← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 161

Sashe 32

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

acikin sauri yafara duban physical symptoms na hrt failure ajikinta yana kuwa dora kansa asaman kirjinta yaji faint parpalpitations with strong Shortness of breath ma'ana ba suma tay bama kawai numfashinta ne yakage ataciki yana mata wahalar fita waje, she started to look so pale nd more weaker, yasan badon ana ruwa ba da zufa tuni ya rufeta

thank god for his elite private club practicals da duk bazai san wayannan abun ynxu ba, dagota yay hannunsa yakaita motarsa seat din baya danya bata up front emergency help dan karta mutu masa ya shiga ukku,

niyyarsa saita farfado kafin ya wuce da ita can wajen haj mairo inyaso daga can anemi iyayenta dagatacan

kai tsaye yafara Loosening zip din doguwar rigarta then he sat her down comfortably ajikinsa ya fara Monitoring vital signs inta kafin can ya fara supplying mata extra oxygen baki da baki cikin ikon Allah kuwa tafara responding...

daga yadan hade bakinsu yahura mata iska yana shafa mata gadon baya ahnkli ahnkli sai kaga ta saki nishi me dan uban karfi wani hammmm sai tasake komawa lagwas ajikinsa amugun raunace, suna cikin wann yanayin bai hankara ba kawai yaga maza da sanduna suna ihuuuu suna fitowa wasu tagaba wasu ta bayansa duk sunga ayaanah kwance ajikinsa yadda yake fmr hura mata iska abaki yay kamar kiss sukeyi ga kuma hannunsa zagaye da ita ta baya nd he had no way to loosen her up face saida ya zarge zip din bayan rigarta..

kafin kace wani abu matasan fulani da buzayen nan kaf suka zageye masa mota suna kkrin zasu faffasa motar da sanda yay sauri ya kullesu aciki bai tsaya kintsa ta ba ya haura kan driver seat ya kunna motar ya taka motar da karfi ya dan razanasu har saida yaga sun ja baya baya.

ihuuu da hayaniyane ya cikkke wajen shikansa ibaad yasan inhar ya fito toh tabbas zasu kashe shi da duka dan yaga ga dukkan alama jahilai ne sosai kuma sunfishi girma da karfi

he was confused as to keep driving them off koya dau wayarsa ya kira gida akawo masa dauki, gashi aayanah ta kankame jikinta abayan seat, ko zip din rigarta bata mayar ba sai kuka kawai take mishi a motar kamr wanda yasota duk yarasa abunda ke masa dadi minti goma basuyi ba sai gasu juma da wasu dattajai sun faso..

nan akafara hayya hayya matasa sukace aisun ga me mota anan suna iskanci da ayaana shiyasa suke so su kashe su atare.

dakyar wani dattijon da ake ganin girmansa ya dakatar da hayaniyar ya karaso wajen ibaad ya kwankwasa masa window ibaad ya bude dan kadan, dacan har mutumin ya fara masa magana cikin bude ido dayaga ibaad din bai nuna alaman tsorata ba ne yatsaya yaji ba'asin sa. ibaad ya gaya masa shima ana ya sameta, snn zai basu yarsu amma inkuma suka tabashi already ya riga da ya kira hukuma ya basu information na inda yke ynxu haka suna hanyar zuwa nan kawai ajirasu su iso shi bazai ma fito ba sai hukuma sunzo.

dake yan kauye akwaisu da mugun tsoron hukuma sai kuma aka samu rarraben kai suka fara negotiating dashi, wai lallai saidai ya fito daga motar, ya basu yarsu hannu da hannu kawai ya wuce dama nemanta sukeyi in kuma be fito ynxu anyi magana ta nitsuwa dashi ba zasu kasheshi anan da duka inyaso duk wani abunda zai faru ya faru

dakyar da wuya ibaad yadau risk ya bude motarsa yafito tare da ayaanahn datake kukan tsoro sosai da alama ma batamasan zip din rigarta yana bude ba.

daga dattijon sai kuma juma sune akurkusa da motarsan sauran matasan dukkansu an umarce su da su tsaya agefe

...yawansu da makaman dake hannun su da ibaad yagani yasa kansa yafara juyawa kamr abun arxiki su juma suka fara magana da shi, da juma da dattijon ibaad ya musu bayani dalla dalla yadda ya same ayanah anan.

fuska ba yabo ba fallasa juma yace mish sun gode dama shine mahaifinta.....neman ta sukeyi ɓace musu tay.. amma tunda ansameta shikenan.

ibaad was kind of relieve dayaga sun fahimceshi, dan juyawa yay bayansa zai cewa ayaanahn ta karasa wajensu yana budan baki kamar kiftawa da bismillah yaji an buga masa wani abu akai da mugun karfi for good 30 minutes baisan inda yake ba sai kamr bayan mintina talatin masu kyau ya bude idonsa yaga hannunsa adaure gashi nan awani fadar kauye agurfane agaban wasu sarakuna su biyu, taron mata da matasa da dattajai sun zagaye su...

yana daga kai abunda yafara ji a kunnensa shine "ni juma maharazou naba da auren yata ayanah, inyaso yaje canshi bariki ya karasa abunda ya farayi da ita, danko mun kashe shi bamusan dan waye bane kuma yariga ya kira hukuma gara abashi yarinyar tunda yafara lalata yaje can da ita nayafeta ma duniya su je duk inda zasuje suyi iskanci suyi muna fatan har abada karta sake dawowa mana wann gari....

ran sarkin buzu ya turmusa ya baci baice komi ba dan sosai yaso abashi yarinyar sabida yaga tana da kyau sosai, amma kuma tunda akace musu a motar kafiri aka sameta harkuma ya cire mata riga yana shafa mata jiki sai yazama na bazai iya fitowa fili yace abashi aurenta mashi da almajiransa bakuma.

