma ayaana nauyi a kirji musmn ma tunda ammi babba tafara zuba wani irin karya da makirci agaban hajiya mairo..

nan ta kwashe labari a juye ta gaggaya musu cewa ai fada sukayi da zainab din jiya da yamma,kuma zainab din ta bar gidansu tanata kuka basu san me ibaad ya gaya mata dahar taje tay tunanin kashe kanta tace musu kuma bappa xaidu yaxo yagani yana daure masa gindi duk da ma sunga halin da xainab din ta shiga ciki

labarin take bayarwa tana kuka agaban hajya xaka rantse da Allah agabanta akayi komi dan babu irin karyan da batay akan ibaad ba, kuma ta kwashe komi tace lefin bappa zaidu ne dama tajima tana gaya masa ya sakalta ibaad, baya ganin leifinsa ko yay laifi baya masa fada snn yana nuna fifiko da bambamci, cikin habaici tarinka cewa ai yanayi ne dan ya burge ammi karama bata dai fito fili ta kama suna ba amma babu kalar gori da habaicin da batay ma ammi karama ba.

tun jin wann batu hajy mairo ta birkice ta fara tsine tsine tana zagin ibaad, ayaana tabar wajen ta koma daki tanata kuka dan tasan bazai taba yuwa yama xainab wani abu me muni da zaikai har haka ba, sultana ne take rarrashinta sai safiya data fice wajen jin gulma..

ammi karama batace komi ba tay shiru musm dataga kowa ne yahaura sama, uncle moh, ammi babba da su anty safeera duk magana daya suka taru suna gayawa hajiya mairo cewa laifin duka na ibaad ne kuma ya samu daurin gindi ne daga bappa zaidu .

cikinsu babu wanda yaso yay bincike ko yasan asalin meke faruwa kusan kowa ya hau dokin xuciya sai tay shiru abunta batace komi ba.

uncle moh ya kira prof yafi sau talatin amma bai daga ba maza maza yace ayi shiri kawai aje asibitin tunda bappa zaidu yana tare da ibaad a police station...

daga asibiti kuwa kusan sabida content na hard drugs ajinin zainab arifah yasaka bata farka akan lokaci ba it took her 6 good hours snn aka samu ta dawo hayyacinta she wake up very weak duk an lakaba mata IV fluids da pressure dressing a hannu

tunda asubah data farkan iyayenta kowa yaxo jikinta kowa da salonsa na nuna mata soyayya amma kuma hawaye take sam sam taki tace musu komi tun suna mata lallashi har suka aje so agefe suka fara mata fada kowa ya harzuƙa yana fadin mata asalin manufarsa akan tarayyarta da ibaad tuntunin nan saiyau suka iya cire so da gata sukahau bayyana mata asalin yadda basu kaunar ibaaad kuma suka tsane tarayyarta dashi kwata kwata..
saidai basu sanar da ita cewa har sunsan an kama ibaad din ba

their words of hatred akan tarayyarta da ibaad din'nt hurt her much sabida ta riga ta jima da lura da hakan musmn ma awajen mummynta hajiya hamida da tasan ko kadan bata kaunar dangin ubanta bare kuma ta haɗa jini da wanda take ganin kamar bai kaisu arziki ba.

duk hargaginsu da lallashinsu shiru kawai tay tana hawaye batace musu uffan ba wanda hakan ya kara daga musu hanklinsu sosai.

strickt security akasa a inda suke, wajajen 10am manyan gidan gabaki daya suka taho asibitin a motocinsu amma haka kememe aka hanasu shiga ciki..

hajiy hamida sosai ta haukace ta haura can sama da fushi da tsana tace Burin yan uwansa kenan dama su kashe masa yarsa kwalli daya, dan shima a cusa masa baqin cikin da zai kashe shi, snn idan ya mutu a dauki dukiyarsa abasu

tana masa kuka ta maimata masa wann maganan cikin bori da fushi yafi sau hamsin..

daga wajen kuwa bakaramin rikici akayi da hajiya mairo ba in kaganta ma daukawa xakay an mata mutuwa, can daga baya saida akazo aka mata wayo akace ai zainab din tana cikin wani hali ne ana kkrin dagata ba asok hayaniya kuma hukuma na ciki ana bincike shiyasa ba ason kowa ya shiga kawai suje gida.

bada son ransu ba ammi babba ta dawo da hajiya mairo uncle moh ne da anty safeera kawai suka tsaya a reception na asibitin.

ammi karama kuma daga wajen ta wuce police station duba halin da su ibaad suke ciki...

