← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 161

Sashe 47

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babban damuwarsu kawai ta buɗe musu kofane domin kowa yay aikinsa tunkafin prof ya dawo aci taransu na rashin kulawa masa da ƴa, shiru shiru bata fito ba kuwa har suka gaji da sintiri suka hakura musmmn jin ta kunna loud music, wakar ozeba by rema na wani oron tashi a dakin tamaida gidan kamr gidan party wanda hakan yasa kowa ta hqra takoma maids station for a while...

Dagata daya bangaren kuwa wajajen 4pm na yamma ibaad ya fito daga school masjid bayan sun kammala normal lectures dinsu, dake yau din kwata kwata basuda wani private club activities kusn yau ranar hutuce ga duk wani student beginner a boyayyen club din nasu, iyaka yan assigemnt na Bio1201 da chem1241 da aka basu daga two lectures din da sukayi yau ya fito dashi wanda tun a ajin ya solving kayansa sabida he is far ahead of this basic level1 topics, already duk an kokkoya musu shi a matsayin basic introduction to medicine a club dinsu just recently inda ma ake hada musu da practical aspect na abubuwan sosai.

kasancewarsa smart guy kuma kyayyakwa dan gidan masu shi yasaka mutane dayawa daga classmates dinsa suke son suyimasa magana saidai kwarjininsa da yanayin emotionless fusknsa da kame kansa dayakeyi yasaka gabaki daya a ajinsu baida wani aboki
dan ko a seat ne shidayansa yake yawan zama batare da wani seat mate ba.

yana barin school masjid arnd 4:20pm yay gaban wata garden ya samu inuwa me sanyi ya zauna agindin wani decorative tree yana latsa wayarsa sleek champaing golden colour latest samsung galaxy me flip cover dake shi duk brand din samsung din kawai yake riƙewa bai fiye biyewa abun yayi ba.

kusan sau uku yana kirar layin maheer dan yaxo ya daukesa a mota suwuce asibiti saidai yana bugawa saiyanajin user busy da alama yabar wayarsanne a DND mode harynxu, after sitting for like 3 more mins ya tashi ya nufi gate yana tafiya anitse har Allah yasa ya kawo main gate batare da bata lokaci ba ya tsare abun hawa direct yace awuce dashi al-eeman private hospital dan ya dauko ayaanah su wuce gida.

ana saukesa a gate jikinsa a gajiye ya shiga ciki,not minding duk wani ido dake sauka akansa kai tsaye yy hanyar nurse station yadan leka ta glass windownsu daga can nesa sai baigan kowa anan ba, he stood der for a while yana daddana waya yana kiran layin anty hauwa amma duk ya kira sai yaji ba a dauka ba, can kawai sai yadawo baya wajen har reception ya samu wata nurse a tsaye yay tambaya anan aka sanar dashi cewa anty hauwan tana emergency ne saiya jirata na akalla five min yanzun nan zata fito..cikin gamsuwa da hakan yanema waje ya zauna shiru jin yunwa ta fara damunsa ga wani dan banzan tunanin yadda zaije ya tarar da fitinan ammi babba agida, duk saiyaji kmr kansa na juyawa cikin kkrin kauda wann tunanin aransa yafara kakalo tunanin gym routine dinsa da kwana biyu ya dena zuwa he was thinking of going back to gym training koda ma stress din dake jikinsa zai warware.

yana cikin wnn nazarin jim kadan wayarsa tafara kara yana dagawa kuwa yaga anty hawwan ke kiransa, cikin nitsuwa ya kai wayar kunnensa yay sallama yace mata yazo yana reception, atake anty hauwan tace masa ya karaso ciki ynxu.
..room3 ya nufa kamr yadda ta gaya masa, wajen was quiet babu motsi, ya tura kofar ahnkli da karamin sallama abakinsa jin muryanta kmr ita daya ne acikin room yakara bashi gwarin gwiwar karasowa ciki ahnkli ya turo kansa ciki yana shigowa kuwa idonsa suka sauka akan ayaana dake kwance akan gado mashak har ansaka mata ruwa

kallonta ya dingayi da mamki har ya karaso jikin gadon yagama bacci ashe takey nan suka fara gaisuwa da anty hauwa, out of curiosity yace mummy jiikintan ya tashi ne? da yanayin tausayi ta kalli fuskar ayaanahn dake kan bacci tace "mishi, ehh toh, she was just dehydrated nd weak, kaga can abincin da kuka bata da safe koda tasa abaki amansa kawai tay shine na aika aka siyo mata fruits ta samu tasha..then she dozed off for a while, tana tashi na haɗa mata ORS amma still aman bai dena ba shine kawai nasaka mata ruwa,"...kansa na kallon kasa ahnkli yace "thank you soo much mummy, kiy hakuri fa mun daura miki wahala.., tana murmushi tace "haba bakomi ibaad, amma gaskiya inaga yarinyar zata bukaci nitsuwa da kulawa, i think she needs a quiet nd peaceful environment to settle dan kamar she is grieving ne fa, ko kai bakaga hakan ba?

