← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 161

Sashe 8

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sosai anty raihanatu ta tsane anty fatiman har bata iya boyewa, kamar kishiyarta haka take kallonta duk dama tay nasarar hana bappa zaidu aurenta, sau da dama taso talaka mata sharrin zina dan kawai akoreta a ahalin sabida wann uban kishin datakeji aranta nacewa haryau idon bappa zaidu yana kan ammi karama shiyasa ma aka nace ta zauna agidan akan yaranta har saita samu mijin aure..

sanadiyar yar wann hatsaniyrsun yasaka aka raba musu gida, ammi karama (anty fatima) da yarta safiya suna zama ne a can family house inda uncle moh da matarsa anty safeera da yaransa biyu suke nan zaune acikin anguwar rijiyar zaki. sashenta daban nasu ma daban sai babban self-con asama shima anbari ne ma hajy maituwo sabida hutun weknds da zumunci da duka jikokinta.

shikuma ibaad yafi zama ne a karkashin bappa zaidu, tare da cousins dinsa maheer da kulthum, toh dake hajy me tuwon ma acan gidansa aketa tsammani zata zauna duba da yafi kusa da kasuwa, yasa gidansa yake da girma sosai dan yariga ya mata babban flat aciki ga kuma sabon motarta na zuwa shago daya gina mata a kasuwan anata jira dai ta dawo.

kusan al'adar gidan ne duk weknds kawai ake dan tarkartowa duka azo cikin family house dinsu na rijiyar zaki domin hutu da kuma karfafa ziyara da zumunci, uncle muhammad ne dama aka bari anan wanda shi ne autanta kuma civil engineer ne, kowani wknds shi yake amsar kowa da kowa cikin aminci da fara'a da tausayi he is deir young nd happy uncle moh, still thriving in his career sabida political connection da iyayen matarsa suke dashi yasaka yana samun kudi sosai shima ba lefi dan shi baida matsala ko kadan.

idan anzo family house na rijiyar zaki ne ibaad yake samun cikakken ganawa da mahaifyarsa ammi karama, ita kuma ammi babban ko da sunzo family house din tafison harka da matar uncle moh wato anty safeera duk dama ta girmeta sosai amma itadin tana da sisterly connection da hajy hamida shettima sabida anty safeerar yar masu kudi ne kowa yasan babanta ya taɓayin minister, infact da ita kawai hajy hamidar take magana a dangin miji, anty raihanatu kuma dama akwai dan uban maganadisun gulma da kwadayin abun duniya kullum dai tana mugun son taga tana raɓuwa dasu babban burinta baifi dataga anware ammi karama ba.

ya kasance awajene anty safeera zainab arifah take sauka inta sace jiki da driver tazo ziyarar itama, tun jikokin gidan alhaj almansur makarfi suna yan kanana ake gudanar da xumuncin ahaka adaddafe sama sama, full of hidden malices, and classism na ciki duk na ciki.

maheer da Ibaad sun shaku da junansu sosai, duk dama uwayensu mata basa jituwa amma sosai ake zumunci, maheer din ya bada ibaad like 2yrs gap dake ammi babban aka fara aurowa, snn ya kuma bawa mujaheed 4yrs dake shi mujaheed sa'ar zainab arifah ne,
wacce ko tazo gidan kwainanenta na sangarta kawai takeyi bata fiye son harka da su ba, kulthum da sultana kuma are all almost same age da safiya duk dama sun bata 2yrs dan a gidan safiya itace karama as of now batafi 10yrs ba.

duk da hadewar kan yaran, ammi babba haryau tulin kishi na dawainiya da ita haka kawai ta tsani ibaad har cikin kokon ranta, zama dashi kawai take agidanta na dole sabida batason ta saɓawa mijinta bappa zaidu, amma bata kaunarsa ko kadan, dan wani bin ko amsa gaisuwarsa baso takey ba gani take kawai kamar duk shirin aure mata miji ammi karamar take kanyi shiyasa ake kan cusa ibaad a zuciyar bappa zaidu haryake daukar nauyin komi na karatunsa tun daga primary gashi nan har scndry.

haka rayuwa yake tafiya a familyn alhj almansur na tsawon lkaci, prof zayyanu adan dole kawai ya hakura yabar yarsa zainaba arifah take shigowa dangi, kamar yadda ammi babba take zaman dole da ibaad anata gidan na GRA.

gabaki daya yaran gidan sun kasance mabanbanta hali, but one thing they all have in common is deir natural striking pure fulani beauty da albarkan ilmi me amsa sunansa ilmi.

