← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 161

Sashe 17

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taàwure ta kalleshi da karyayyen zuciya ganin ya zuba musu idanu mecike da tuhuma sai tay sauri ta taho gabansa domin ta amshi jakar dake hannunsa wanda tunkan ta karaso ya tsime tare da daka mata tsawa yanamai cewa "Ke da Allah. Dakata min awajen. ya dada haɗerai yanamai kare musu kallo"wai meke faruwa ne na ganku haka a tsakar gida cirko cirko? kuma ina kike nufin zakije da mayafi ajikin ki batare da izini na ba. kafin ta bude baki cikin masifa yace "ikon Allah wato abunda ake yawan gayamin akanki gaskiyane, dake da yaranki duka baku da tarbiya daga nasaka kafa nabar garin nan dandalin bushasharku kawai kuke buɗewa kina yawo kamar wacce bata da aure su kuma kmr wanda basuda uba, duk kinbi kina zubar min da mutuncina a garin nan ana gulma na akanki keda ƴaƴanki, toh wallh taawure nafi karfinki, karyanku yakare tunda na dawo gidana kuma da cikinki na dawo, zan nuna muku cewa ni juma, tsayyayen namiji nake agidana kowa cikinku sai ya gane kurensa agidan nan.. mtss yaja tsaki daga fadin hakan ya kama hanya yawuce turakarsa fuuuu ransa a mugun zafafe.

kallon bayansa taawure ta dingayi cikin rasa nacewa
jikinta a matukar sanyaye ta dawo jikin yaranta da suke zaune akan tabarma itama tazauna tay wani irin tagumi shiru ne ya ratsa wajen banda nishi nishin inayah babu abunda ke wulgawa, can cikin tunani taawure ta miƙa hannu tajawo sauran ruwan maganin zazzabi data jikashi acikin kwarya ganyen rai ɗore ne aciki tana kokarin bawa inayar abaki sai kuma taji jikin inayar yay mugun zafi harma fiye da kima.

hankali atashe ta tallabota ayayinda taji jikin inayar yafara mild convulsing kusan koinanta yana rawan ɗari, zanin inayar atake yadan subuce gefen cikinta na dama inda ya kumburo sai yay kamr wani babban kurji ne acikin nata.

a mugun tsorace taawure ta kai hannu kan kumburi zata taɓa taji meyene tana tabawa kawai inayah tay wani irin gigitacen ihuuu saida dukan su suka rude sukaja baya suna salati me ƙarfi

rawanin juma a hannu ya fito daga turakarsa a mugun razane shima kusan arude yana cewa wacce yar kafurar ce take mana ihu acikin gidan nan waye..waye waye me ihun nan...yan iska kawai marasa tarbiya da imani mutum ya dawo gidansa bazai huta ba kenan wata shegiyar yarinyace tay ihun nan inci ubanta.

da gudu ayanaah taje ta kara rungumar inayah tareda fashewa da kuka me tsananin rauni wanda kukan ayaanahn ne ya dan katseshi,taawure tay sauri tarufe kumburin cikin inayan da zani dan karma juman ya gani yayi musu wani fassara na daban dan talura kamar ransa a mugun baçe ya dawo daga boda.
#surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[27/10, 19:43] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE ƁOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️8️⃣

juma yana gyara tsayuwarsa yace...
"Dabbobi ne agidan ina tambayarku kuna min shiru?

araunace taawure tace megida dama jikin innari ne babu dadi tunda muka dawo daga tudu yau kwanan mu uku kenan tana zazzabi..

