← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 161

Sashe 59

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

akofar gidan suka parker jeep dinsu snn suka shigo zauren gidan suka zauna akan tabarma after like 30 more minutes suna zaune wata babbar mace data toshe fuskarta da face mask ta fito ta wuce snn akamusu iso suma suka shigo ciki

shu'umin dattijo futuk ne tsiriri da farin gemu ke zaune akan kujerarsa ga kayan tsafi kala kala barbaje acikin dakin.

suna shigowa ya fara hangame baki yana kallon hajy ramatu dake mutumiyarsa ce sosai ya saba kwanciya da ita, da wani irin rangwadi hjy ramatun ta rusuna gabansa tana rausaya jiki cikin kashe masa murya tace"..malam nawa nina Allah yaza zamaninka malam ranka shi dade ina miko gaisuwata me dadi musmn ga kayan aikin ka masu dadi.

wani shuumin murmushi yay yace "hajy ramatu kenan gidan dadi, toh dani da kayan aikina masu dadi duk muna amsa gaisuwa...ku samu waje ku zauna inji meke tafe daku?

tana murmushi ta miƙe daga rusunan suna zama ammi babba ta hade rai daga baya bayan kawartan tace "malam ina wuni "wani irin kallo yamata snn yace "lafiya hajya...snn ya juyo da kallonsa kan hajy ramatu yace toh ina sauraranku meke tafe daki yau kuma?

...murmushi tay tace malam akan dai maganar mijinta ne,
kwana biyun nan gabaki daya abubuwa sun rikice mata harma ya koreta agidansa, snn munji labari soyayyarsa yake kwasa da wancan matar, harma syyn nasu ya dawo kamar sabuwa. shine mukace bari muzo muji kome ke faruwa.

cikin gamsuwa da bayanintan ya gyada kansa baice komi ba ya jawo wani katon tukunya ya kunna wuta akai hayakin na fara tasowa yafara sumbatu yana maganganu da hayaqin kamar wanda yake magana da asalin mutum da wani irin yare..

yana gama maganan wutar ya kashe kansa, nan ya tuntsire da wata mahaukaciyar dariya ya juyo ya kallesu duka yace "Asirin hana yuwar aure yana nan daram bai karye ba..saidai adduar da sukeyi da maganin kariya da suke karba shine yake saka asirin yake yin sanyi amma badon ya karye ba..kunyi daidai da kuka zo, idan da ba haka ba wata rana zakuji cewa sun sami wani lakani da zai warware musu sihirin.

cikin jin sanyin jin ance asirn bai karye ba ammi babba tace "toh malam dan Allah yanzu ya za'ayi ka kara zafafa abun nan a raba su,ya zamana baya son ganinta itama bata son ganinsa, su tsane juna..dan wallh ina cikin tashin hankli malam, matar nan ta kwace min mijinaz snn tazo ta kwace min yarana..tunda nabar gidansa yau kwana shida kenan amma ko sau daya yarana basu nemi ni awaya ba suna can atare da ita..nide ko ma miye ne kayi dan matar nan tariga tagama da rayuwar aure na.

shuumar dariya yay yace ki kwantar da hanklinki hajiyabai aure kam fa bazai taba yuwa ba..aljanun mu sunce babu aure a tsakaninsu wann shirmen da sukeyi duk zasuzo su dena kece matarsa na qaddara ,gidanki ne ke kadai zancen kshiya babushi ma a qaddararki.

wani dan uban murmushin bazata ammi babba tay tare da sakin wata katuwar ajiyan zuciya hummm masha Allah malam, ai iren iren maganan da nakeson ji kenan toh inde har hakane kuwa godiya nake Allah yakara maka basira nide yanxu ataimaka min dai na koma gidan mijina tunda kace bani da wata matsala da su anan gaba

cikin gyada kai yace 'angama' ke dai kije ki kwantar da hanklinki
aure fa babu shi aljanu sunce mana kece matar mutuwarsa..

wani irin murmushi ta karayi tanajin wani irin matsanamcin dadi na ratsata mata jikinta irin wanda ta jima bataji shi ba...

wani kullin magani ya ciro ya bata yace mata taje dashi ta jika a gora duk sanda zataje rokonsan ta kurkure bakinta da ruwan maganin babu makawa zai dawo da ita..

karban maganin tay tace masa nawa ne, yace aa kyauta ya bata

rusuna kai tayi tana masa godiya, nan hajya ramatu tace mata taje kawai ta jirata a mota bari itama tama bokan special godiya ata ciki.

bafulatin yana lumewa yar cikin dakinsa hajy ramatu ta sabi jiki ta bishi ciki suka rufe kofa

bata damu da salon karuwancin kawartan ba cikin kyabe baki ta fita can waje tana murmushi danyau bakaramin kwanciya hnklinta yay da taji batun bokan nan ba...

daga cikin dakin bokan kusan minti talatin yay yanakan durjan hajy ramatu sai can bayan har kura ya lafa snn yake gaya mata asalin maganan asirirrince...

cikin girgiza kai yace....hajiya 'ina tausayin kawarki dan gaba fa bazai mata kyau ba, da ace itama zata yi wayo irin naki tazo tana jiyar dani dadi nida aljanu na muna gamsuwa da romonta aida kuwa taga aiki da cikawa

hajy ramatu tace bangane ba malam dama akwai wata matsala ne?amma ai dazu naji kace mata komi lafiya, kuma aure bazai yu ba kode raihantu zata mutu ne???

yace a'a..bazata mutu ba, amma fa abunda zai faru agaba zata gwammaci da mutuwar ma tayi, dan kuwa wayancn mutanen nata sun rike Allah inkin lura shiyasa banfiye son mata aiki

