← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 161

Sashe 129

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahnkli ta gyada masa kai yadora bakinsa akanta yay kissing goshinta lightly muryansa kasa kasa yace"i apologise on thier behalf
...murmushi me sanyi almost in a whisper tace thank you, and Don’t stop talking to me like this It will make me feel chosen...murmushin bazata ya kufce masa yana kallon kwayar idonta baice komi ba ya kara sakar mata soft kiss asaman goshi yakara jawota jikinshin sosai ..dan karamin shiru ne ya ratsa wajen tana lafe ajikinsa har saida yaga ta samu nitsuwa snn ya kalle agogonsa yace "kije can dakin kijirani i will go nd get u some cloth nan da 40 min prince hassan zai karaso sai muje wajen program din nasa tare ko? ahnkli tagyada masa kai tace okay toh saika dawo kallonta yake har ta miƙe da sanyin ladabi ta shige ciki shikuma ya mike ya fita waje...

gobe zanje na duba hakorina please use this pages as ur tmowrw page snn karku manta saura kiris ne mu rufe book 1..
#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[11/12, 14:11] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.

⏯️4️⃣3️⃣

ibaad yana ficewa cikin motarsa ya buɗe ya shiga ciki ya zauna snn yaciro hadaɗɗen wayarsa ya shiga wani site me 5str rating yay odering full set na kayan sawa da zata saka ajikinta hade da duk wani abunda suke buƙata for the night including a make up artist All his oders secured are arriving by 7pm on d dot cos they need atleast 1hr to get ready. yana gamawa ya kunna motarsa ya fice ya koma gida agaban masallacin bappa zaidu yay parking after few words dashi yajasu akayi sallahn magrib suna daf zasu shiga isha aka kawo masa duk wani kayan da yay oder in a fancy bag yasaka acikin motarsa

ana idar da ishai da minti 5 ya fice sharply yajeshi family house dan already bappa zaidu ya gaya masa cewa kowa ya dawo.

zuwa yay ya samu any cirko cirko ana ta hayya hayya a sashen hajiya mairo anty safeera ce kadai a sashenta sam taki fitowa dan tun awajen hidiman ashe sultana da safiya sukaji labarin abunda ya faru abakin masu aiki dake can sama suke lokcin da ake korar kawayen hajiya hamida duk sunji me sukecewa gameda walakanci da cin fuska da akayiwa ayaana.

sultana kuwa tun suna sauka kasa awajen ta zo tagaya gayawa ammi karama sosai ran ammi ya baçi tafara gayawa hajiya mairo kenan su ammi babba tazo tace ma hjiya mairo sam ba haka bane yafaru ta jujjiya maganan tace kawai ibaad ya sakalta ayaana ne dayawa waidaga an kirata za'a aiketa saitafara kuka shikuma yanazuwa sai ya dauketa suka tafi..

wann maganan har suka dawo gida anayin shi, ammi karama da nata version din, hjiya kuma tace sam ai agaban raihanatu akay komi kawai karya sultana tay ba ama ayaana komi ba sakalci me data samu ana daure mata gindi tana raina kowa.

itama safiya taxo da dogon baki na buga ruwan makirci, atake tahau bin bayan duk wani maganganun da hajiya mairo take furtawa tanamai cewa ai dama can haka yaa ibaad ya sabayi, koda ayaanah tay laifi ko rashin kunya baya mata fada ko hukunci saidai ya bi bayanta kuma shiyasa take aikata duk wani abunda taga dama.

ammi karama tay musu dasu akan wnn mgnan har tagaji da magana basu fahimce ta ba, haka hajiy mairo ta hau dokin zuciya akan batun cewa wai ayaana ta riga ta lalace kuma ibaad ke daure mata gindi tana iskncinta yadda taga dama a gidan ai baza'a taru amata karya ba.

tun dayaji tashin wnn hayaniyar sai bai shiga sashen hajiya mairon ba, ya wuce falon amminsa direct yana zama akan one sitter ya dau wayarsa ya kirata yace yana jiranta a falonta amma sauri yakeyi babu yadda batay dashi akan yazo falon hajy mairo aji ta bakinsa ba yace mata baida lkci tazo kawai.

kyalesu tay ta fice hajiy sai masifah take ta inda take shiga batanan take fita ba tanamai cewa ai rayyanu yasan baida gaskiya ne shiyasa yaqi zuwa gabanta ynxu ya fada abunda ya faru kuma wallh zata dau mummunan mataki akan irin rashin kunya da sakalcin da ayaana takey agidan nan musmn wa manya.

Da bacin rai Ammi karama tabar sashen tazo ta samesa yana zauna bayabo ba fallasa suka gaisa

zata fara kawo masa maganan yace "mata tabar hajiya kawai ta yarda da abunda take so ta yarda dama ita hajiya mairo one sided tafiye son yanke hukuncinta kuma kodama yajr ya gaya mata gaskiya yanxu inda akan batun ayaana ne bazata taɓa yarda dashi ba..

dakyar ammi karama tabar maganan dan tasan sultana bazata taɓa zuwa tana kuka kuma ta mata karya ba beside tasan ammi babba bazata taɓa fadan gaskiya akan ayaana ba.

bayan ya lallabata tabar maganan snn ya sanar mata cewa zaijeshi program tunda ayaana na tare dashi yana neman izini awajenta zasuje tare nd he wll bring her back home safe in an tashi.

