← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 161

Sashe 66

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamar wata mayya haka saida ta siya wani expensive botle na
Maison Francis Kurkdjian Amyris Homme perfume, a Fresh, woody, and very refined perfume. which According to Viora London is more classic Parisian ambrosia. perfect for sum one who is polished, intellectual and quietly wealthy kamar ibaad inta. da wata apple smart watch da niyyar kai ma ibaad su kyauta ranar asabar intaje tarban kakanta hajy mairo mai tuwo.

gani take tunda bai karban ma sister dinsa dukkan tarkacen chokolates inga ba ai dolene ran asabar ya amashi wayann kuma yasaka ajikinsa.

kafin ta gama waya da mujaheed maid dinta sun rage mata rabi daga kayan jikinta daga nan tashi kawai tay taje wanka, tay sallan isha ta tsalleka magrib sabida kyuwa, fav coffe dinta kawai aka kawo mata yaji madara tasha snn ta jawo computerta ta cigaba da karatu..

Daga nan gidan bappa zaidu kuwa ibaad na dawowa gida ya samu already maheer yana jan sallahn magrib a masjid dan haka aje bags din shpping din kawai yay akan gadonsa yay alwala yawuce masallacin shima ya jonasu

ayanah tana zaune a daki da tunanin irin saukin kai da kirkin da maheer ya nuna mata a case din satan nan, wanda har wajajen bayan isha kuma sultana bata leko dakin ba, ita tun tana fushi da ita harma abun yazo wuce mata, ganin ita dayane a dakin yasa tafara tunanin yin wanka...

dede lokacin an gama sallan isha'i kenan ibaad ya lallaba yashigo dakinsa inda ko taba bags din shoping din baiyi ba saiga maheer nan ya tura kofar dakin da sallama ya shigo kai tsaye.

idonsa kuwa na sauka akan shoping bags din yace woahhh damn..so may shoping bags.. and what are all these for? kuma kayan yan mata...wait man..did u go for shoping witout me..

ibaad yanakan cire takalminsa yace yeah, is for the girl..

maheer yace "what??amma meyasa? i tot sultana had enuf kuma she is ok dat they can share..ko dan sabida abunda yafaru dazune shikenan kuma kaje ka siya mata kayan sawa

ibaad zai magana maheer ya hade ransa sosai yace...look ibaad ayaanah fa yarinyace..nd so what if she took a piece of meat frm a pot..wann halin kowani yaro yanayinsa gigin kuruciyane ba dabiarta ba..i think both you and mummy are overly reactiive over this girl's issure, toh meye aciki dan ta dauki nama a kitchen taci?

cikin dakatar dashi ibaad yace "Dat is the problem maheer..i do not want her taking food or things..weda freely or stolen. beside i am very sure bata dauki wani nama ba, ka ma dena cewa waita dauka, dan nasan wallahi bata dauka ba.

baki bude maheer yace" 'harfa wallahi kakecewa.. hmm okay, tell me, why did u scold her then..

calmly yace "i know why
snn banason muja wani dogon surutu anan kawai kayi hakuri inhakan did not sit well with u. amma dan Allah kana duba condition inta..wancan karon ma kusan hakane ya faru yarinyar nan tun batagama farfadowa da jimami ba tazo gidan nan snn tasake shiga wani damuwa, nd then jiya ne kawai muka dawo da ita daga asibiti after spending 7 days in admission sai kuma in sake zuba ido adaketa akan namar da batama dauka ba?

cikin sauke ajiyan zuciya maheer yace "toh naji, hmm but you dont have to pay mummy with cash you knw.., sultana tagaya min duk yadda kukayi,she asked u to pay for damages nd u sent her the money, ibaad,..dat was rash nd stupid of you..in ita mummyn bata da hankali sai kai ka biye mata? yau in kuma baba yaji wann maganan me zakace masa?..i get that u want to protect her at all cost amma badai ta haka ba....kaima fa kasan halin mummy, farkon xuwanka gidan nan kaima batay kkrin kawace kudin abincinka agidan nan ba ne?.. son zucyarta yay yawa, inkana biye mata wallah sai kaga ta dawo da hakan kamr wani hanyar cuta da caca. dan haka ni zanje in ce mata ta maida maka kudadenka kawai yanzu nan ko wallah na hadaku duka da baba.

juyawa yay zai fice ibaad ya riko hannunsa da sauri da fuskan magiya yace maheer please Dan Allah kabari..i know what i am doing. kuma nasan inda kaine a position dina zakayi abunda yafi haka, kai bakasan ya mukayi da mummy dazu ba...i desprately want this girl to have a small moment of peace ne shiyasa ma nabada kudin bawai dan bani da hankali ba, please kaji tausayinta mana duk abunda ya faru da ita abaya akauyensu is still taunting her emotionly nd she is sick. wallah i will give twice as dis amount dan kawai a kyaleta, inkuma bawai so kake kajawo mata wani fitinan da zai saka ciwonta ya dawo full blown heart failure bane dan Allah kabari. let bygones ne bygone. let ur mum have peace in her marriage too, tunda na rabasu lafya pls karkay involving bappa aciki just let it go for the sake of the girl.

kallon cikin idon ibaad din maheer yaketay all this while yana reading all the sincerity dats coming out of it..

idonsa atake yay jaaa jikinsa sai yay sanyi sosai.

ahnkli ya kwace hannunsa ana ibaad din yace "okay fine..for the sake of the girl, amma badan haka ba da wallah bazan kyaleta da kudin nan ba...excuse me!!

