← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 161

Sashe 37

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

acikin nitsuwa da girmawa ibaad din ya tashi ya raka malamin waje, suna ficewa hajy mairo tahade rai ta juyo da bambami tanata kallon ayaana

da kmr bazatace komi ba can cikin girgiza kai da rage murya kasa kasa tace "hmmm, ke kuma yannan ai dabaki nuna musu bakison auren nan ba, wann aure ai kariya ne agareko ayaanah, duk taurin kan rayyanu yana girmama nagaba dashi hala ynzu da malamin nan yasaka mana baki ya roqesa ya amsheki a matsayin matarsa kodan kisamu kibishi binni da cikakken lasisinki, inba haka ba dayuwar mahaifinki juma zai zonan yakafa wani kwakkran dalilin da zai karbeki ahannun taawure kuma dai kinsan duk wani kalubale da zaki sha ahannun jikana rayyanu bazai kai rabin dumbin wahala da kuncin rayuwa da zaki kwasa a garin majiya a hannun ubanki juma ba.

dan shiru aayanah tay kmr bada ita hajyn ke magana ba, a mind intq gani take harma yaushe ta isa amata aure bare har ta zaɓi ta zauna da ibaad da tuntuni banda kushe lamarinta babu abunda taji yanayi. hawayen ta na zuba ahankli cikin tunani taki cewa komi, iyaka yawan surutu da lissafe lissafe da hajy mairon takeyi akan hakan saiyasa tadinga jin rauni da mugun tsoro maihade da fargaban yuwar komawarta hannun juma yanamai kare lullumeta, ahnkli wasu sabbin raunattacun hawaye suka dinga fitowa daga cikin idonta cikin rasa abunda zatace mata ta dadayin shiru tana sauke ajiyan zuciya ahankli....

karar bude kofar yasa hajy juyowa katse maganan da sauri, caraf kuwa suka hade idanu da ibaad, wani irin kallo tamasa da shirin masa masifar akan kin auren dayay saidai ganin yanayin daure fuskan daya tunkarota dashi yasaka ta sauko kasa da tempernta suka fara magana cikin hankli ayanah tana hawaye tanajinsu, yadda haj mairon take raki tana kara fahimtar dashi kalar hatsarin da rayuwar ayaanah zai shiga in suka bari hakan ya jawo ta koma kauyen majiya, da irin sharrin tsafi da mugunta dake cikin kauyen, ce masa take duk runtsi duk wuya ayaana saidai inzata zauna ahannunsa dan bazata taɓa bari aji labarin cewa baya tare da ayanah amatsayin ma'aurata ba inba haka ba juma da mukarabansa akauyen majiya zasu tsafeshi tass koma su kasheshi.

tace inma bazai riketa wajensa ba dole ne kawai ya tafi da ita birni inyaso zata gaya ma danta zaidu, ko muhammadu ko kuma surkuwanta fatima su rike mata ayanahn acan. da wani abu aran ibaad ya kalleta bayabo ba fallasa yace "hajiya duk hakan dakike fada fa bazaiyu ba, yarinya da ubanta da uwarta a raye sai ke kice akaita wani waje tay rayuwa, nidai bazan sace musu yarsu in kaita koina ba...ita kanta hjyn fada yay mata yace koda take matsayin kakarsu yakamata ta dinga tuna cewa ba alaqar jini ne ya hadata da taawure ba, taawure yar rikontace, wacce ta sameta sanadiyar aurenta na biyu, dan haka bata da wani hurumin yanke musu wann babban hukuncin akan yarsu..

kusan musu suka dingayi da kakar tashi akan wnn magann duk saikaji ka rasa waye me asalin gaskiya acikinsu...

