← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 161

Sashe 56

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hawaye nakan zuba a idonta tace nifa wallh nagaji da mummynmu, itafa asalin muguwace bakiga abunda tay ma ayaanah bane da karfi tajeta shakure mata wuya tana buga mata cikinta, kullum sai tay fushi da su yaa maheer kuma takiyin mana abinci tabar mu sha yunwa kuma saitana ihu tana zaginmu duka damu da babaa..

Kallonta ammi karama ta dingayi da mamakin jin abunda take furtawa, kafin can takara jawota ta rungumeta ajikinta gently tadinga sassaita tana cemata tay shiru ta dena cewa hakan aikomi zai wuce..

sultana tana kukan sosai tace
ammi nide kawai ki amince zaki zamo mamanmu wata rana..

tana shafa kanta da tausayi tace in sha Allah sultana koda bana cikin gidanku i wll alwys be ur mother kinji ko

wasa wasa dakyar ta rarrasheta snn tafara mata few questions akan abubuwan da ya faru, wasu abun da bata gaya ma babanta bama duk saida ta gaya ma ammi karama, ammi was also very shocked to hear the full story, sai yanxu kuma tagane cewa ashe ba ma ayaanah ake son kawo hari ba asali tea din da ake shiryawan na bappa zaidu ne ake son saka masa asiri aciki

nasiha tay mata cikin hikima tace mata duk randa taga mamanta tasaka wani abu a abincin babanta karta sake ta barsa yaci, snn maza taje ta gaya masa dan kar wata rana ya mutu abarsu da kukan rashin sa,da iya ka wnn kalman ta dan razana zucyar sultana tareda cusa mata raayin zamowa very alert musaman akan abincin baban nasu.

..tun bayan nan tay shiru da tunanin abun aranta at same time tacigaba da rarrashin sultana har tay shiru batare da tace komi ba

suna zaune nurse ta shigo da ayaanah akan wheel chair cos she is weak nd drowsy tafiya ma bata iyayinsa sosai yanxu

suna hade ido sultana ta tashi taje ta dan rungumeta tanata bata haquri. ayaanah taji dadin ganinta sosai. nurse din tana ficewa ammi ta jawo su duka,ita ta gyara ma ayaanah position ta dora ta akan gado azaune ta sassaka mata pillow abayanta snn sultana ta zauna kusa da ita tana share hawayenta suna kallon juna...

kallon ayaana ammi karama tay cikin tausayawa tace "yan mata ya jikin naki?? ahnkli ayanah ta dinga kalonta ganin tamata mugun kama da ibaad bakinta na rawa rawa tace da sauki..

she introduce herself as a mother very gently to her, tace mata karta damu zata kula da ita..nd she wll be fine...wata nurse ce takara bude kofar tace ma ammi doctorn sun yana son ganinta yanxun a office dinsa dan zai tafi

kyalesu tay subiyun tabi bayan nurse, tana fita sultana tahau gaya mata cewa ai wann itace mummyn yaa ibaad kuma tana da kirki wata rana ma itace zata dawo mamansu..

ayaana batasha mamakin hakan ba sabida tariga taga kamanninsu sosai..kuma ta lura matar akwai kirki da sanyin hali

hira sukeyi daddaya it seem like duk ta kalle sultana saitaji kmr da addanta take hira...

cike cike ammi tay tabi ta karbo sauran drugs na ayaanah tana dawowa ta samesu suna hirarsu kadan kadan, atake ayaanah saita tsinci kanta dajin kunyar ammin ibaad musmn ma data lura kamar mutuniyar kirkice sam bata da hayaniya
...fresh fruit salad din data siyo ta bawa sultana da ayanaahn dan suna ci atare.

sai ita tafi tasamu anty hauwa acan waje daketa kkrin shirin komawa gida dantaje tay ma mijinta girki, nan tahau gaggaya mata abunda take harsashe bisaga labarin da sultana ta bata akan lamarin raihanatu, anty hauwa tace mata bakomi izuwa gobe zata bincika taji gaskiyan dan akwai wata kawar raihanatun datasani me son surutu tana aiki aitama anan asbitin amma sai goben zatazo kuma tasan duk yadda zatabi ga kwakwalo musu duk wani zancen raihanatu abakinta inde asiri ne ma zasu tabbatar tare da sanin kalar matakin da zasu dauka..ammi ta mata godiya ta bita rakata har waje sukayi sallama kafin ta dawo ciki..

samu tay har ayaana ta amayo dukkan fruits din dataci cikin kulawa ta karbeta a hannun sultanan ta kaita bayi ta wanke mata fuskanta da bakinta tass snn ta cire mata kayanta ta saka mata kayan asibiti sabo dall data karbo acan waje..

a very thick 3qtr gown green gown me round neck da guntun hannu tanata mamakin yadda taga ko gyarama ayaanan gashin kanta ba'a tabayi ba, she look neat in her body but very unkempt in her looks, sun jima a toilet da ammi karama tana gyarata, ayayinda ta aje kanta akan cinyarta tahau kitsa mata suman kantan into two pieces har saida tagama tass snn tadore mata jelarsa yasauka mata har gadon baya.

daga kayan asibitin da kitson duk bakaramin kara fitowa da kyaun ayaanah yay ba hannunta ammi ta kamo suka fito waje suka samu har sultana tay clearing wajen yay fess..ammi ta dauki ayaanah cak ta dorata akan gadon cikin lallami take tambayarta ko tanajin shaawar cin wani abu sai gabaki daya tama rasa me zatace dan batasan metakeji yanxu ba..