wani irin yatsina fuska yayi cikin katseta da zafin kai yace "toh sai kuma me? akanta aka fara zazzabi ne?yo akan dan wnn ciwon zazzabin shine har zata daka min irin wann ihun jahilcin acikin gidana yo uban waye yasaka mata ciwon inba iskanci da sakacinku ba, nide wallah kar a sake min ihu agidana. ku karata tacan da abun kunyar ku ai da ɗa namiji kika haifa min da bazai zamo rago har haka ba. sai a zauna ana ihu akan zazzabi? _Ko waata nyiɗi, ɗum yoɓa wuro.”_

yana gama maganar sa still yaja musu tsaki a mugun zafafe ya kuma wucewa ciki lokcin kuka inayah da anayahn sukeyi rungume da junansu abun tausayi...

ayaanah bata taɓa ganin addanta cikin wann yanayin raunin ba sai gabaki daya zuciyanta itama ya fara mata ciwo amma take kkrin daurewa sosai danso take ta koya ma kanta jarumta..

tun bayan faruwar wnn hatsaniyar taawure ta kasa xama dan ko kaɗan bata iya ganin yaranta acikin rauni suna kuka gani take dolenta kawai ta neman musu mafita, acike da jarumta ta miƙe tabi bayan juma cikin turakarsa ta samu har ya gama warware jakansa yaciro kayansa mararsa nauyi daya saba sakawa inzai dan fita majilisansu na dattawa a kofar sarkin buzaye inda kowani gida ake kawo kwanon abinci aci atare. sanin cewa tunda aka haifo ayaanah aka dena cin abincinsa a majalisa ke dada bata mai rai, sabida al'adar kauyen ne inhar duk gidanka mata ne toh andena cin kwaryan gidanka kenan har sai ka haifi namiji ko da guda daya ne. ya dawo daga boda da tsananin fushin sanin kayan abincinsa bai kare ba, gashi yana so ya fita yabar musu gidan yadansha iska acikin mazaje, shikansa inya tuna cewa duk gidansa mata ne sai yaji wani makokon matsanancin bakin ciki ya ƙara rufesa.

taawure tana shigowa tun bata masa magana ba ya bita da wani irin kazamin kallo na tsana, bata damu tadan rusuna agabansa tafara rokonsa koda zai bata izini taje ta nemo ma yarsu innarin maganin zazzabi, cikin magiya tace masa na asibiti yafi ci dan tsabar ta damu batasan ma ta furta masa haka shaf ta mance cewa ya haramta musu ambatar asibiti agidan sa....

shiru yay yana jinta face har saida ta ambace asibiti yaji bazai iya daurewa ba,wani irin harquka yayi Ya sare sanda ya buge bango tare da yin tsalle yace Weehoo…taawure ni kina gayen kalmar asibiti Kangon kafuraye?? Taáwure, anin k’ombon ma yanka....

muryanta na rawa rawa jin ya soma cewa wuyanta yakai na yanka a mugun tsorace" a'a mai gida lafiya nake niman wa innari.. da karfin rauni tace _Jikko on wondi sokka, ɗum no feere magani ganya walaa ɗum waɗa._ nufinta Jikin yarta ya yi zafi sosai, wannan ciwo ne mai tsanani maganin jeji ba zai iya warkar da shi ba.

wani irin ja idanunsa yay ya ɗada murza sandansa tsabar bacin rai jikinshi na rawa bakinsa har na tara kumfa ya nunata da shi yana cizza labba yace “ _Wallahi, miɗo yoɓi maaɓe, on no wala ndiyan...”_

da mamakin jin yace zai ci ubanta ta budi baki kenan zata amsashi ya rufeta da wata harzukakn duka

yanayi taawure ta saka ihu tana neman tsira amma yabi ya shaƙeta kamr zai kasheta ayayinda yaransun suke jin abunda ke faruwa duk jikinsu ya dau rawa anayah tafara kuka me ƙara.