sunq cikin musun har tawuree tasamu isowa asibitin dake taje gidan hajiya bata sameta ba, tun daga kofar dakin ta tsaya cak tanajin bayaninsu sai jikinta yayi sanyi sosai musmn data gane kmr ansamo yarta ayanah, Allah Allah take ta shigo saidai yadda taji ibaad din yake tsagewa hajy mairo gaskiya akan alakarsu matsayinta na matar kanin uba ga taawure yasa ta dan dakata kadan

yace "sam shi bazai tafi da wata ayaanah birni ba, inma kareta sukeso suyi toh ta zauna mana agaban mahaifyarta anan, hjy mairo taci kuka, tamasa zagin duniyan nan amma ko ajikinsa,

duk ta dauka tsabar baqin hali ne da ra'ayin banza yasa yake ture maganan tafiya kano da ayanahn gefe yana nuna bayaso, batason harga Allah tun jiya ya riga ya shirya yin haka aransa ba. babbn burinsa shine yajawo wata babban yarjejeniya a tsakaninsu dan ya zamana tay saurin jin maganansa akan batun dawowarta gida, in return shikuma saiyace mata zai wuce da ayanah binni. kawai de so yake yaga yadaureta da jijiyar wuyarta, dan ta amshi dukkan bukatansa, hajiya mairo tsohuwa ce mai son rikici yasan saiyay da gaske kafin ya iya rabata da kauyen nan na har abada.

suna tsaka da wann musun ahnkli taawure tabude kofar tare da musu sallama sabida bata da wani dogon lokacin batawa ya zame mata dolene taje wani waje me nisa ta ɓoye kanta nadan wani lokaci sabida aika aikan da ta rattabawa arzikin juma..

tanayin sallama kusan kallo daya ibaad yay mata jikinsa ya bashi ko ita wacece, caraf kuwa hjy mairo ta juyo baki na rawa ta ambace sunanta tana hamdala a raunace suka dan rungume juna cikin fashewa da sabon kuka tana tuhumarta ina taje

jin muryan taawure yasaka ayaanah tay firgit ta bude idanunta da suka gama jiƙkewa da ruwan hawaye dan yadda taji ibaad yanata rejecting inta yadada sawa jikinta yay sanyi bana kadan ba, sai ta dada aminta dacewa duk duniya ne aka tsaneta, ba zallan babanta da yan kauyensu ba, ita de da alama kowa ne baya son riketa.

muryan taawure dataji yasa ta kara fashewa da kukan itama ta firgita tana cewa umma umma jikinta na rawa har zata diro kasa daga gadon ibaad yay sauri ya rikota ajikinsa da karfi duk da firgicin fushi data farayi masa bai saketa ba har kafin nan taawuren ta sake hajy ta karaso wajensu ta amshe a hannunsa ta rungume yartan tsamm da wano mugun karfin shauqi ta lullumeta kamar za'a kwace mata ita dan ko kadan batay tsammanin zata zo nan ta tarar da ayanahnta ba...

sosai nauyin datakeji a zucyarta ya dan ragu data rungume ayaanah..koba komi tay riba tunda ta samu yarta Alhamdullh

dake taji duk abunda suke fada tun a kofa bata kula bayanin aayana ba har saida ta fara gode ma ibaad tanamai sakamai albarka da ya dawo mata da yarta wajen hajy mairo

kalamanta masu sanyi sosai suka ratsashi, idanunsa suka ciko da ruwan hawaye, tausayin taawuren ya hanashi furta mata komi kai kawai yake gyada mata cikin sanyin jiki har snn yay excusing dinsu ya fice waje agaggauce ya nufi motarsa ya shiga yazauna aciki tare da kifa kansa akan stiring dan yay catching breath insa...

hajy mairo batay kasa a giwa ba ibaad yana ficewa kusan tass ta kwashe labarin yadda akayi da batun auren ibaad da ayaanah tagaya ma taawure, itama taawuren bata tsaya ba tagaya mata iya abunda taje tayi ma juma acan kauyen majiya amatsayin daukar fansa wanda hakan ya razana hajy mairo sosai dan ta jima da sanin cewa taawure mace ce mai kunya da dumbin haquri.