few question ammi tay masa bayan ta qamsu da inda zasujen sai batay wani gardama ba ta kyaleshi, dan tasan muddin ayaanah ta shigo gidan nan yanzu haka hala hajiya mairo bazata mata adalci taji ta bakinta zatay xuciya ne ta zazzageta akan abunda bata aikata ba.

around 15min after 7 yabar gidan ya wuce quest house inda ya bar ayaana ita daya, female wokers din wajen suka bata wajen sallah tay both magrib da isha snn suka hada mata warm bath tay wanka ta shafa lotion snn suka kawo bathrobe me kaurin gaske suka bata ta saka ajikinta wanda har kusa idon sawunta ya kai, doguwar sumanta duka ta dauresa acikin towel tay zamanta abakin gadon dakin tana Allah Allah ibaad ya dawo....

after few min tana kwance da idanunta lumshe ahankli taji anbude kofar while she is still relaxing eyes closed taji qamshin turarensa ya bule wajen atake, cikin bude ido tareda miƙewa xauna tana mai dadda gyara zman bathrobe din ajiknta da sanyin sallama ya karaso ciki da ledan kaya ahannunsa tamiƙe tsaye dq amsar sallaman abakinta snn ta karbeshi da ladabi, ya hade harda hannunta ya rike yana mata wani irin kallo yace i took so long ko? cikin idonshi take kallo tace"..uhm but i am not bored! kallon bathrobe din jikintan yay yace "mmm i can see that..nan saiya sake mata hannun tare da kayan duka cikin sauke ajiyan zuciya yace "get dress dan its almost time

kafin ta amsa yace "i wll be in d oda room zan shirya acan, snn wata mata zata shigo nan yanxu ta tayaki shiri nd w'll meet in 15min, yeah? da sanyin murya tace "yeah..daga nan ya juya tabi bayansa da kallo yana ficewa kuwa sai ga wata siriryr mata ta shigo da wani katon akwatin kwalliya

tunda daga kofa dataga kalar kyaun ayaana ta fara mata murmushi

salam alaikum gud evening maam...

ayaanah ta amsa ba yabo ba fallasa tace kece zaki tayani shirin?

matar tace yes maam both make up nd styling can we start? ayaanah tace sure...

gaban madubi suka karasa kafin kace wani abu har sun fara the lady was very cheerful professional nd fast kusn komi zatay sai ta nemi cikakken izini awajen ayana, dan hakane ma yasa ayaana bata sake an yanke mata gashin girarta ba which save them alot of time kawai shaping insa tay tay grooming dinsa dakyau snn ta zuba mata dark eye shadows, thick feline eye liner, da nude red lipstick dayaji lipgloss me kyalli, countour din ma sama sama ganin ayaana already tana da wannan natural kyanta duk dama simple hot kwalliyar bakaramin kara fitowa da ita yayi ba. idonta da sukaji thick liner suka kara manya so sexy looking dogon hancin nan an kara shapin yay zarr kmr ita ta yanka ma kanta, da dan karamin bakinta, wani irin gyara tay ma gashin ayaana, ta zuba masa original wavy gel agaba gaba, jelar wave daya me tsayi ta sauke mata shi ta side daya in a very classy way yadda kai tsaye zaka gane cewa tana da doguwar suma kuma yolo yolo, har saida sukagama da fuskarta tsaf kafin suka bubbude kayan sawan within few minutes suka ciro su, alexandre vauthier V-neck rose red designer maxi gown, with subtle shimmers, sai YVSL sandals in nude, da sleek red clutch, earing da neck piece kuma gold ne da karamin red rubie stone ajiki..tana gama saka kayan matar ta dora mata nude turban kalar shoe inta tay mata push dashi kadan, matar sai rawan jiki take tsabar yadda taga ayaananh ta kure mata kyau she kept asking ko ita asalin yar nigeria ayaana saidai tay mata murmushi....da wuri suka gama komi tabar ayaana a tsaye tana kallon yadda tay ma kanta wani irin kyau

nan matar tafice taje ta kwankwasa ma ibaad kofa tareda sanar dashi cewa sun gama, he paid her nd gave her extra tip saboda ta rokeshi ko zata dau hoton fuskar ayaana ta zuba a cataloge inyaso kamfanin su zatana biyan ayaanan weekly, amma yaki sam, yace mata matar aure ce kuma baison fuskar matarsa akowani irin professional catalogue so she understood him and left.

da har zai koma dakin shi yagama shiryawa yaji kai bazai iya ba, jacket din suit dinsa dasu wayarsa da wallet dinsa kawai ya dauko ya kulle dakin da key gabaki daya qamshin jikinshi ya gama karade ilahirin gidan da wani irin sanyin dadi me ratsa zuciya da kwkwalwa signature perf dinsa zhexoff naxos tareda Tom Ford Noir Extreme ya shafasu duka atare,he is wearing a crispy white shirt me open collar mahadar midnight black tailored suite dinsa from Brioni, irin single breasted sharp shoulders din nan with no tie da black leather chelsea shoes sai hddn agogonsa na patek philippe daya fito yana kan kkrin mannata a hannunsa cikin sauri

kai tsaye dakinta ya nufa ya bude kofar ahankli daga kofa ya tsaya cakk ya zuba mata ido fuskarsa na kkrin canzawa tana juyowa for a moment ji yay kalamai sun dauke abakinsa gabaki daya...

tana murmushi tace yaa did i look okay??
Chapter 129 · 0% Book details