← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 161

Sashe 42

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ibaad ya kallesa da kyababben baki yace "seriously? ohh pls, not now mana.. saina settling a karatuna kadan kafin na fara tunanin me zanyi da rayuwata nan gaba. cikin rolling idanu maheer yace "ok fine, but the earlier the better. see yhu at d table. gyada kai ibaad yay har saida maheer din ya wuce part dinsa snn shima ya bude kofar dakinsa ya shiga ahnkli kuma cikin nitsuwa hoping to see ayaanah tagama wanke jikinta ta fito waje tana zaune akan kujera caraf saiyaga wayam snn dakin ya dauka da wani irinn shiruuuu kamar babu kowa aciki kusan ma yadda yabar dakin haka yazo ya sameshi..

kirjinshi har yana bugawa ya aje duka kayan akan gado da bala'in sauri sauri yay kofar bathrum din ya bubbuga da tunanin koma suma tay awajen yana can waje yanata bayani baisani ba...

kusan sau uku zuwa hudu ya buga dabaiji ta amsa ko tay motsi ba hannunsa harna rawa rawa wajen sauri da karfin tsiya ya bude kofar yashigo ciki adan gaggauce wanda karar budewa da shigowarsan ne yasaka ayaanah bude lumsashun idanunta data rufesu tamm tabi ta takure kanta akasa awani lungu tay shiru idonta nakan zubowa da hawaye.

yana hangota akasa arakube kusa da sink yaji ransa ya mugun baci, kai tsaye ya haɗe ransa kmr bai taɓa murmushi ba cos despite his bathrum floor is sparkling clean nd dry sam sai baiga dalilin da wani zaiso yazauna akasa acikin wajen ba...

tsawa yay niyyar daka mata sai kuma yaji ya kasa yin haka ya dan tsaya cak sabida rauni da tsoro dayake hangowa ajikinta sosai....kallo daya kamata zakasan cewa she is u can still grieving the loss of her sister inayah.

tunda ya shigo kallonsa takey a mugun kasale cikin jin tsananin tsoronsa ta kankame jikinta tareda jin matsanancin fargaba tana nishi nishi kmar wacce take shirin sumewa.

akanta yatsaya tareda zuba mata manyan hazel eyes dinsa that are sharp nd piercing, baice mata komi ba for a minutes sai can cikin tattaro makansa nitsuwa ayayinda fuskarsa take a mugun dore ya daga kirarsa sama yace "keee, menace miki kiyi? kanta ta sauke kasa ahnkli bakinta na rawa rawa tace "kace nayi fitsari'yace dakikay fitsarin sai kuma nace miki kizauna anan akasa wai ke wata irin kazamiyace iyeee daga kiyi fitsari ajiki saiki zauna a toilet?

shiru ta masa hawayenta na diddiga gwanin ban tausayi,

cikin sauke sihirtaccyar ajiyan zuciya yace toh "tashi"

a daddafe ta miƙe tsaye kanta na kallon tiles din, baice mata komi ba ya juyo wajen towels dinsa yasa hannu ya dau blue colour me kyau ya miƙa mata ta karba, ya dauki spare brush dinsa yasa tooth paste ya aje mata akan sink snn yay setting showersa zuwa warm yajawota gabansa kamar yar tsana giving her sound stern warning cikin zare mata ido yace "ki cire kayan jikinki, ki aje acan, snn ki daura wann towel din dana baki ajikinki, kishiga shower can kiyi wanka snn kidawo nan ki yi brush..kina gamawa ki fito..do not allow me to come back here for you for the scnd time.

shi baisan ma kotana jin turanci ba amma ganin yadda take gyada mai kai da sauri sauri cikin jin mugun tsoronsa yasaka ya kyaleta ya fita waje.

bayan ya rufe mata kofa kai tsaye ya fara kimtsa dakinsa kamr yadda ya saba, ayaanah stood for a while tana bin inda yabin da kallo, can kafin nan ta share hawayenta ahankli ta aje towel din ta kunce zaninta ta cire kayan jikinta duka ta ajesu agefe kamar yadda yace mata tayi

wani irin sanyi ta dingaji
sabida akwai A.c har a toilet din dakyr ta shiga shower sabida bata taba wanka aciki ba komi tanayine da tsoro tsoro har saida ruwan dumi yafara malala ajikinta sann taji kamr hanklinta yafara dawowa jikinta sosai.

she saw all his expensive gels nd soaps collection dake ta iya karatun turanci sosai kuma tana da ilimin ganewa amma dake batasan ya ake amfani dasu ba sai batay gigin taba masa abunsa ba.

acikin shower tay tsarki ta tsuguna ta wanke koinanta sosai da ruwa tafita tass, ta murda wani abu taga ruwan ya dauke sai tazo gaban sink din tay brush ta wanke bakinta, tay alwala tabi ta dauki dankwalinta ta rufe sumanta daya jike shataf jikinta na ɓari sosai ta bude kofar ta fito...

samunsa tay a zaune akan reading chair yana duba wani katon text book na anatomy and physiology sama sama sabida duk sun wuce basics din a private club dinsu...

irin kallon daya ma fatar jikintan ryt from head to toe yasaka ta sunkuyar da kanta can can kasa jin yay shiru ahankli muryanta na rawa rawa tace "uhmm mai mota...cikin katseta da mugun kallo yace "kee??? arazane ta kallesa yace uban waye mai motar ki? wani irin kankame dankwalinta tay zata fashe da kuka yaja tsaki yace"kar in sake jin kin kirani da wannn sunan now go on nd tell me meye matsalarki

bakinta na bari tace "na gama wankan ne..

