← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 161

Sashe 11

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tun kan ayaanah ta dago kai gabaki daya sai sukaga idanun matasa da dumbin mata dake kofar gidan sarkin kasuwa sun dawo da idanunsu kan inayahn atake da wani irin mummunan kallon zargi....

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 👇🏻

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[24/10, 19:47] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️6️⃣
Da wani irin ƙarfi zuciyar ayaanah ya buga bisaga kallon reaction na zargi dake cikin kwayar idon mutanen da suke zubo musu ido sai taji ta mugun razana da yanayin inayan jikin ya dau rawa itakanta batasan sadda ta zube kasa tariko kafadun addan nata cikin ruɗewa ba...

"Subhanallah… lafiyá de kuwa adda? Méyé sàmèki haka..Mei yé sàmèki a cikin?”

muryanta maicike da tsoro da dumbin rauni yafito da rawa rawa ayayinda harshen buzancin nasu ya dada bayyana cikin kwababben hausarta ta abazata...

wani irin zafi inayah taji agefen acikinta dake tahowa tun daga wajen cibiyatta kamar ana zungurosa da icce irindai kamar ciwon ulcer ko irin ciwon cikin nan da ba asan asalinsa ba.

ganin idon mutane akansu yafara yawa yasaka inayahn tay ta maza tabi ta shanye dumbin zafin datakeji acikinta ta dagokai tana dan ƙoƙarin yin murmushi saidai ji take kamar bazata iya miƙewa tsaye ba..

kallonta ayanaah ta dingayi ganin wani irin sudaɗɗen hucin zufa yadan fansama asaman fuskar addanta me bayyana halin da take ciki na ciwo da tsananin zafi, tsamm inayah tay ganin irin kallon razana da anayahn take mata cikin dauriya tay saurin dauke idonta kasa ahnkli ta danne komi tadauki jakar tadan miƙe tsaye ahankli ahnkli dakyar tana cewa "hai kekam, à handi mboni baki da dauriya sham anyi babban matsoraciya ganin ayaanahn tanata kallonta har yanxu batace komi ba yasa ta kara mikewa
"karki damu Lafiyata lau… wataƙila yunwa ce ko saboda nagaji...

Abunka da yaranta wani irin nannauyar ajiyan zuciya ayanahn ta saki feeling a bit relieved ahnkli cikin sanyin murya tace tohm shikena,sannu da jin yunwa adda am. toh muje ciki ni zanje madafi na kawo mana abinci yau bake ba..ke aizaki huta yau ko??

a daddafe kuma a ɓoye inayah tay still a tsaye da hannunta ɗaya data zamarshi ta cikin hijabi tadan riƙe gefen cikin nata dake mata ciwon sosai sai murmushi kawai takey ma yar uwarta ayanah badon ciwon cikin ya tsaya mata ba sai danta dada kwantar mata da hankli.

not minding ydda ake satar kallonsu da yanayin gulma ahaka har suka saka kai suka karasa cikin gidan nasu atare. saidai dake yamma ne basu tarar da kowa agidan ba, lkcin duk dai ana kasuwa da alama dai izuwa nan bada wani jimawa kowa zaidawo dan ankusa kirar sallan magriba ynxu..

duk da rashin girma da wayon ayanaah yau sosai take saka ido akan yanayin addarta inayah da taga kamar ya dan canza, suna shiga harabar gidan tanema mata wajen zama akan dakalin kofar daki snn ta amshe jakunansu dukka ta kai daki ta ajeshi, aguje tadawo ta same ta tadan jingina da bango tana dan nishi har yanzu da hijabi ajikinta ta damke cikin nata taciki, da gudu gudu sauri sauri ayanah ta je wajen da ake aje musu kwanon abinci ta dauko musu tuwon dawa da jar miyan kubewa har da ruwan sha tazo ta ajeshi agaban addanta duk hanklinta ya tashi ta dauka kawai tsabar yunwace ke neman ya naƙasa mata addanta inayah..

ita kuwa inayah gashi dai ciwon cikin na mata kamar na yunwa yunwa amma koda ayaananh ta zubo musu abincin sai taji abincin kamar yana daga mata zuciya tana jin ɓacin rai sai tanaji kamar ta washe abincin aranta, saidai dake batason ta dagawa yar uwarta hankli yasaka ta daure
taci abincin kadan baifi loma biyu ba snn ta sha ruwa sai tace mata zataje ciki ta cire uniform ta dawo tunda ta taɓa abincin kadan. tafiya ahnkli ahnkli tayi har ta shiga dakin ta cire kayanta ta saka riga da zani jin ciwon cikin gabaki daya yane neman ya hanata tsayuwa da kyau, kawai sai ta nemi waje ta kwanta atake kuwa wani bacci me nauyi ya kwasheta abazata

wanda kusan abun al'ajabi ne kaga inayah tana bacci gabanin magriba sabida bata kaunar abunda zai saka tay lattin sallah a rayuwarta dan in batay sallahnta akan lokaci ba har kuka takeyi.. jim kadan koda su taawure suka dawo gidan gabanin magrin suka tarar da Ayaanah ita daya a haraba ta saka tuwon agabanta ta tsaya cak bata cigaba da ci ba, ta kuma rabza uban tagumi hawaye sun ciko acikin kwayar idanunta sosai abun yadaga musu hankli.

hajya mairo ce ta fara rufeta da tambaya toh ita bata gane komi ba, sai tahau gaya musu iya abunda ya faru, cewa takewa addanta tana jin yunwa amma taqi cin abinci dayawa kuma gashi nan bata baccin yamma sai yau taga tanayi, yadda ayanah ta daga musu hankli babu shiri taawure ta shiga dakin tahau tattaɓa jikin inayah ta na duddubata sai kuma taganta kalau, kaidai dakyar suka wanye maganan aka bari akan cewa ko yunwa ne ya haɗu mata da gajiya. hajy mai tuwo har da cewa kar asaka inayan aikin gida gobe da sassafe abarta tana dan samun isasshen bacci...