wani irin kukan tsoro sukeyi suka rungume junansu suna kiran umma umma umma

duk da acikin zafin ciwo inayah take amma wani irin ɓari jikinta ykey tamkar mazari yanayinta me cike da zafin rai da zuciya sai cixgewa take tana Allah Allah ta iya koda miƙewa ne tsaye koda da ja da gindi ne jitake za taje takarbe uwarta, saidai ganin ciwon ya hanata koda motsawa na da can yasa tayi ihu me karfi lkcin numfashin ta sama yayi kamr zai dauke jin irin dukan da ubansu yakey wa taawure aciki kamar ba mutum ya samu ba, kuka suke suna kirar taawuren gashi basuda makwabta sune karshen gari daga dabbobinsu sai gonayen su

kamar daga sama ayanah tasake kirjinta data damqeshi tamiƙe tsaye arikice kuma a zuciye kusan idanunwanta a rufe tana kiran sunan ummanta da wani irin zafin zuciya me radadi abunda bata taɓayi arayuwarta ba sabida kowa yasan ayaana da rauni.

yauda dan uban gudu ta tsallake inayahn dake kwance tana nishi ba acikin hayyacinta ba takai zuwa kofar batajira ba kawai ta fanjama cikin dakin baban nasu da dama bata taɓa shiga ciki ba
tana shiga ta faɗo kan jikin taawure ta riƙeta dam dam tana wani irin razanannen kuka tana cewa...

"Baba no ɗuka umma maa! No waɗa umma maa. babaaa.. babaaaa no ɗuka umma..

sanadiyar kanannede taawuren da ayaanah tayi tana kukan cikin firgici yasaka juma ya hakura da dukan ransa a matuƙar bace ya dau rawaninsa ya dora bisa kansa jikin shi harna kyarma muryansa tamkar tsawa ya dube su duka yace falmata Wann ma kadan kikakga gani tunda rainin ki har yakai in saka doka agidan nan ki taka. dama can ana gaya min cewa na sake miki dayawa bansani ba saiyau dakike neman ki nuna min kuskure ne toh wallh baki isa ba. in kuma kika kara ambatar wani asibitina kafuraye agidana saina hallakaki daga ke har yayan naki dama ba amfanin komi kuke min ba banda kuci kuyi kashi. kai bari ma ingaya miki,' daga yau sai yau idan kika kara ficewa agidan nan abakin aurenki..shashasha mutuniyar banza mutuniyar wofi

daga haka ya saka kai ya fice baiko lura da inayah dake kwance awajen cikin tsananin murkususun ciwo kukan zuci da gushewr hankali ba.

ranar taawure tay kuka ranar bana kadan ba har sai bayan da abun ya lafa musu snn ta daure ta aike aayanaah jeji ta dan debo musu wasu ganyen ta aje kurkusa duk baqin cikin dake ranta haka tazauna tayita hadin maganin gargajiya ma inayah tana bata tanasha tana amai har dai zafin jikin ya sauƙa.

kwana daya bayan haka yasakance Yaune bappa zaidu sukay da ibaad akan zai kai ziyara da yammaci izuwa gidan su zainab Arifah, abun ya mugun tsaya ma ammi babba a wuyanta anma shi sam abun be wani ɗarashi ba, shide aransa yasan umarnin bappa zaidu kawai yake bi .

yau tun bayan sallahn asubahi ibaad ya dawo dakinsa yana ta rera karatun qur'ani for almost 50 mins ya dauko tundaga kan suratul ma'ida izuwa suratul taubah cikin hadda, bayan yagama ne ya dau lokaci sosai yanaima mahaifinsa adduar samun rahma a kabarinsa,snn yay ma mahaifyarsa adduar samun lafya da miji nagari, yayima da shikansa kafin yay ma sauran ahalinsa gabaki daya bai rage kowa ba, baitashi a wajen dayay karatun ba har saida zuciyarsa tay masa sanyi cos there’s always smthing heartbreakingly disciplined about him, shi namiji me dauke da wata inner wounds aransa na kalubalen maraicin uba ata young age that made him sharper nd not bitter nd hot tempered kamar yadda wasu suke fassarashi
Chapter 17 · 0% Book details