sai kallon bakinta take tana salati.."la ha ila ha illahu, anya taawure kina da hanklin kuwa da kikaje majiya kika aikata musu irin wann tijara da dumbin asara? toh da yanzu sun kamaki sun suka kashe ki fa ma ubam waye zakiwa asara inba yarki ba.

kusan a zuciye cikin fushi taawure tace "hajiya koda naje majiya a shirye nake, akasheni mana,dama..meye zan samu na farinciki a duniyan nan bayan juma yay wa ƴata sharrin zina ya tozartata snnn ya walaknta gawarta, yanzu inba don ahannun jikanki ayanaah ta fado inace da har na mutu bazan san inda yata take ba? hajiya, gaskya bazan iya yafe masa ba, inda ace ma nabiye wa zafin zuciyata da har lahira saina kaishi wallah, yayi kadan ya kasa..amma kinga ai bankasheshi ba, dukiyarsa da lafyarsa na rabashi dashi kuma banajin dandanasani yin haka, dan ko yanzu akace na sake masa haka wallah wallah zan iya sakewa, kaf majiya ba'a isa a walakanta ni snn a walankanta rayuwar yayana ba. ..

tana maganan ne tana kuka sosai rungume da ayaanah

ganin irin birkicewa da fushi da taawure tay yasa hajy mairo kasa cewa komi kawai ta karkada kai tana hawayen itama can dai tafara bata hakuri tana lallashinta kana ganin taawuew kasan ba acikin hayyacinta take ba dan sosai mutuwar inayah ya ruguza mata duk wani kofar tunani ya kuma saka mata baqin ciki me tsanani.

tun hajya na lallashinta har ta hakura ta kyalesu da ayaanahn dan suyi jimamin rasa inaya da sukayi atare..

jikinta a sanyaye ta basu waje tana rufe musu kofa ahnkli ta tsaya agefe tanamai share hawayenta, can kafin tafito har waje ta isa gaban motar taje ta samu ibaad ya jingine kansa da stiring motarsa idanunsa a lumshe yay shiru kamar wanda yay nitso acikin tunani

kwankwasa mai kofar motar tay ya daga kai suna hade ido ya bude motar ya sauko kasa, wani iri hajy tay da fuska kmar wacce zata masa kuka, tuni ya bi ya hade ransa, tun kafin ta fara kukan cikin katseta yakawo mata offer cewa kafin ya amince yawuce mata da ayanah can gida sai inhar zata amince tazubar da makaman neman gaskiyarta ta tattara inata inata tabar garin tudu, if not shi bazai kai ayanah ko ina ba, snn zaije kano yagaya ma su bappa zaidu da uncle moh cewa tazonan ta sato yar mutane tariketa bada cikakken izinin iyayen yarinya ba. sabuwar musu suka dingayi, kusan ince ma wayo ya mata sosai, ya nuna mata kawai bata da mafita, ai tunda aurensun ma is invalid uban kowa ma yasan labarin shi baidamu ba, inkuwa har bata amince zata bar tudu ta koma kano ba saidai abari har juman yazo tudu ya dauki yarsa kawai inyaso yaje can ya kasheta.

still suna cikin wnn musun sai ga nan taawure ta fito da sauri saurinta tana share hawayenta da suka ki tsayawa, anan ta samesu agaban motar ibaad, tana isowa ibaad ya rusuna har can kasa cikin nuna tausayi da ladabi ya gaisheta, ya mata proper gaisuwa, snn yamata ta'aziyar mutuwar yarta inayah yadan babbata hakuri shima haka tadinga bashi hakuri akan abunda ya faru dashi akan taimakon ayaanah dayi..

cikin kwantar mai da hankali tace masa babu komi itama tafahimce shi, tasan kuma gidan su babban gidane, bazata so wani abu na rashin mutunci yazo ya faru tsakaninsu da juma ba, inde bazai wuce birni da ayanan ba babu damuwa zata san yadda zatayi a rike mata ita har sai ta dawo.
Chapter 37 · 0% Book details