← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 161

Sashe 68

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikin katseta da wani salon manyance ahnkli yace but mummy you have to be careful akan wasu abubuwan da kikey agidan nan, which i think sune suke sakawa baba yake miki wasu abubuwan.... wani uban harara ta banka masa tunma be gama rufe bakinsa da tsawa tace kuttuman uba?maheer mani kake gaya wa haka?ta nunasa da yatsa" kai karka kara gaya min maganan banza anan..uban menake muku a gidan? kaidai fito fili kawai kace wata mace ta shanye ubanka baya ganina da daraja a idonunsa yanzu...

sounding sooo stiff nd arqumentative yace"...or, maybe he need alittle quite somehwer else, kece kullum fada tsakaninki da shi akan ammin ibaad, kuma haryau bai kare ba, mummu ke kadai kin tsani duk wani baqo yazo gidan nan, kin tsani ibaad, kin tsani yarinyar da aka kawo which u knw ba dawwama agidan nan zatay ba..shin baki tunanin duk sune suke gajiyar da baba yake miki haka?

hannu ta daga azafafe zata wanka masa mari ya rike hannuntan yana kallonta da calmness a idonsa ahnkli kamar wanda baison wani yajisu yace "mummy calm down" har cikin ranta taji tsoron cold voice din dayay maganan dashi ..manyan idanunsa ya dasa anata snn yace"nafasan cewa kin karbe kudi me yawa awajen ibaad, nd i knw how much u took frm him duk dan sabida yarinyar nan..and before u even started shouting at me kisani bani kadai nasan hakan ba, sultana ma tasani, dan itace tafara gayamin kafin nima na binciko
...even if ibaad does not plan to expose u, kinsani idan baba yazo yaji maganan bazaiji dadi ba musmn idan yazo yasan cewa yarkice ma tamiki satar nama ba yarinya ba...

wani irin kwace hannunta tay anashi da karfin hatsala tace da Allah sakeni karya kakeyi, i cought her red handed...cikim katseta yace "yes".. but sultana has already confessed har agaban ibaad cewa itace ta dauki miki namanki ta bata.. mummy, pls stop what eva ure doing dan Allah... ki rabu da yarinyar nan .bcos if u cant muma bazamu iya yin shiru akanki batare da mun gaya ma baba wasu abubuwan dakikeyi agidan nan da bayanan ba.
uve alwys said that bana kaunarki...well let me tell u, ranar da kika bar gidan nan da mukazo shiryawa zamuje schl da ibaad i came to dis room nd i picked ur phone up, na bude na naga text messgs da kukay ta exchanging da kawarki akan maganin dakikazo har schll kikamin karya akai wai na ciwo ne, mummy inda ace bana kaunarki wallah da sai na gaya ma baba kuma na nunasa abunda kiketa shirya akan rayuwarsa...but for god sake mummy pls dan Allah kibar aikata wann abubuwan.

u know i wll alwys know the truth..i am curently the best law student..but i cant save you if u cant save urself mummy dan Allah kibari wann batun sihiri sihirin let peace reing in this house for once..

wani irin cak tay da fuskar ta tana kallonsa a kangare ahnkli numfashinta yadinga fita sai tarasa borin kunya zata masa ko borin hauka..cikin jin tsoro da shan mamkn yanayinsa saitay maza taya juuya masa
baya cikin hatsala da fushi ta fashe masa da wani irin kukan makirci tafara wasu irin irin magangnu out of self pity tana cewa ai sharin shaidan ne kuma ai tunxirata ubansa yayi

obseving inta yay sosai snn yay murmushi me sanyi kmr bashi ba, jawota yay ta zauna akan gadon shima zama yayi kusa da ita yadan rungumeta yana rarrashinta daga ganin ta kasan ta mugun girgiza da kalaman nasa, sai kuka take tanata maganganu cikin borin kunya sai yay amfani da wann damar yayi silencing dinta gabaki daya akan haukar borin datakeyi a gidan nasu gabaki daya, he showed her yana tare da ita sosai kuma yana sonta amma bata wannann hanyar data dauko na cutar da mahaifinsa da yan uwansa ba.

bata da choice haka tay mazamaza ta zubar da makaman yaqinta a idanun maheer bawai dan ta saduda ba sai lura data cewa yasan abubuwa dayawa akanta ynxu wanda zasu iya kashe mata aurenta na har abada gashi mijinta yace inta sake furta zata tsine masa toh abakin aurenta, bata taba jin nadaman barin maheer ya karanta law ba sau yau, dan tsabar bincike iya kwakkafinsa da wayonsa yay yawa kuma tasan zafin ransa sarai dolene sai tabi shi a hankli...

bayan sun kammala maganan duk sai ta fasa zaman dakin ta fito kitchen ta fara shirya musu abincin karyawa da already batay niyyar yinsa ba.

sultana tagama shirin scholl kenan wayarta ya fara kara tana ganin ibaad ne da sauri ta dauka a ladabce tay sallama, yana amsawa yace tacewa ayanah tazo ynxun ta sameshi a dakinsa. tana sauke wayar a kunnenta tace ma ayaanah yaa ibaad yana nemanki a daknsa, itama bata wani jira ba ta cuccusa dogon sumanta acikin dankwalinta snn ta fito kai tsaye ta wuce dakin nasa..

kwankwasa kofar takey tun tanayi ahankli har tafarayi da karfi yana gama waya da mum dinsa ya miƙe yaje ya bude mata kofa batare da ya kalleta ba ya dawo wajen zamansa ya zauna yanakan karasa saka takalminsa, satan kallonsa ta dingayi harta karaso ta gabansa ta dan rusuna ganin ya kara mata haske yay kyau suman kansa yay baki ya wanku haryana sheki musmn daya saka wata well ironed dark blue long sleeve shirt da beige trousers wani dan uban qamshin xerjof naxos na tashi ajikinsa kamr ka lashe shi..