sarkin fulani ne yace shin kowa ya amince da wann auren??

kusan kowa ya amsa da ehhhh..

sarki ya mike tsaye ya kalle ibaaad cikin ido yace toh kowa ya shaida ayau Mun bayar da auren ayaanah yar gidan juma maharazou wa wnn mutumin mai mota..

agogon ibaad me tsada da suka cire a hannunsa sarkin fulani ya daga sama yace jama'a ashaida wann shine sadakinsa...

amugun rude ibaad ya daga kansa cikin daka ma sarkin burkitaccen tsawa yace 'a'a dakata min malam...wallah ban amince ba.
SURAYYAHMS
08060712446
[04/11, 21:22] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ⏯️1️⃣4️⃣
wani irin shiru wajen ya dauƙa ayayinda ibaad yagama daka ma sarkin fulanin nasu tsawa da wata iriyar kakkausar murya me razanarwa

"ban amince da wann auren ba, wllh yadda kuka kullashi ann haka xaku warwareshi..what in the world is wrong with u people haaaa daga taimako?...

cikin datsar numfashinsa tare da kai ma bakinsa duka dogaren sarkin yace "kaiiiiiii yaro ka iya bakinka!!kasan cewa agaban sarakuna biyu kake magana zamu iya kashe kafiri, mubinne mushen gawansa ann abanza, dan haka kama mutane shiruuuu ka rusuna kasa kayi ma sarakunanmu godiya da irin dumbin adalcin da sukamaka suka baka mata snn maza maza ka dauki matarka ka kara da gaba...

adaddafe ibaad ya miƙe tsaye jini ya taro a bakin sa still hannun sa biyu duka a daure cikin tsananin tashin hankli da bacin rai yace"wallh baku isa ba ku kukasan wani aure ni bansan shi ba, kuma baku isa ku lakamin wani auren karya ba, tunda har kunsamu yarku, ku kwance ni kawai na kara da gaba, inba tsaban hauka da jahilci ba kun sanni ne da zakumin aure???? kunsan daga ina na fito? waye ubana? haka kawai daga taimakawa yarinya akan hanya sai kucemim wai na aureta a ina aka taba daura aure haka...

Da wani irin zafi zafi dogare ya baaje rigar sa zai zaro dorina ya zanesa cikin tsananin izza da mulki sarkin buzu ya daga masa hannu snn ya kalle ibaad din cikin ido yace "kaiiii yaro kalleni nan..babu tsoro ibaaad ya daga kai ya kallesa duk mamakin yaron sai ya rufe jama'ar majiya da sukay shiru suna kallo

sarki yace duk tashen rashin kunyarka akwai wanda sukafika anan dan haka mu muka daura auran snn babu wanda ya isa yazo ya kwance shi.. akwai wasu sharuda da dole ne zamu gindaya maka akan auren nan inka gama rashin kunya da surutun banzan kan saika sanar damu ka shirya.

acikin kyabe baki sarkin fulani yace "kyaleshi, yana nufin daya lalata mana yarinya zaisha abanza ne bai aureta ba? tomu anan garin majiya duk wanda ya lalata mana yarinya yay iskanci da ita koda bamu daura masa aure ba aure tsakaninsu ya dauro..dan haka tun kafin raina ya baci na saka matasa su maka shegen duka anan gara ka fadi gaskiya snn kay niyyar tattara kafarka da matarka kubar mana gari..

atake jikin ibaad yafara rawa rawa cikin rasa abunda ke masa dadii tsaban bacin rai he was just in a total confused state kmr zai zauce...

cikin tattaro makansa nitsuwa dakyar ya dubi sarakunan yace banfa gane me kuke nufi da na lalata muku yarku nay iskanci da ita ba? ni a ina nasanta da zan lalata, wann karaman yarinyar har me zan dauka ajikinta...

cikin katse shi da hatsala juma yace" kaiii kafiri, karya kakeyi wallahi, karka sake ka raina mana wayo duk cikin mu babu wanda baigane ma idonsa abunda yafaru atsakanin ku ba...

da bacin rai "ibaad yace meyafaru wanda ban maku bayani akai ba?? me kuka gani, innalillahi wa inna ilaiji rajiun
..yallabai dakai fa awajen komi yafaru ni banyi ma yarku komi ba kuma kasani

juma baice masa komi ba ya jawo aayana a wani irin walakntcyrr ya finccikota gabansu a walakance kamar yar baiwa snn ya jefota har cikin fili tare da juyata yanamai nuna masa bayan zip dinta dake nan haryanzu a bude

yace "inba iskanci kukeyi ba uban mezai saka har kacire mata riga snn ka kulleta a motarka kana tsotsan bakinta? tunda ka riga ka lalata min yata toh fa dolene ka tafi can barikin da ita kaje ka karasa iskancin da ita acan wallah bazamu amsheku anan ba.

muryan ibaad na rawa rawa cikin tsananin tashin hankli da rudewa mai gauraye da bacin rai ya lumshe idonsa ahnkli yace "To hell with you malam!! ni ba dan iska lallatacce bane, kuma babu abunda ya hadani da yarka face mutuwar da ta tashi yi na ceto ran ta waiku wasu irin mutane ne haka abunnan ya faru a idonku ne snn kazo ynxu kana kawo wani xancen...just let me go out of this damn place

nan take juma ya hatsala yace au zagina zakayi da yaren ku na kafirai?dan iska kawai makaryaci, baqin kafiri, lallataccen banza dan wuta,..karya kake wallhi
Chapter 32 · 0% Book details