← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 161

Sashe 104

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yau Waking Moment dinta ma daban ne hajiya hamida ne tazo da dakanga da wani irin expenisve botle of champaing da sassafe cikin tsananin farinciki tay poping fasss a sama tace baby girl… wake up. its ur day!!! Da tsananin farin ciki Zainab tabude idonta a hankali ta tsaya cakkk ta yi blinking sau dyawa saboda dakin nata ya canza tamkar magic land with all the light, dolls, and gift boxes sorrounding her, atake Tsigar jikinta ya tashi ta mike zaune cikin wani irin sautin murna tace "yeeeyy...finally, i am a graduate! awn nd dis is All for me?hajy hamida tay dariya softly tadan shafa kanta tace yess Everything for you, my daughter. You earned it. Today is your special day.”

tun bata amsa ba sai gan nan prof zayyanu ya shigo cikin dakin sanye da farar jallabiya yana murmushin farin cikin wanda bai iya boyewa,with this strong i am proud of u energy yace heyy "look..my princess is up! top of her class,best in the whole set Zainab Arifah Ina alfahari dake sosai, Wannan ba ƙaramin abu ne, zamu iya yi komi don nuna miki yadda mukeji princesss u can name anything in this world today nd i prmise u it will be yours..

da tsananin murna ta dora kanta akan kirjinsa ta dada rungumesa sosai tana jin wani irin sinadarin sonshi yana lulluɓe ta. da wani irin shauqi a muryanta tace i love u dad
...you are best man in this whole world. zan iyayin komi dan nasaka farinciki..dad..all this success is dedicated to u ...

idonsa kamar zai zubar da hawaye yace "Thats my girl.. i love u too my princess..ure my world. ta kara kankamesa ssai hajiya hamida ta dinga kallonsu feeling sober tanata murmushi sosai

jim kadan manya manyan kawayenta su Nala da Rukky suka iso gidan suka kawaye ta yadda ake ji da zainab din kowa ma zama yay sunai mata kallo kamar wata real princess.

professional yan kwalliya su biyu ne suka mata special makeover aka saka mata Wani shimmering italian pinkish gown da gold shoes, kayan ya kwanta a jikinta tamkar anzana ne ajikinta her Hair was styled neatly, aka mata subtle make up mai kyau irin nasu na masu shi, kawarta Rukky tana tsaye a gefe tana tahowa kasa da excitement. tun daga can tace “Nalaaaaa, yaufa akwai bura uba anyah kuwa arifah bazata makantar da yaran makaranta yau ba? Nala ta ce, we run d town remeber? Wallahi the whole school will bow for her today, Dukansu suka yi dariya.

at arnd 9.30 am aka gama duk wani shiri suka fito tare da ita iyayenta da kawayenta dukansu suka sakota a tsakiya suna masu yagalgalata, a cikin wata exotic convoy na mercedez bunker Jeeps guda hudu suka nufi wajen hidima cikinsu babu wanda bai tsokalo wankan kyau na fitan hankli ba.

Wajajen karfe tara da rabi suka isa babban conference hall inda venue graduation in yake security ne kaca kaca a school din har da surveillance drone

tun daga waje manyan motoci keta hayaniyar parking sabida ingancin karatun da ake samu awajen yasaka wasu masu kudin marasa girman kai suka kawo yaransu schl din duk dama basufi daidaiku ba.

Drivers suna gama parking ahalin prof sauka suka karasa ciki her family arrival was chaotic dan kafin ma su iso cikin aka fara zunde ana nunasu saiji kake ana ambatar the almansurs, ihun rans dinta kakeji "O.M.G its zainab Arifah almansur"top student! she broke the school record! kusn kowa idonsa nakanta suna takowa hannunta makale dana babanta tana wani irin yngatcn murmushi ana musu confetti har inda zasu zauna lokcin zuciyarta acike yake da farin ciki danji take kmr wa ita kadai akay shirya wann taron bama sauran dalibai ba.

decoration din wajen yayi balain kyau yaran masu kudin nan are all dressed like met Gala red carpet event, basu saka wani graduation gown ba kawai sai aka rabawa kowa expensiv silk graduation banner kowa yamakala wuya like a parade prince nd princeses.

Bangaren su hajiya mairo kuwa dake yau asabar ne tun jiyan ta dinga jadadda ma kowa fitowa da wuri dan zuwa wajen hidimar nan dan bawai zainab Arifah zataje ta gani kadai ba harda ma zumudin son taga zayyanu duk dama ya raba kansa da ita amma still akasar ranta tanaso koda fuskansa ta gani. haka tasaka aka tashi sassafe, tun 6 am aka hau shiri, dama kuma anyi odern abinci da kayan snacks anyi packaging insu in d best way possble duk na kaiwa graduation ground domin taya zainab arifah murnan gama makaranta.

kulthum da sultana suka saka designer gowns dake ynxu sunyi tsayi duk angirma sai bakaramin kwalliya me aji suka sha ba classy french gown ne ajikinsu amma na sultana mint green, na kulthum kuma calm champainge gold da duk wani matching accesories bakaramin kyau suka yi ba...