yadan sosa kansa kadan yace "mumy we are still working towards dat, kawai dan ammi bata zauna bane amma in sha Allah komi zai wuce awann fannin, tace amma meya farune, why does she always cry? ko raihanatu ta mata wani abu ne

a nitse yace a'a..dama yar uwartace ta rasu few days ago kuma inaga abunda yake damunta kenan, but i assure u she will get over it, cikin yanayin tausayawa anty hauwa tace ayyah,..Allah sarki wallah tana ban tausayi sosai, duk wanda baisan zafin mutuwa ba bai faru dashi bane Allah ya jikan yar uwanta, ahnkli yace Ameen mummy...kallon bed stand din tay tace "opps gashi ruwan ma ya kare toh bari nacire mata canula sai in tasheta a bacci saiku wuce ko dan nasan hala ka gaji...karamin murmushi yay yace" a'a mumy basaima an tasheta ba is best inta samu bacci. batace komi ba ta gyada masa kai ahnkli tafara cire mata ruwan harta manna mata plaster a hannu ayaana duk bata san anyi hakan ba. after giving him few words of advices akan jikin ayaanah da irin mugun zamansu da ammi babba cikin saukar da kai yamata godiya, daga nan ya gyara zaman laptop bag dinsa snn ya dauke ayaanahn cakk ya dan rungumeta akan kafadarsa suka fito har kofar asibitin anty hauwa ta rakosu har bakin titi ya nemi abun hawa suka dawo gida.

iskan hanya yaso ya tasheta amma jin qamshin turarensa yasaka ta kara lafewa akan kirjinsa tareda nitsewa cikin baccin sosai, lokacin already karfe biyar na yamma yayi, mai adedeta ya ajesu a gate din gidansu dede gaban masallaci, he was hoping in sun shigo gidan zaizo su samu an aje musu abinci kmr yadda aka saba aje musu kullum dan ya gaji sosai baison yakara ficewa

ayaanah tana hannunsa ya shigo har main palor, wanda tun anan yaga koina yay shiru kmr babu rai aciki, very gently ya sauketa akan 3 seatter cikin kulawa ya jawo soft throw pillow ya dora kanta akai snn ya miƙe tsaye yana shirin rarumo wayarsa daga aljihunsa zaiyi kira kenan saiganan sultana ta fito, jikinta all covered dq dogon hijabi har kasa da katon math textbook a hannunta zataje lesson..

suna hade ido tabi ta rakuɓu da jikin bango tazura masa ido muryanta kasa kasa tace sannu da dawowa yaa ibaad..
kallo daya yay mata ya dauke kansa kasr wuyarsa yace mata "sannu,..shiru tay sai after few min of silence snn yace "ina mutanen gidan kuma sai yanxu ne kikaga daman zuwa lesson din? cikin saukar da kanta kasa tace "a'a yaa..yunwa fa nakeji shine yasaka ban fito da wuri ba kuma ai mummy ma ta fita batay mana abinci ba, shine naje na dafa dakaina itama saddiqa mai aikinmun batazo ba...

yace "ohh sannu newscaster! "bakowa agidan kenan sai ke, to wani shirmen kuma kika dafa?

tay shiru can kuma saitace "indomie..cikin kyabe baki yace "toh good for u. daga haka sai bai kara kulata ba yabarta da ayaanah a falorn atsaye ya haura sama dakinsa abunsa, yana shiga ya aje yar jakarsa yq tuɓe gabaki daya daga nan wajen wanka kawai ya fada kai tsaye...

sultana tabi ta mance lesson zataje ta karaso inda ayaanahn take kwance tazauna daf da ita tanata kallon kyakkwan fuskar ayaanahn tana mamakin irin sanyin kyan da Allah ya zuba mata, for almost like 30 min tana zaune tana abu daya jin karar saukowarsa yasa tacire takalminta ahnkli cikin sanda ta ruga waje da gudu ta nufi spot din math lesson inta dake bayan gidan .

..cikin nitsatsiyar takunsa me daukar hankli ya karasa saukowa wanda tun dagakan stairs kwarjininsa ke haskawa, yasaka cool marron raymond shirt paired with grizly sand colour trouser da silver agogo. wnn hadadden qamshin turarensan atake ya fara aiko sauƙo ayayin da sassnyar qamshinsa yacanza iskan gidan gabaki daya ya rikagasa isowa,

kan ayaana ya tsaya direct yana dan taɓa fukarta da cold hands dinsa tay wuf ta firgita ta farka adan tsorace ayayinda raunatun kwayar idanunta suka fada acikin hazel eyes nashi ahnkli ta lunshe ido ta bude tun kafinta budi baki tamasa magana cikin sauke ajiyan zuciya datazo mai bazata yace "ke tashi kije sama kiyi wanka, zaki ga kayanki na jiya na aje mikisu akan gadona inkinyi wankan sai ki dauka ki saka ajikin ynxun nan kafin na dawo...gyada mai kai tay tana layi layi kamr wacce baccin bai gama saketa ba..har saida yaga ta sauke kafafun ta kasa ta miƙe tsaye lafya lau snn shima yasaka kai ya fice agidan da key din mota a hannunsa..

baiy wata wata ba ya wuce cikin gari gaban wata babban fast food joint mai hade da wata katowar groceries mall ya tsaya yay parking dan shima sosai yunwan ke damunsa dan haka babu bata lokaci ya shiga ciki ya dauki basket ya siya babban goran fresh milk,da fruits salad packs,da fried rice nd chicken with cream nd salads in 4 parts dan yasan duk tsiya a agajiye maheer zai dawo anjima shima.

yana gama siyayyarsa ya dawo gida still ya samu gidan shiru nd its almost 6pm amma babu wanda ya kara shigowa banda sultana dake can baya wajen garden dinsu da lesson teacher inta, dakinsa ya nufa yasamu ayaanah har tay duka abubuwan da yace mata tay neatly, he was impressed abit da kokarinta, dan yadda yaga bata yi masa wani shirme adakin ba she seem to be a fast learner..
Chapter 47 · 0% Book details