← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 161

Sashe 20

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ibaad ya dago kansa ahnkli suka haɗe ido fuskansa adan daƙile yace mishi "she is alive. prof yay dan kwafa a shashance "tou hakan yay dai-dai alhamdullh tunda kuna da wacce zatana ciyar daku kai tashi muje ciki nagaji da wann surutun..ibaad yay shiru kamar baiji shi ba, har saida prof din yamiƙe yafara tafiya snn ibaad din ya mike tsaye shima yafara binsa abaya,

wani katafaren hallway suka ratsa, acikin izza prof yake tafiyarsa yana lallatsa wayarsa kai daga ganinsa kasan ba har cikin ransa yake son wnn yanayin ba, shidai kwata kwata baison yan uwansa na jini suna raɓar gidansa bare arzkinsa wnn karon ma babu yadda ya iya ne rayuwar yarsa tafi mai komi muhimmnci a yanzu

suna shigowa wani katon white hall mai tattare da babban dining area sai ga nan matarsa hajy hamidan tabude wani babban kofa ta fito amugun mugun kasaitance wani irin kwalliya tayi tamkar ɗawisu qamshin hadadden turarenta tuni ya bule wajen da qamshinsa, tana taku dai dai kmar bazata taka kasa ba, tasaka wani ubansun boubou na original shadda lace royal blue colour wuyanta da hannunta sunci uban su da gwalagwalai.

suna hade ido da ibaad ta tsaya turus tanata kallon yaron cikin fallasashen ruɗewa dan acikin ranta batay tsammnin wai harya girma ya ƙara kyau haka ba, tasan dai zainab arifah tana yawan zuzuta kyansa ita a mind inta she expects to see notin but a hungry local boy with no social class, dan rabonta da ganin fuskarsa tun ahoton haihuwarsa datagani awayar anty safeera.

cikin neman wakanta nitsuwa tay gyaran murya me aji tabi ta tsime batako musu sallama ba dake taga mijintan nakan amsa call kai tsaye ta shigo cikin dauke kai tayi kamr batagan ibaad a tsaye ba.

tana zama akan chair ibaad ya daga ido ya kalleta daga tsayen yace"ina wuni ? ranta a harde ta masa wani irin kallon sama da kasa me shaqe da rainin wayo muryanta ciki ciki tace "lafiya. snn ta dauke kai tay banza dashi, shima sai bai kara kallonta ba, shiru ne ya ratsa tsakaninsu dan wani mugun haushin yaron ne ya riketa kamr zai fasa mata kirji irin feeling feeling dinnan najin anrainata dake ta riga ta saba ana yawan mata fadanci ko mutum ya girmeta zakaga yana rusuna mata kai kasa sabida matsayi da dumbin ikonsu, yadda tagama raina ma labarin kyan ibaad wayo sai kuma tazo taga ya ashe ma wuce yadda take tsammani tun daga siffarsa har izuwa kan dressing insa me mugun dauke ido da uwa uba yadda dadin turarensa me aji ya kusa danne nata me matukar tsada.

shi mutum ne wanda iya tsaftarsa ne zai soma dauke maka hankali, he always look so smart nd very neat, shi baya son tula kayan sawa ajikinshi amma kuma sutura me bala'in aji yake yawan sawa.

prof ya gama wayarsa kenan ya kallesu duka ganin kowa ya dauke kai sai yay gyaran murya yace hajiya hamida wann fa shi ne dan gidan marigayi babban yayana late dr almustapha almansur.

cikin rolling ido ta juyo tanamaiyin kamar tuntuni bata ganesa ba, da wani irin yaken makirci tace ohhhhh ayya, Allah sarki ashe dan marigayi ne, gashi kuwa ya girma da kamannin mahaifinsa, gosh jishi duk ya zama abun tausayi toh Allah dai ya jikan babankan, ran ibaad yafara baci bt still ya kwantar da hanklinsa yace Amin. ido ta zuba masa ta kara kallonsa ita dai gaba ki daya ji tay kmr taƙi jinin yaron dan daga ganinsa tasan zaiyi girman kai yadda taga ya hade ransa baya ko murmushi, saida ta gama kare masa tanaɗi aranta sann tace Alhaji sai ku karasa dinning din i am sure we are all famished.. prof yace aa hajiya kinsan ni bawani son cin abnci da yamma nakeyi ba amma dai tou bakomi muje dai zan taɓa.

tay murmushi yawwa my darling ai kuwa dazance kar kayi haka

ta kalli ibaad da rainin wayo a kwayar idonta cikin rage murya kasa kasa inda tasan ibaad din zaiji tace "ohh ni hamida dama haka yaron yake abun tausayi, alhaj ya naga duk yunwa ne ajikinsa kasan me? kuje kawai kan dinning din zan sameku acan i need to check on our princess,

prof baice komi ba ya gyada mata kai tana barin wajen ya kalle ibaad wanda already zuciyar yarinta na raya masa akan kawai yaqi cin abincin ya tafi sai kuma yay wni tunanin kawai sai ya danne zcyrsa yabishi suka zauna akan dinning table din kusan atare.

nan ma shiru ne ya ratsa tsakaninsu har saida hajya hamidan ta dawo ganin ita daya ta fito babu zainab arifah yasaka tun bata zauna ba prof ya fara tambayatta inq yarsan take, fuska ba yabo ba fallasa tace "alhaj ka kwantar da hankalinka she is coming kasan dai yarkan sarauniya ce mai son kwalliya da tsafta, so she will be here in few minutes dai tacemin, cikin jin dadin hakan yace its awryt let her take her time she will alwys be the prize, atare sukayi dariya. shide ibaad baice musu uffan ba,

daga kan long luxurious table din ido kawai bazai iya kirga abincin da ake jera masa agabansa duk dan a nunasa nasa bambamcinsa da su.

