← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 161

Sashe 22

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zainab arifa ta jima a tsaye anan kafin can ta koma ciki tana jin wani irin sanyi a ranta dan baitaɓa tsayawa tayi magana me tsayi da shi kamar nayau ba, da wani dan uban murna ta koma gida ta rungume babanta tana masa godiya

fannin ibaad kuwa tun be bar titin anguwar ba abubuwan da yafaru agidan ya dinga dawo masa akai sai yanaji kamar zucyarsa na mugun tafarfasa waima ahakama bappa zaidu ya bashi key dib babban mota da kudin sayan sabbin kaya kenan da baisan wani irin mugun cin fuska za'a masa ba, can dai wayarsa yafara ruri ganin sunan maheer ne akan screen babu bata lkci ya jawo ya dauka ya duba sakon dake kai daga nan bai bata lkci ba yakara ma motar wuta tareda shan kwana yanufi anguwan abokinsu abdl gaffar, anan ya samesu dede sunfito gate suna tsaye suna jiransa, sama sama suka gaisa tsakaninsu maheer yabude motar ya shiga suka kama hanyar gida..

tunda suka hau titi ibaad wasnt looking fine at all kawai tuki yakeyi duk kalaman cin fuskar da akama uwarsa tafi masa zafi, wani irin nadama yakeji aransa dan daya san dukan zainab arifah dayay ranar zai iya jawowa har azagi mahaifyarsa comfortbly agabansa ba dabai fara ba

maheer nata shan mamaki ganin yay shiru baice masa uffan akan zuwansa gidan kawu babba ba har suka isa gida kuma baice masa uffan ba.

yana gama parking ya bawa maheer din keys na motar snn yakai kayansa daki baijima ba ya fito agurguje sukayi alwala awaje atare, as usual shiyaja su sallan magrib da ishai a masallincsu na kofar gida, har yanxu kuma baice ma kowa komi akan ziyarar da yakai gidan prof ba suma kuma basu tambyesa ba sabida yanayin fuskarsa.

bayan sun idar da sallanne yaje ya gaya ma bappa zaidu akan zasuje can family house shida maheer wajen maman sa dan tun safe tace tana son ganinsa.. kai kawai bappa zaidu ya gyada musu, kowa jikinsa na bashi wani abu, har suka kama hanya suna hirar ball sama sama har suka kai kwanan anguwar rijiyn zaki maheer baiwani gane kansa ba...
#surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 👇🏻

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[29/10, 19:23] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️1️⃣0️⃣
Wajajen karfe takwas na dare saura suka shararo kwana cikin anguwar rijiyar zaki, dakema tsohon famly house din nasu na al-mansur babban gida ne me tashen daraja sai yasaka layinsu ya shiga can can ciki inda kwata kwata babu yawan hayaniyar jama'a kebetaccen layi ne me tsafta gidan nasu yake kusan shine babban gida na farko,

Ahnkli maheer yake tukosu yana jan tsaki sabida buga musu bayan mota da wani dan adaidaita yayi shide ibaad baice komi ba har suka iso kofar gidan nasu yay horn a bakin gate mai gadinsu yazo agurguje ya buɗe snn ya shigo da su ciki batare da bata lokaci ba.

Babban compound ne sosai dake dauke da gungimemen baqin gate da bishiyoyin kwaiba da kwakwa da umbrella guda hur hudu masu daukar hankali a kowani kusurwa, kai kana ganin tsakar gidan kasan wadata da kwanciyar hankli ta zauna kusan dai babu abunda suka rasa na arziki sede a idanun prof da matarsa ne kawai suke kallonsu tamkar almajirai..

makeken tsakar gidan nasu na dauke da manyan sassa har uku masu design iri daya ko wani side akwai coridors da matakala mai dan tsayi tsakanin sa da wani sashen, sashin farko wanda shi zaka faracin karo dashi bayan shigowar ka cikin gidan shine yaksance babban morden bungalow yana da girma sosai ananne main family house falo yake me girma mei cin setin kujeru hudu da katon dinning area, sai wani dan karamin falona privacy asama, anty safeera da uncle moh da ƴayansu biyu sune suke zama ata nan fannin don sashin ya fi kowanne girma sosai, yana da extra rooms nd big luxury falo dake tsakanin sashen da sashe, sai yar medium self contain da aka tanadashi wa hajy mairo mai tuwo intazo musu hutu.

dayan Sashen da baida girma sosai su ibaad suka wuce kai tsaye dan anan ne mahfiyrsa take zama wanda na musamn bappa zaidu yasa aka sake gyara yanayin building dintan tun alokacin da mahaifin ibaad ya rasu badon komi ba saidan dan ammi karama taraini yaranta acikin nitsuwa da kwancyr hankali, hatta ibaad da baiya zama da ita sai wkends yana da nashi bed room din da closet dinsa inda ke lode da kayan sawarsa kala kala masu tsada da kyau. In ka shiga Bangaren nasa zaka san indeed shi dan gatane awajen mahaifiyarsan inyazo gida yakan xabi xama ananne sabida anan ne yafi sakewa.