Bayan awanni biyu ana daf da ishai snn inayah ta farka lkcin zafin ciwon cikin nata yaƙara matsawa izuwa gefen dama kusa da kasan cikinta. but the pain is bit bearable, duk sai ta farka a ruɗe, ga kuma anxietyn rashin yin sallah akan lokaci kawai saita daure ta waske ta miƙe garau ta yi sallolinta har ta dan saki jiki ta zage ta koyawa ma anayah karatun sukayi basic _phytogoras theorem_ dan kawai hanklinsu taawure ya kwanta sosai.

washe gari basu barta tay aiki mai yawa ba duk dama ta nace saida tay yar shara da wanke wanke snn suka ci abinci nan ma sama sama taci snn suka wuce makaranta

yau suke cike wata daya da sati biyu a tudu, ana saura sati guda kenan ayi ma inayan saukar qur'ani, ga kuma tests na boko shima sun farashi dan anata tsammanin exams dinsu na zuwa ajin gaba yazoshi akan lokaci

sosai yaran suka kara zage damtse wajen karatu, saidai ata fannin inayah kmr kusan kominta ne takejin yana canzawa acikin jikinta, tun data fara ciwon ciki sai taji takasa gane ma jikinta gabaki daya amma dake tanada taurin zuciya sai ta matse komiii tana kaucewa duk wani abunda zai jawota baya a karatu dan batason tay wasting wann dumbin Risks da effort da kuma ubam kudaden da mahaifiyasu take zubawa akan batun ilimin datake basu.

kasancewarta ƴar fari, al'adar kunya da dumbin kawaici dake tsakanin uwa da ƴar fari bai ɓari sun shaƙu sosai da taawure ba, saidai fiye da kowa a duniya inayah ce take mugun mugun tausayawa ma mahaifyarta aranta, duba da tsauraran dokoki na al'ada da sukebi a kauyensu, da kuma irin jahilci, taurin kai da tsaurin ra'ayin irinna mahaifin su malam juma.

tasan bakaramin jarumta da soyayya me yawa taawure take musu aranta ba musmn data iya daukar wann babban Risk na rintse ido akan batun al'ada tare da saɓawa ra'ayin mijinta nazama acikin jahilci har tay burus tasakasu a makaranta a ɓoye donta ilimantar dasu addininsu da zamani duk dama abune wanda tasan zai iya ƙarar mata danata rayuwar, zai jawo mata mutuwar aurenta da juma, da kuma tsangwamar mutane duk sanda aka kamasu suna aikatawa.

shiyasa koda wann ciwon ciki ya fara mata taki sam tana nunawa a fili, babban burinta shine taga ta karfafawa taawure gwiwa, sun zamo silar farincikinta ita da yar uwarta ayanah, duniya da lahira. dan taawure jajirtacciyar uwace data musu dumbin sadaukarwan da bakowacce uwa bace zata iyashi.

bayan kwana biyu rayuwarsu ya cigaba ahaka, alamomin ciwo sunata zuwa ma inayah suna tafiya, wani lokaci ta ji sauƙi, wani lokaci zafin cikin nata sai ya dawo, musamman bayan cin abinci ko wani aikin wahala. wata rana koda ayaanah tayi kmr ta ganota sai ta ce mata gajiya ko ulcer ne.

satin sauƙar qur'ani na zagowa aka qaddamar, wanda kusan babban hidima hjy mairo me tuwo tay domin jikarta inayah

nan akayi mata gagarumin murna na zamowa gwarzuwan karatun qur'ani na gabaki daya yankin tudu, anyi abinci hilimi guda akay sadaka aka ciyar da almajirai sosai, kai dai tamkar bikin auren inayah haka hajy mairo ta daukaka abun har anko na kaya saida tay musu shadda me kyau. ayaanah duk tafi murna da cigaban da addanta ta samu na zamowa gwarzuwa kuma mahaddaciyar littafi me tsarki, ranar Taawure bakaramin dadi tare da alfahari da yarta inaya tay ba.
basu taɓa magana cikin nuna soyayya ta uwa da ƴa me tsayi ba ma sai aranar. bayan hidiman ne ciwon cikin ya fara taɓa inayah acikin dare sosai, wani bin da dadderen zata ji ciwon ciki da ba ta taɓa jin irinsa ba.

Cikin nata kamar ana murɗa shi da icce mai kaifi, haka zata kasa bacci tayita juyi tana huci, Ayanah takan ji tsoron duk abunda ke faruwa da yar uwarta inayah da kuma mugun tausayinta amma hakanan inayan take hanata gayawa kowa halin da suke ciki dake kuma suna farkawa da safe sai taganta garau har suje makaranta.

tunda aka ma inayah sauƙa sai ta dan bude karamin islamiyatta na dare, bayan isha sai ta jawo ayaanah zuwa zauren gidan ko gindin bishiya inda take koyawa sauran yaran anguwar wanda iyayensu basuda halin sakasu a makarnta karatun qur'ani dana bokon sama sama ayaanah tana tayata.

hajy mairo mai tuwo ce ta dada daure mata gindi, dan ita macece me kaunar taga yaro karami mai dumbin kwazo tare da son kawo babban cigaba musmn ma ga dumbin al'umma, riƙe ƴayan taawure kusan abun alfahari ne agareta duk dama riketa kawai tay basu haɗa jini ba, duk safiyar Allah sai sun sakama inayah Albarka a rayuwrta.
Chapter 11 · 0% Book details