yana miƙewa tsaye da sauri ta ja baya ta mannu da kofar a mugun tsorace tana hawaye

baiko kalle ta ya wuce ya shiga bathrum din kallo daya yamata ta karaso ciki, a miskilance yace "go back in der. ya kara nuna mata shower. snn yace kijje ki kara wankan and dis time use soap on ur body kingane me nake fada? da sauri ta gyada masa kai tunma bai fice ba tay sauri ta koma cikin shower ta tsaya, she read all the product on scrolls, har saida tagane wanne zata dauka aciki, koda ta rarumi katon shower gel dinsa tafi mintin biyu tana kokawar budewa, dakyar tazo tagane inda abun yake da yadda ake amfani dashi tana matsawa da karfi kuwa ya fantsama mata a fuska sauran yabi ya zube all over the floor, wanda ya zube ajikinta ta karasa mulkawa sann ta saka ruwa ajikinta wani dan uban kumfa da qamshi da tsantsi atake ya rufeta tana gama dauraye jikinta ta jawo towel din ta dora batare da ta lura ba tana saka kafa waje kuwa wani uban tsantsin gel din data zubar ya jawota waje suuiiiiii ya fetta ta akasa wani dan uban ihun razana ta zuba shikansa baisan sanda ya turo kofar agaggauce ya shigo ciki ba..

ganinta akasa yasa bai yi wata wata ba ya karaso wajenta yace meye faru? kuka take rabzawa dakyar ta nuna masa kasar floor din yaga duk gel dinsa ne akasa ya karkada kansa ya dauketa cak ya fito da ita ya ajeta akan chair snn yadan tsuguna agabnta ya kama kafarta ya dudduba koina yana mammtsa shi tsabar dadin dataji ita dakantan ta dena kukan tay shiru... dabai ga komi ba ya miƙe tsaye yay wani lungu after few mins ya dawo da white bathrobe dinsa ya lullube mata ajiki dashi snn ya umarceta data tashi ta karasa sawa sai ta bashi wet towel din, cikin saibi tamike ta aiwatar da hakan tana bashi towel din yace mata ta zauna, tana zama ya tattara jikakken suman ta duka acikin towel din ya daure mata shi tam tam snn ya kunna room heater acikin dakin for about 5 min, ya je ya dauke men hair dryersa ya kwance mata daurin kan ya fara bushar mata da gashinta yadau lokaci sabida yawa da tsayin sumanta har saida ya gama busharwa tsaf,lokacin ayanah kallon kasa kawai takeyi dan ko motsi batay iyayi bare tari.

tunda ya gama bushar mata dakai taji dumi ya dan gaurayeta daganan sai bai sake kulata ba, kyaleta yay anan for a while yaje ya wanke cikin bathrum dinsa ya tattaro kayantan data jika da fitsari yazo yasaka a engine ya wanke ya matse kafin nan ya dauke body oil insa ya bude yazo yana zuba mata kadan kadan a hannu tana shafawa a hannu fuska da kafarta, daga inda suken ya mata nuni da kayan sawanta akan gado yace yabata 3 mint ta saka kayan ajikinta ta jirashi yana zuwa, tun kafin ta amsa taga har ya fice abunshi, he went out of the room for a while, at exctly 3nd half minutes saigashi nan yadawo yazo ya sameta har tasaka sabon pant din da short ataciki da doguwar rigar da ya dan mata yawa kadan amma baiwani damu ba

suna hade ido tadan sunkuyar dakanta can kasa, ahnkli tace "umm.. zanyi sallah"yq kalleta da mamaki kafincan ya gyada kai kasar wuyarsa yace good for you. wucewa gaba yay barta a tsaye ya dau sallayarsa ya shimfida mata yana tsaye yana kallonta har ta cusa gashinta ciki ta dauresa gamgam sosai sabida yanada tsantsi snn ta gyara zaman mayafin gown in akanta tafara sallanta a nitse,

da gefen idonsa yake kura da ita she really looks pale nd light weigh, kamar jiri jiri yana janta har dai ta idar, tay adduarta hawaye ya cika mata ido ta juyo da sanyin murya tace mishi ina kwana?? sosai ya sha mamakin unxepected halin nitsuwarta daya soma gani sai kawai ya amsata da kai...adan dakile yace mata"are u done? tace uhm. yace "tashi ki biyoni..

babu musu ta miƙe yay gaba tafara binsa abaya tafara takawa ahnkli ahnkli kamr wacce kwai ya fashe mata ciki dan bakaramin rashin karfi da matsancin rauni takeji a zuciyarta da jikinta ba.

kan steps suka bi direct sashen bappa zaidu yakaita kusan kowani takawa sai taji kirjinta ya buga hardai suka iso wani mayen falon da bata taɓa ganin irinsa a kyau da girma ba suna shiga bappa zaidu ya bude kofar masters bedroom na gidan already ya gama shirinsa yay kyau cikin wata dakakkiyar coffe brown shadda ya dora matching colour borno cap mai kyau da kyalli wanda ko ba agaya maka ba kasan naira yay kuka ga designer cover shoes dinsa sai shinning take qamshin turarensa na original hugo boss tuni ya cikke falon da dadin qamshi..

ayaanah na baya baya har ibaad ya karaso da ladabi yace bappa ga yarinyar nan, i tot i shud bring her since she is ready.

kan ayaanah na kallon kasa bappa zaidu yadan lekota ganin ta kyakkwan gaske yasa yay murmushi yace masha Allah.. shigo ciki mana yan mata..
Chapter 42 · 0% Book details