babban cikinsu yaa maheer is faintly chokolate skinned, calm, and reserved kamardai babansa bappa zaidu, inkaga yana surutu to musun ball suke da ibaad, yana da kama kai,da sanin yakamata hakan yasa sukafi jituwa da ibaad din sosai dan baifiye son mutum me kananan magana ba, shikuma ibaad din mutum ne murdadde, a walking puzzle in human form,yana da piercing hazel eyes da dark pink lips, farinsa kuma is more like a ethiopean beauty, soo calm, yellowish skin tone ba irin dau innan ba, babu karya yafi uban kowa kyaun jiki da tsarin fuska tareda farinjinin yan mata sabida mum dinsa farar shuwa arab ce yake da suma baqi qirin, saidai kmr yadda hajy mairo take yawan faɗa ne, ba asan gaban ibaad ba bare bayansa, yana da mugun son tsafta, in yay dressing damnnn kamar italian model, saidai birkitaccen mood swings da wnn emotionless face din nasa yasa ake ganin kamar ma shine babba agidan sabida baiya wasa ko kadan da kannensa msmn ma mata, komin rikici da surutun da akey agidan yana shigowa zakaga an watse waje yay shiru, he is deeply introverted with a touch of hot temper, highly emotional intelligent, sosai ya iya karantar halin da mutane ke ciki shiyasa ba masa karya, akan ra'ayin kansa ya fiye zama. baida tsoro sam, amma kwata kwata baison hayaniya, duk duniya babu abinda yake mutuwarso aransa kamar murmushin mamansa, itace kawai intacemai yayi abu ko da baiyason abun to zakaga yayi atake,
mujaheed kuma shi fari ne sosai kamr yellown inyamuri, MJ sarkin tausayi ne yana da saurin kuka ga rauni, baida raayin kansa his dad alwys tell him wat to do, he is hopeless romantic at heart, snn yanason soyayya mai zurfi da ma'ana. sai dai daga zarar ya gane mace batayinsa toyakan hakura hargara yabar abun dayakejin ya kashe shi acikinsa.

duk wani hali da MJ yake dashi ajikinsa kusan shi zainab arifah shitake ji dashi, a kyau babu ta inda takasa, itama fara sol ce sol kamar mjn din tanada kuma manyan idanu da pink lips me kyau da yar doguwa fuskarta, kawai dai tana da dan girman jiki ne tun tana yar karama, da tun lokacin datake at arnd age 10 shatin fitowar nono already yafara bayyana mata sabida irin kulawar datake samu na wuce kima, tana da rauni, she is so soo vulnerable nd hopeless romantic at age 7 tafara wani irin silent crushing akan yanayin dressing in ibaad, abun yafara mata kamar wasa, saidai tsoronsa da ake mugunyi yasa bata iya nunawa ba then the more she sees him the more obsess she bcm with him, hardai takai 12 yrs shikadai ne namiji aranta duk dama ko kusa dashi basa iya zuwa tsabar tsoronsa da sukeji.

inda kawai suka dan bambanta da mj shine inhar tana son abu koda abun bayasonta bata iya haqura dashi saidai a mutu. yar a mutu a love ce, bata san meye babu ba, bata san meye kalmar hakuri ba, she believe duk abun da zuciyarta yakeso kawai xata sameshi. sultana da kulthum kowacce tana kama ne zak zak da mahaifyarta, safiya ce kawai take kama da mahaifinta sosai, nd each of them are so beautiful in their own ways. saida zainab takai har 13 kafin ta fara nuna alamomi a fili cewa ibaad yana ranta sosai. kullum akazo wekdns inbata gansa ba bata sake fuska da kowa, ya zama kamar ganinsa shine kawai abunda yake kawota gidan.

wa Ammi babba hakan ya farayiwa zafi dan ta tsanesa sosai, toh amma sunsan zainab arifah yar gata ce na bugawa a jarida basu isa su fara juya brain inta ixuwa hana yuwar komi ba duk dama sunga aboye take zuba crushing inta akn ibaad sabida yadda taga ake mugun tsoron masa shirme. tun da zainab takai jss 1 ta dada fallewa da jiji dakai snn tagamu da kawaye irinta sangartattu yayan masu kudi"Nala, da rukky, haka zasu zugata tayi wann tay wancan domin ibaad, amma bai taba kulata ba dan ya tsane yadda ake nuna mata fifiko tare da sangartata agidan, nd worst part ma yadda take xuba ma uban kowa fi'ili da manyance ana kyaleta dan ba ason ran ubanta ya ɓaci, tun tana wannan kananan shekarun tafara koyan kwalliya da saka matsatsun kaya wai dan kawai ibaad yayi noticing inta amma inaa shi mugun haushi ma take bashi aransa.

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[23/10, 18:55] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: _ABUNDA KE 'BOYE...._
_Love And scandal💕_
*_Arewabooks@surayyahms_*

⏯️5️⃣lamarin boyayyr soyayya me zafi da zainab Arifah take kumsawa aranta akan ibaad yakan daure ma kowa kai musmn dake ita da kanta ɓoyewa takey sai ya zamana kowa yana dan dauke idonsa akan wasu abubuwan datakeyi, kafin takacika 14yrs duk matayen familyn al-mansur saida suka san da wannan ciwon obsession datakema ibaad wanda ynxu yafi karfin ace masa tsaftacyar soyayya dan wani bin inbata gansa ba iskar datake busan numfashi dashi kamar dauke mata yake a makwogoro, haka ma duk ran da akace tazo gidan ta gaishesa yahade rai ya wuceta be amsata ba haka zatayta kuka da tsananin fushi kamar me fama da aljanu a dakin anty safeera, wani bin har kaga tana zazzabi me tsananin zafi, haka ma inta koma gidansu xata kulle kanta a dakinta tay ta rabza kuka kmr an bugeta tanajan zuciya wai dan ibaad bai amsa gaisuwarta ranan ba,

gabadaya sai ta Ɗaga ma kowa hankalinsa agidansun, saidai duk rintsi duk wuya bazata taɓa iya furta ma kowa cewa ibaad ne matsalarta ba, kuma shine take mutuwar so aranta a fili ba, yanxu haka iya kawayenta na schl ne kawai suka san asalin meyake damunta aranta..
Chapter 8 · 0% Book details