yana fadin hakan yay waje jin hawaye na tarowa a idonsa yana shiga dakinsa ya zauna abakin gadonsa dan jiyake zuciyarsa na masa wani irin zafi sosai da sosai daga bisani ya tashi yay wanka da niyyar zai kira ibaad ya rakasa gidansu abdl gaffar suje sharply ya amshi assignmnt dinsa ya dawo gida yayi.
#SURAYYAHMS

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[20/11, 20:54] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: Susum writer:
⏯️2️⃣6️⃣_ABUNDA KE ƁOYE💫_
_Surayyahms_

https://www.arewapen.com/book?id=68b893fa83afa58b60006705

https://chat.whatsapp.com/HBrDJW5WI7h7uwSbRg77tf?mode=hqrc

https://vm.tiktok.com/ZSH3X6SPhYWXw-nxc0O/

wajajen 8.30pm maheer ya kammala wankarsa yafito direct ya tsaya atagaban gadonsa kuqunsa daure da thick white towel da wani dankarami daya riqo ahannun shi yanamai dabbing ruwan jikinshi slighly, wayarsa dake kan vanity table ya daga yana daga tsayen ya rubuta short text mssg ma ibaad akan zai rakashi gidansu abdl gaffar ynxu, yana gama tura masa text din yawuce gaban standing mirror yana kallon kansa a madubi not giving much tot ma yadda yaga duk ya xube kwana biyun nan yay kwafa kafin nn ya jawo kayan shafe shafensa yahau shafawa a smooth healthy skin dinsa ya taje kansa yay fess..

sharply ya saka wasu kananan kaya da hadadden jacket akai yafesa turarensa me qamshi kafin nan karfe tara yacika har ya fito waje,

kai tsaye yaje ya bugawa ibaad kofarsa, yana tsaye awajen after like 7 min sai gashinan shima ya fito sanye da rigar sanyi ta hoodie ajikinsa irin clean pure white colour innan da wandon blue jean da white sneakers duk sunyi matukar kyau har bazaka iya saurin bmbmce waya yafi haduwa dan kuwa danyen shekarun samartakansu na nunawa sosai..

Suna ficewa agidan bada jimawa ba saiga sultana tayo sashensu, ahnkli take tahowa tana waige waige looking so scared but dertemined to come nd tell ibaad the truth dan tun dazu abunda tama ayaana ya hanata sakat yana samata fargaba...

deciding tay gara kawai taje tagaya ma ibaad gaskiya inyaso ko dukan ta zaiyi still dai zataje tabawa ayanahn haquri halama taji tausayinta ta yafe mata.

tun bata karaso kofar dakinsan ba taji kirjinta yana bugawa da wani dan uban karfi kamr zai fita,acikin dauriya ta tsaya saida tay tsayuwr kusan minti biyu kafin ta tattaro courage ta fara buga kofar ahnkli har saida ta lura kmr a kulle yake snn ta koma ta duba na yaa maheer shima ganin da alama duk basu nan yasa tasauke wani maqudan ajiyan zuciya tare da barin wajen da bala'in sauri, direct ta koma quest room din ta cigaba da zamanta anan cikin sanyin jiki da tunani duk hanklinta ba akwance ba musmmn inta tuna cewa ita tay satar naman, kuma ayaanah bata tona mata asirinta ba har awajen yaa maher tay shiru...all this feelings are very new nd weird to her, ko karatu ta kasa yi sabida damuwa cos she tot she cud have defended her too, sosai taji babu dadi aranta data bari jin tsoron ibaad datakeji ya hanata yin abunda ya dace wa ayaanah dazu.

bangaren ayaanahn kuwa kusan komi ya wuce mata dama ita bamai saurin riko bace, she was calm abit musmn ma data shiga bayi ta watsa ruwan dumi ajikinta tay wanka tazo ta canza kaya.

tun bayan iddar da sallan ishai tabi ta kwanta time to time haka abun daya farun na dawowa mata ranta but she still wonders haryaushe ne sultana zatadena buya ta dawo cikin dakinta ta kwanta, tadauki tsawon lokaci tana wnn tunanin har tazo tadena tunanin qaddarar rayuwarta dana ummanta ya dawo mata afresh wasu silent hawaye na zuba a idonta tanaji kmr mafarki takeyi ba gaskiya ba. inta tuna irin mugun halin baban ta, da kuma irin zafin dataji da addanta ta mutu sai kuma tay shiruuuuu thinking maybe duk abunda ya faru dasu hala shine musu mafi alheri.

tama kasa iyayin tunanin makomar rayuwarta anan gidan musmmn tare da ibaad, da kuma mutane daban daban datagani wasu masu kirki, wasu mugaye. ganin tunanin zai iyafin karfin kwakwalrta sai ta dauki qur'anin gefen gadon ta mike zaune da pillow a kirji tarufe dogon gashin kanta da mayafi tahau karanta suratul Rahman ahnkli tanayi tanamai tuna nasihohin ummanta da na addanta game da rayuwa. tasan duk yadda akayi dolene kawai tay hakuri ta daure snn ta amshi sabuwar qaddararta, da wn sabuwar rayuwar, da kuma wayannan sabbin fuskokin dake zagaye da ita ynxu, duk dama aranta bata taɓa tsammanin hakan zai zo ya tunkareta adede wannan mayucin shafin qaddatararta bayan ta rasa addanta a duniyan nan ba.

karatun qur'ani ta dingai tana hawaye tana kuma tunaninsu har saida taji sanyi snn ta aje qur'anin ta kwanta cikin sauke ajiyan zuciya mai nauyi..
Chapter 66 · 0% Book details