,.magungunan dana baku na hana yuwar aurencan badan da baqaqen ifiritan aljani mukayishi ba da tuni sun kwanceshi. kuma ita waccan din datake gudun itace ma asalin matarsa ta qaddara, lokacin aurensu ne dai bazaizo musu da wuri ba, amma kuma fa manyan aljanunmu da suka shafa sama shekaru dubu daya suna harka sunce min zasuyi auren harma da rabon yan biyu atsakaninsu anan gaba.

a firgit hajy ramatu tamike tsaye cikin doka kirji tace "nashiga uku, haba malam...kace min wasa kakeyi dan Allah?...

jin yay mata shiru yana karkada kai tace...innalillah wa inna ilaihi rajiun lallai kuwa akwai matsala yanzu dan Allah ko kashe daya acikinsu bazakayi ba??...wnn abun inhar yazo ya faru wallah wallah raihanatu mutuwa zatayi

cikin kyabe baki yace.."ai kafin ta kashe wani acikinsu sai inta shirya mutuwar itama, ai suma ba azaune suke ba, mijinta yana can yana neman makansa kariya itama matar tana neman makanta kariya akwai kaikayi koma kan masheqiya ajikinsu, inhar dagaske kinason kawarki toh maza kijje kibata shawarar kartaje wajen wani boka da maganan kisa dan wallh kanta zai dawo, snn kiy duk abunda zakiyi ki rudeta ta cikagaba da yarda da cewa auren nan bazaizo yu ba. inba haka ba sakamakon da zata tarar fa mutuwa ne shima bamai dadi ba..

jikin hajiya ramatu a mugun sanyaye ta koma ta zauna tay jimmm....can kuma tace toh bakomi malam inaga mafita daya kenan.. in sha Allah bazan bari tasan asalin gaskiyar ba, sn inka amince zanyi kkri naga na shawo maka kanta inta yarda zatana jiyar da kai dadi saika taimaka arage mata wani abun ..niko haihuwar yan biyu acire shi acikin qaddararsu, fisabillah malam da wanne raihanatu zataji???

karamin dariya yay yace "babu komi kuje kawai...aiwnn magani dana bata zaisaka mijin ya maidata zuwa gobe. karku damu inyaso duk abunda kukeciki zanji daga wajen aljanu

godiya ta masa snn ta tashi ta tattare kayanta data zubar akasa ta saka ajikinta babu kunya ta fito ta same ammi babba acikin mota, wanda har suka iso cikin garin kano masifa kawai suke ma juna akan zina da bokan nan datakeyi anyhow batare da jin wani remorse ba..

duk wani salon wayo da iya magana hajiya ramatu tabi dan ta ganar da ita irin dadi da karfin buran bokan nan amma haka ammi babba takijinta sam tace na mijinta zaidu batagama iyawa da dadinsa bare na boka

hardacewa kazanta bokan yake bata kuma har ta mutu bazata iya bude masa gindinta yaci ba.. haka suka sha musunsu har hjy ramatu tay give up, ta zuba mata idan while aranta kawai tausayin futuren raihanatun takeji bana kadan ba.

dukkansu sunsan bazasu taba iya zaman hada miji da fatima ba sabida sosaine tayi musu nisa wajen iya gayu, gata da kyau,da halaye me saurin shiga zuciyar namiji sabida ta iya girki ga tsafta ga sanyin tarbiya da iya magana.

wajajen 2pm suka iso gidan jaju ramatu, anan sukay wanka taci abinci, ko hutawa batay tay maza ta nemi gora ta zuba maganin aciki ta saka a leda tace zata wuce offishin bappa zaidu kawai bataci na xama ba.

hajy ramatu batace mata komi ba har sukay sallama ta wuce wanda tundaga gate din office dinsan akace mata ai ya fita da wasu muhimman bakinsa tun safe basu dawo ba..

da haushin haka tajuyo da Allah yaso ta ma ta amshi kudin abun hawa isashshe awajen haj ramatu, kai tsaye university ta nufa, tajeta har Department of law cikin cin sa'a kuwa yau maheer basugama lectures ba baifi 10min ne atashesu bama.

zama tay har saida aka tashe sun yana fitowa kafin ya daga wayarsa yakira ibaad yazo ya daukesa kawai sai yaji muryanta abayansa tana cewa maheer maheer kai maheer

Da dumbin mamaki ya juyo yana kallonta itama tana kallonsa ganinsa yanayinsa kamar ba abunda ke damunsa aranta tadinajin kamar ta dura masa ashar mai zafi ko ta tsine masa, musmn najin zafin yadda ya debi kashinta ya watsar sai sam bataga alaman kmr mheer yana da imani akanta ba

budan bakinsa kuwa babu gaisuwa yace "mummy meyakawo ki nan?? mugun hade rai tay amasife tace "meyakawo ni fa kace? hmm aidole ka tuhume ni maheer, tunda har kayi wata sabuwar uwar dayasa ni dana tsuguna na haifeka baka kason ganina a kusa dakai..kazubar dani a kwandon shara sabida fatima ko?...toh ni ai banida zuciya, duk yadda ka tsaneni ni uwarka ce babu wace macen da ta isa ta cire sonka araina, zuwa nay dama na duba lafiyarka amma tunda bakason ganina shkenan, 'na lura kanacikin koshin lafya maheer,. sai anjima...bari nakama gaba na kafin kay fushi ka zageni ko ka kadeni da mota marar hankali kawai.

rai amugun bace ta juya zata bar wajen da sauri ya jawo hannunta ta dawo baya cikin sauke murya yace "haba haba mummy nide ban tsaneki ba,
kuma ban mance ki ba infact kullum ma ina miki addua.....

cikin katsesa da haushi tace kana addua dan Allah ya raba ubanku dani ya kawo muku fatima gidansa ko?
Chapter 59 · 0% Book details