ayaana tay kasa da kai cikin ladabi muryanta na fita ahankli tace "ina kwana? tun be amsa ba idonta ya ciko da wani irin ruwa muryanta na rawa rawa tace"sultana ne tace min kana kira na.. kallonta ya karayi shima ahankli snn yace toh saiki bari na amsa gaisuwar kafin ki cigaba da fadin abunda bantabayeki ba, dan shiru tay,

harya gama saka takalmin da wani irin tausayi a cikin kwayar idonsa ya kalle sunkuyayn kan nata ahnkli yace "ya jikinki? wani irin sanyin muryansa ne taji ya rtsata sosai adan sakalce tace masa "da sauki" yace "toh yay. kai tsaye ya mike tsaye ya jawo wani madaidacin akwati acikin set in nasa ya aje agabanta, snn ya kalleta yace "zaki iya tuna duk abunda nace miki jiya? kanta na kallon kasa tace ehh,kace kar nasake daukar abun da banawa ba.. hawaye suka kara ciko idonta har suna neman zubowa,..atake ya haɗe rai yace" shikuma kukan dakike min ynxu na miye ne? ke na taba dukanki ne ko nataba cinyeki? da sauri ta girgiza kanta yace "idan har naga hawayenki daya akasa zakiga abunda zan miki'..

sauri tay ta tsare wanda ya fara zubowar da hannunta

yana daga zaune yace "i dint call u here to scold you, zan jadadda miki, kisani duk sanda kika taba abunda banaki ba shine zaki jawo makanki cin mutunci da zagi ako ina ba lallai sai gidan nan ba. dan haka ki kama kanki banason fitina, ko shishhigi,, bana son yawan surutu, ko son karban aro, babu ruwanki da abunda bana ki ba kinaji na ko?.

duk wani abunda kikeso a duniyan nan kizo ki gayamin, inbe fi karfina ba zan siya maki, idan bana nan kuma ki koyi hakuri inna dawo kizo ki gayamin ko karfe nawa ne bazai gagareni ba..kinga baki da lafyar jiki, duk wnn son kukan dakikeyn kisan yadda zakiy dashi ya dena zuwa inba so kike kema ayi janaizar ki da wuri kmr na yar uwarki ba, duk wnn shirmen ma yakamata kina yawan kiyayewa sabida mahaifiyarki tanaso taga rayuwarki yayi kyau, inkika zauna cikin ciwo kinga wata rana sanadiyarki zatazo tana kuka ko kinasone tay kukan rasaki kema???

hawaye masu zafi suka kara cikowa cikin idon kanta akasa ta girgiza mai kai da sauri da kuma muryan kukan tace "a'a banaso. amma...amma yaushe ummanan zatazo?kai tsaye yace" nima bansani ba. "see,. just forget abt her. inbaki nitsu kindena yawan mana koke koken banza ba bazata taba zuwa ba! da yaranta ayanayinta sosai ta share hawayenta da sanyin jiki tace mashi toh ai zan dena kukan
..baice komi ba ya kalle akwatin snn ya kalleta suna hade ido yace "kayanki ne aciki. karki manta idan kinason wani abu come to me first. tace mishi toh..sai ta danyi shiru bayan ta gama goge fuskarta ta kallesa tace nagode..baice komi ya dau wallet dinsa ya ciro kudi five hundred naira sabbi ya bata guda goma aciki yace ki aje acikin kayanki, shima naki ne.
hajiya zata dawo nan da kwana uku zamu wuce can gidanmu inda zaki zauna tare da ammi kafin musan me zaay anan gaba dan haka ki zama cikin shirin tafiya. tashi muje kije ki gwada kayan..snn ki tabbata kin mayar ma sultana nata dakike sawa. cikin ladabi tare da girmawa takara ce mishi toh..nagode" tana mikewa yasa hannu yadauki akwatin dakansa suka fita tana binsa abaya har ya kai matashi har kofar dakin sultanan snn ya kyaleta awajen ya juyo abunsa.

kallon inda yabi ta dingayi tanajin matsayinsa da kimarsa na dada yawa aranta bata daga ido akansa ba kuwa har saida taga ya bace a sashn gabki daya..

kwankwasa kofar tay sau daya sultana ta fito jin yadda qamshin turaransa ya kama wajen tafara waige waige

kusan atare suka shigo da akwatin ciki tana tambayar ayana a ina kika samu wnn qamshin turaren ayaanah tace banawa bane nashi ne shine ya kawomin akwatin nan yace wai kayana ne aciki

baki bude sultana tace kina nufin yaa ibaad ne ya rakoki? wow...i am sure he bot this for u. .toh mu bude mana mugani.

daura akwatin sukay akan gadon, sultana ta koya mata yadda ake budewa suka fara ciro kayan daya bayan daya
hadaddun Plain black abaya
da coloured A-line gowns da wata Front-open abaya da Kaftan with matching hijab, Two-piece prayer dress, su Inner Wears ne dasu Cotton underscarf da sleping dress guda biyu, Soft cotton veil da camisoles, Comfortable cotton underwear, leggings, da Hijabs, designer Jersey hijabs, Chiffon hijabs Instant pull-on hijabs da takalma in Black flats, Modest sandal ,Sneakr, da Simple dress shoes sai Gentle body cream, Lip balm, da Mild deodorant harda dan safe sunscreen inta mekyau kusan komin ta in 2-3 pairs bai cika mata ba dan yasan dolene inta koma gabansu amminshi zasu saya mata kaya sosai
Chapter 68 · 0% Book details