tana zuwa station dake ana matukar daraja familynsu sharply aka kaita wani waiting room ta samu bappa zaidu a zaune yana kan waya suka hade ido dan hawayen datake dannewa atake suka fara sauka katse wayar yayi har tagama karasowa gareshi tun basu gaisa ba yace haba Fatima meyasa kema kika zo nan kuma baga ni nan anan ba?

da matsanacin damuwa a kwayar idonta tace "yaa zaid Kay hakuri kawai so nake naga halin da rayyan yake ciki

bappa zaidu yace 'interrogations ne kawai babu komi ba tunda bawani laifi ya aikata musu ba neman fitina ne kawai. the highest they can do is to detain him here kuma insha Allah i wont let that happen.

cikin lumshe ido da budewa da karyayyen zuciya tace Amma meyasa rayyan zai saka kansa acikin wnn matsalar..cikin fashewa da kukan da yazo mata bazata tace kaikuma kamar baka ganin lefinsa. yanxu duk cikin gidan kowa yana fushi dashi, hajiya ta dau abun da zafi dan Allah inde rayyan ya aikata wani abu na cutarwa akan zainab kawai ana gaya masa gaskiya ni wallah banason hakan yaje ya jawo masa karin baqin jini acikin gidan nan dan baida kowa a duniya inbasu ba.

cikin sassauto da muryansa kasa yace haba fatima yau kece da kanki kike furta min wann maganan? i tot kinfi kowa sanin cewa ibaad kamar dan cikina na daukesa meyasa kike tunanin inhar yay wani abi ba daidai ba zan zuba masa ido in kyaleshi...in dis case he is just a victim of circumstances tsaya masa yakamata muyi bamu hau dora masa laifi ba...ita hajiyar tasan asalin meyafaru ne??

ammi tana share hawayenta tace ni bansani ba amma ai maman sultana ce tazo ta gaya mana wai fada sukayi da zainab din jiya shine ya mata wani abu hartaje tay tunanin kashe kanta..kuma tace tun jiya kay shiru baka masa fada ba duk dama agabanka akayi komi

ahnkli yace fatima
ive personally talked with zainab jiya, nazo kam na sameta tana kuka nd she told me they had a fight..da naje na tambaye ibaad kuma yace min tazo tace masa ne akan suyi aure next week, snn ta dau dollar cheque ta bashi claiming wai zatay sponsoring auren...

i scolded him sabida tace min yagaya mata magana dabai mata dadi ba, but dan yaqi karban wnn qudurintan kuma sai nahau masa fada akan me?an taba siyan soyayya da kudi ne ko ana dole ne?..kuma kekanki kinsan da wuyane in iyayentan ma suna sane da wann abun, wallah inda ya biye mata wani matsala na daban zata jefashi aciki...karshe suce yay manipulating yarsu ya sace musu kudi, ko su masa sharri cewa shi yy influencing maganan aure akan yarsu..na lura kamar kaf kuna yin abune kamar bakusan waye ubanta ba. he will protct his child bazai taba karban laifin yarsa, so why i cant protect mine, badan ganin darajar su hajiya ba da nima fa ina da dama in shigar dakara akansu ai ba a relshp na dole, sun takura ma yaron nan tunda jimawa ohh wato mune bamu iya kaiwa kara ba ko? is not fair mana haba fatima...nayi ma yara na alkawari bazan musu auren dole ba saidai a bisa qaddara kuma kema kinsani, i cant force ibaad ya aure wacce bayaso gaskiya...so wnn kananan maganan raihanatu da hajia kawai kibarsa dukn su basu san asalin meke faruwa ba...kema kiy hkuri ki kwantar da hanklinki babu abinda zai same ibaad in sha Allah..

shiru tay kanta na kallon kasa har ya gama maganan kafin can ta share hawayenta ta dago kai cikin sauke ajiyan zuciya tace "toh shikenan..inde abunda ya faru kenan da sauki
dan wallah hanklina ya bala'in tashi da irin magngnu da ake kanyi akansa acikin gida.

yace "karki damu in few hours zamuje gidan in sha Allah babu komi sai khairan..

daga haka suka zauna awajen har sai kusan 12:30am to 1pm ma rana kafin suka sake ibaad daga interogation room ya fito ya samesu

bappa zaidu da ammi karama suka hau tambayarsa me akace masa bai boye musu komi ba ya gaya musu

after a while bayan sunyi maganan sai hukuma sukazo sukace zasu rikeshi detention sai jikin zainab yay improving out of danger zuwa yamma azo a daukesa
Chapter 134 · 0% Book details