karasowa sukayi cikin karamin parlournta iya muryoyinsu kawai tajiyo tamiqe zaune kadan jin motsinsu a kusa tay murmushi cikin furta kushigo daga ciki

Gyara zamanta tayi akan dark red colour daddumarta tana dada gyara zamn wata white cotton lafaya lace ajin farko data sayeshi from mum ramlat's clothing collection,tayi masa dinkin riga da zani irin maiduguri style innan dayagaji da haduwa wanda duk dama dare ne amma Wani dan uban qamshin turaren wutane na dutches da sandal wood original already yagama cikke sashenta da azaban qamshinsa traditional incence burners dake ci da wuta agefe da gefen kowani kusurwa na famar kara masa kaimi..

sanye take da farin gilashi à idonta na karatu, Gabanta kuma nadauke da hadadden royal flask sabo daga uwargida kitchen utensils collections shima badai dauke ido da rike zafi ba, tashakeshi tam da herbal tea, sai tazuba Kadan adan karamin transparent kofi na shayi tanadan zuƙa ahankli,a shekaru dai kwata kwata ammi karama bazata wuce 40yrs ba dan kuwa da danyar shekarunta mahaifin ibaad din ya aurota tun tana yar 18yrs a duniya, bayan aurenne ta haifa ibaad while she was just 23 Sai kuma tay ta samun ɓari Allah bai kara bata haihuwa sai da ibaad yacika 7yrs a duniya tana daf kuwa da haifar yar autarta safiya mijintan kuma ya rasu..

kwance tashe gashi wai har ibaad dinta yadoshi 18yrs kuma har yafara karatun dream course dinsa shida babansa wato medicine, wanda yasaka take dada mika dumbin godiyar ta ma Allah da kuma bappa zaidu dayayi tsayin daka akan rayuwarta dana y'ay'anta wajen ganin sun cika burikansu na rayuwa tun mutuwr ubansu har gobe.

da fara'a ta tarbe su maheer ne yafara neman waje akasar capert ata gefen hagunta ya xauna yana murmushi me sanyi shikuma ibaad din ya karaso tagaban ta tare da zama dab da ita kusan atare suka hau gaisheta tanamai saka musu albarka cikin fara'a da dattako.

hirar karatu suka fara da maheer kadan dake sun saba da juna sosai akabar ibaad din yana kalle kalle, can cikin katsesu yace Ammi yana ganki ke kadai anan, safiya fa? badai taje tazuba kananan idanunta tana kallon indian series ba. dan murmushi ammi karama ta yi tace.."a'a..tasan ai zaka zo, so i am sure tana can dakinta tana fmr duba karatu...tun kan ya fara mita tay saurin maida hanklinta kan maheer tana cewa babban mutum tashi ka zauna kan kujera toh bare naje na kawo muku abin taɓawa, kan maheer a kasa yana dan murmushi ya amsa da toh dan bakaramin kaunar tsaftaccen qamshi da taste din girkinta yake yi aransa ba, shi hasalima abunda yafiye sakawa yake mutuwar son babansa ya aurota kenan, tana da tsafta, gayu, ga kamala, da nutsuwa snn yafiso ace sun zama tamkar uwa daya uba daya da su ibaad acan gidansu,bai fiye nuna wannan raayin nasa ma kowa bane sabida baison mahaifiyarsa ammi babba taga kamar yaci amanarta har tay fushi da shi.

ammi karama tana wucewa kitchen bada jimawa ba sai ga 10yr old safiya ta fito kanta babu dan kwali tanata callara wakar tashar style life its a beautiful world sabida batay tsammanin har sun iso ba. wani yaye labulen tayi caraf kuwa suka hade ido da ibaad da wani irin sauri ta sunkuyur da kanta kasa jikinta ya fara rawa ahnkli ta mannu da bango tace "i ii na wuni yaa ibaad? sama da kasa ya kalleta da daurarn fuska muryansa a mugun shake yace 'sallamarki kenan?

wani zirr hawaye ya ciko mata a ido cikin matsanancin jin tsoronsa ta girgiza kai tace" a'a, sai kuma ta fashe da kuka ahnkli, mikewa yay kamar zai falla mata mari, tay sauri taje taɓuya ajikin maheer da yay saurin tarota jikinshi dan bakaramin tsoron ibaad takeji ba, wani uban tsawa ya daka mata .."kee, uban me aka miki da kike kuka anan, ina wasa dake ko? dada shigewaa jikin maheer tay sosai muryanta na rawa tana cewa kayi hakur yaa aini bansan kazo bane, cikin kara daka mata tsawa yace au sai nazo gidan nan kenan kike abu kamar mutum ko,? toh maza kiwuce kije kisaka dankwali akanki, snn ki dawo nan..ina dai saikinji zanzo ne kike karatu, seee, i am giving u 3 scnds to grab all ur books and come back here yau saina ci ubanki...

da wani irin mugun tsorata ta saki jikin maheer din taballa da gudu kamar zata fadi kasa ta koma ciki tana kuka sosai, maheer dai kallonsa yake yasan dai wann bacin ran bana lfiya ba dan jikinsa nata bashi cewa lallai da akwai abunda ya bata ma ibaad ransa yau sosai,
Chapter 22 · 0% Book details