abincin gargjiya har tuwon biski ta saka anyi wai a tunaninta ko yaron baisaba cin na yan gayu irrinasu ba, itafa komin arzikn ka inhar ajinku ba daya bane to A talaka kawai take kallonka.

sunfi 10min suna zaune ba ataɓa komi na abincin ba sabida suna jiran yarsu yar gata zainab arifa ta gama duk abunda takey snn ta karaso.

hirar business suka faray sama sama tsakaninsu ganin ibaad bamai son magana ba yasaka basuma tsomasa aciki ba.

after like 10 more mins tahowa zainab Arifah takeyi akan golden steps cikin shan qamshi tana taku kamar bazatay ba domin itakanta qamshin turaren data fetsa ajikin nata tsabar yawansu da karfin qamshinsu ji take kmr suna bugar da ita, daya bayan daya take dora kafafuwanta akan step, cikin tattalin kai
can saiga ta bullo ta wajen inda suke wanda tundaga sama ta zubawa ibaad dake zaune akan luxurious dining table din da aka kawatashi da ababen tabawa ido tanajin kamar mafarki takeyi, wani irin sabuwar farinciki takeji mai yawa na mamayarta har kwakwalwa data gansa.

Kasaitaccen sautin takunta shi yadan janyo hanklin iyayen nata bisa gareta dan tay masifar kyaune na kure hankli saide duk gigin zumudintan nan kuwa bata wani tula kayar tashin hankli ajikinta ba, doguwar riga slay queens gown styles marar hayaniya sosai tasaka ajikinta na babban atamfa original engila red colour snn ta cakkara dauri tare da zubo da sumarta kafadunta, cos at this young age already ta fara saka irinsu nails da curtex da gashin doki duk dama babu laefi itama din tana da dogon suma., cikin nitsuwa ta sauko cos she rmbers clearly cewa babanta yace mata kar tay rawan kai agaban ibaad, dan haka tay balain kkri wajen danne abubuwa dayawa na zumudin ganinsa dake yawo cikin ranta da zucyarta.

faduwa gabanta ya dingay har ta iso tana satar kallonsa, iyayen atake suka hau yaba kyanta kamar yadda suka saba, itakuma tana fmr shagwabe musu fuska, ibaad yadago kai kenan suka hade ido da ita, gabanta ne ya mugun fadi saikuma taji takasa motsi tabi takafe shi da kallo mai sanyi kamar bata taba ganin kyakkawa irinsa a duniya ba.

ganin ya dauke kansa a kallo daya yasaka itama ta dauke kantan ahnkli cos she was lost in her tots for a moment dan batama jin me iyayen nata suke cewa kawai satar kallonsa ta dingayi harta karaso gefen baban nata ta nanike ata gefensa yarike mata hannu cikin tsantsan nuna mata soyayya da gata a fili, a shagwabe ta zauna daf dashi batace ma iyayenta uffan ba, tay cunen baki tanajin kanta a matsayin yar gata sangartacciya kuma ƴa guda awajen iyayentan wanda tasan zasu iyayin komi akanta a duniyan nan, yau yadda kasan danyen tuwo haka take narkewa jikin babanta. Tun data nemi waje tazauna acikin yanayin shagwaba batace uffan ba bare tay gaisuwa daga ta turo musu baki, sai tay rau da idanunta cikin tsinannen rigima.

hanklin ibaad gabaki daya baikansu jin yadda iyayen suka fara jajayya da ita wajen gaisuwa dan tun safe bata gaishe da iyayen nata ba.

yau sosai yakara lura da cewa zainab arifah din sangartacciya na kure hankali da tunani kalar wanda tsarin rayuwar banza ya riga yashige musu jikinsu sosai.

da kyar dai suka sakata tay gaisuwar harta gaishesa ya amsa atakaice kafin nan baban nata dakan sa ya bada oda masu aikin gidan dake akansu suka fara aikin serving dinsu abinci wanda gabaki daya wajen ya gamutsu da wani irin qamshi me shegen dadi ga nan dadadan aroma na garnished soups da gasashun namar kaji.

sama sama ake hira akan table din..shide ibaad sam ya kasa fahimtar kalar rainin wayo irin tasu cos all this traditional food tagabansa kawai ake tarawa hakama idan za'a samai abu a plate dinsa sai ancika plate din kamar sun ga mayunwaci ko mabaraci. shide tun da ya rike spoon yana jujjiya wa bai isa yace yayi loma yakai uku ma abincin ba..

prof ne yake magana time time yana kushe kokari, ilimi, da arzikin kowa cikin familyn su al-mansur, at same time yana dan sako labarin mahaifin ibaad din dake duk zuria shine kawai bai taɓa yin zuciya dashi ko ya rokesa kudi, ko wani taimako ba. hasalima badon shegen son zumunci irinna mahaifin ibaad ba da tuni prof ya raba kansa da zuriarsa sabida bappa zaidu da uncle moh sai suyi shekara fiye da hudu ma basu kulashi ba.

shi bawani cin abincin yqke ba kallon ibaad kawai yake yana cewa..."babanka mutum ne mai mutunci duk zuria shine kawai be taɓa nunamin baqin cikinsa ba,shi yasa nake jin kamar ba zaidace mubari zumuncin daya kulla da gidan nan ya yanke gaba ɗaya..

duk da prof baison zumuni bt he try to pursuade ibaad dan yaji aransa cewa zai iya amsarsa agidansa a mtsayin ɗa kodan albarkacin mutuncin mahaifinsa.
Chapter 20 · 0% Book details