.....suna cikin tunanin irin
abincin da ayaanah zataci ya zauna mata aciki arund 2:30pm saiga sallamarsu ibaad tare da maheer dukansu sunsaka kananan kaya ajikinsu daya dada fallasa samartakansu. tun daga kofa ayaanah ta hade ido da ibaad saida suka karewa juna kallo snn tabi ta sunkuyar dakanta can kasa tanajin zuciyarta na buga akansa da bala'in karfi..

kallonta yake har suka karaso ciki suka gaida ammi, ayaana ta kara kallon ibaad ashagwabe as he was busy passing one lovely symphatethic look to her, cikin fahimar irin kallon tausayi dana sannun daya mata sukayi xhnging wani irin silent hrt to hrt soft glances at each oda batare da kowa yalura dasu ba, dama kuma hawayene fall ya cika idonta,daga can yadan girgiza mata kai ahkli da alaman kartay kukan saikuma ta shanye shi tasss tay shiruuuu..

satar kallon juna sukeyi har maheer ya taso ya iso gareta da fara'a ya tambayeta ya jiki itama babu yabo ba fallasa ta amshi ahankli tace da dasauki..

he was alwys so happy inyaga abincin ammi shiya fara zuwa gaban warmers yafara deban nasa dan yasan ibaad is a very picky eater, shidama bakomi yake son ci ba, besides yadda yake cin abincin sa very calm nd classy inkanajin yunwa bazaku shirya ba, dan ko ayanayin taunar ka ma kawai zai iyasawa kuyi fada dashi sosai awajen..

so he fetched his own seprt
yabar ibaad ma ya debi nashi, sunfara ci kenan wata nurse tazo tana gaya ma ammi cewa bazasu iya ma ayaana allura inbata sa komi acikinta ba ..duk da ammi ta mata bayanin yadda abincin bai zama acikinta amma still nurse din tace basuda wani option koyayane kawai asata taci abincin koda kadan ne...

while ayaanah dint say a word, tana zaune kusa da sultana da tun da tagaishe da yayun nata bata kara motsi awajen ba, babu yadda maheer baiy da ayaanah akan taci abincinsa ba amma taki sam...sai can da yagama cin nasan saiya fita dan yaga ko zai gwada siyo vanilla nd cokolate ice creams yaga ko zata iya sha,..

ibaad was eating his food slowly nd observing her, har sai da ya kusa kaiwa can karshe snn yasaka spoon dinsa yayita yayyanka eggs da namansa sukay kuci kuci, snnn ya taso dakansa yazo har ta kan gadon with an unreadable expression,

fusknsan nan amurde ya miqa mata sauran abincin nasa yace "try this one..ammi karama ta juyo ta zuba musu ido tanata kallonsu, tasan kowacce yarinya agidan na jin tsoron ibaad da har kamar zata masa magana tace masa ya kyaleta sai kuma tay shiru ganin kan ayanahn na kasa amma taga wai ta saka hannu takarba plate din daga hannunsa harta rike batace mishi a'a ba.

ajiyan zuciya ayaanan ta sauke duk a tunaninta zai juya ne yaje yazauna awajen zamansa not giving a damn kmr yadda ya saba sai kuma taga ya dada gyara tsayuwansa akanta kyam

suna hade ido taga ya zuba mata idonsa baya ko kiftawa ahnkli ta dau spoon dinsan tadebo iyakan nama da eggs wanda ya yayyanka mata da spoon dinshin tafara ci ahankli ahnkli..

kowa yana kallonta da mamaki har takusa cinyewa batay amai ba...ibaad ya ma sultana wani kallo babu shiri ta sauka a bakin gadon, yabi ya zauna awajen, yana zama yamata alaman ta dauko masa sauran abincin haka taje ta dauko, dakansa ya karba ya kara zuba mata one spoon of rice da two eggs da naman yasake rarrabawa sanda yay loma daya snn ya kara bata spoon din sai ta cigaba da ci ahankli

harsaida sukayi hakan sau uku yaga tafara fidda zufa agoshinta snn ya kyaleta ya miƙa hannu wa sultana ta kawo masa zallan ruwa na gora, ya bude yasha kadan ya miƙa mata itama ta sha ahnkli yace "good girl".suna kallon juna snn ya tashi awajen, hannunsa acikin aljihunsa kamar bashi ba...ya amshi plate din ya ajiye, yay excusing ammin shima ya fita waje..

har wani ajiyan zuciyar jin dadin ayaana taci abincin batare da tay amai ba ammi ta sauke, nan suka zauna kusa da ita suna jera mata sannu, jim kadan ibaad ya turo wata nurse daga wajen tazo tay ma ayaanahn alluran tasha kukan alluran dan yana mata zafi sosai hartagaji tay shiru kafin bacci ya daukata kanta akan kafar ammin..

after some time ibaad ya kira awaya yace ma sultana tafito suje gida tayi wanka ta canza kaya, bada son ranta ba tabishi shima wankan yaje yayi har 3pm ya wuce suna gidan maheer bai dawo ba. sultana tagama shirinta tsaf ta tattara kaya da zatakai ma ayaanah dakyar ma ibaad ya kyaleta suka wuce asibitin tare dan cewa yay ta xauna tay lesson dinta agida tajirasu har sai dare yayi sun dawo haka ta dinga masa kuka tana rokonsa dakyar yazo yaji tausayinta yace mata toh sutafi....

suna shiga asibitin ya ajeta aharaba ya shiga masallaci yay sallan asr yabi ya zauna yana bitan qur'ani abunsa .
Chapter 56 · 0% Book details