ayanaah ce kawai taki sakin jiki ta shiga ribibin hidima dan tafi dmuwa da abunda zai je ya faru acan,haka kawai takejin kwata kwata bata son tana ganin yayanta da anty zainab arifah, kuma wann intense feeling din sosai yake ginuwa acikin zuciyarta bana wasa ba. kowa na zumudin zuwa amma banda ita dan normal make up inta tay ta shafa kajol, tay lining lips dinta ta bishi da shiny lipgloss sai kuma yakara sakawa tay masifar kyau din harma fiye da wanda suka tsaya cancade make up tashirya tsaf cikin atampa exclusive green da pattern din yellow da baki, dinkin yayi mata kyau sosai, skirt ne with peplum blouse mai three quarter hannu, ba a sa komai a jikin rigar ba sai patterns din atamfar aka yi mata aiki dashi, dan kunne kawai ta saka bata sa sark'a ba, agogon gucci ta dauka ta mak'ala a hannunta tay dauri me push back kadan snn ta yafa veil me sharara tagama shirinta ta fito.

ayaanah tayi wani irin kyau, gashi tay tsayi zaka rantse su sultanan ma age mate nata ne, karfe tara da rabi kulthum suka fito daga dakin sukayi dakin anty safeerah, tana ganinsu tace "Masha Allah sisters dina kunyi kyau" kulthum na murmushi tace "not as much as you, sultana tace aikece beauty queen a dan shashance ayaana tay dariya kasa suka sauko suna jiran mujaheed mai kaisu yazo dan Already hajiya mairo da su ammi sun fara yin gaba, daga su yaran sai anty safeera ne ynxu agidan dake maheer akace ya tukasu su hajiy kowa yasan aransa ibaad ma yana tare dasu..jerowa sukayi awaje harabar gidan sunata daukar hotona da selfies da wayoyinsu.

agaggauce anty safeerah ta kulle dakinta wayar ta a kunne tana cewa haba mujaheed yanxu da kabisu maheer din uban waye kake so ya kawo yaran nan bayan ni anbarmin aikin tahowa da abinci
..maganan datake y kenan har ta sauko tana fitowa babban falo tana jan tsaki daga can kasa ta hango ibaad daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka casual ralph lauren shirt da sweat pant ajikinsa kafanshi sanye da slippers din Fenty, babu ma alamar zaijeshi wani waje, hanyan waje taga yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motar da wani irin sauri tace "ibaad, don Allah ga su kulthum nan ko zaka ajiyesu a awajen su hajiya tunda kai ma fita zaka yi pls dan Allah kawaye na ne har sun iso babu wani space a motar kuma bana so suyi driving da kansu, bai juyo ba saida yaji ta gama cikin ransa yace hmm wato dai yau shi yazama driver wa yaran nan,cewa kawai yayi "toh" snn ya sa kai ya fita. anty safeerah ta sauke ajiyan zuciya dan batay tsammanin ma zai amince da wuri haka ba.

hasken rana daya fara fita ya haska fuskar ayaanah dago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauka kanta tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara da yadda take murmushi ahankli. wani abu me karfi kamr sihiri yaji yana fizgarsa, cikin sauri ya dauke kai basu ma lura dashi ba saida ya shiga motar ya danna horn da karfi.

sultana ce ta farga ta fara zuwa kafin kulthum tabi bayanta ta shiga suka zauna a gidan baya da ido suka dinga ma alama ma aayana signal akan ta zauna agaba dan karma yace sun maidashi drivernsu ganin babu yadda ayaanah ta iyane yasa ta shiga gaban har zai tada mota jin dadin turarenta ya bugoshi ya dakata ya dubesu su biyun abaya ya daka masu tsawa yace "ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a bude kmr wasu dolaye ku fice min a mota kuje ku rufe kanku da kyau kuma kar wacce ta ɓata min lokaci...da wani irin speed suka sauko suka wuce cikin gidan da sauri fargaba yasa ayaanah jin kmr itama ta sauka ta bisu tana kama handle din motar ya kwace ya rufe kirjin ta taji ya buga idonsu sakale dana juna yace "where did u think ure going to? muryanta a rarrabe tace "kace...muje...cikn katseta yace "not you..suda bantaba gaya musu bane nace suje ke ai nasha gayamiki kidena tula kwalliya a fuskarki bakiji ba..u wanted me to see it ryt? toh nagani! cikin matsanancin jin nauyinsa ta sunkuyar dakai kasa muryanta na fita ahnkali tace "nifa ba kwalliya nayi ba, amma bari zanje na canza toh.
...dan dauke kansa yay cikin basarwa yace"i dont have that time.. just use ur veil nd cover it up banason irin wann dresing in da zai nuna wani part na jikin ki awaje.. jan veil din ajikinta tay ahankli ta kara rufe jikinta dashi, yana kallonta da wutsiyar ido yace "not like this, sake hade ido sukayi dashi ya mika mata hannu idonsa nakan veil din ajikin sanyin kunya ta zare veil din ajikinta ta mika masa ya rike duk qamshin ta ya buleshi
cikin lumshe ido da budewa ya kare ma jikinta takaitaccen kallo snn ya tattaro makansa nitsuwa carefully yay placing veil din above her head, ya dan rufe mata sama sama daga inda sumanta yake nunawa ta gaba she look abit matured now tamkr wata matar aure
Chapter 104 · 0% Book details