← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 161

Sashe 103

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ko sultana da ta fara saurayi kusan a boye take chat kawai sukeyi, His name is ahmed waziri dan gidan sarauta ne a kanon kamr mamnsa itace first wife na wani tsoho sarkin kano da ya rasu da jimawa. tunda suka hadu da sultana a school yazo daukar jnr sistrnsa yabi ya makalkale mata sosai itakuma bakaramin tsoron yayunta su kamata tana hulda da namiji da sunan soyayya takeji ba.

dagata fannin ayaana kuwa dan subucewar tazarar kulawa da uncle moh yay creating na karfi da yaji tsakaninta da ibaad yasa along the years ta samu dama daga wajen hajy mairo duk ranar da bata da islamiya ko lesson takanje shagon hjiya ta samu ruthy wacce ta gama buduwa tay katuwa kamar ba age mate dinsu sultana ba.

ayaanah intaje bata saida abinci dan tasan ibaad ya jima da hanata amma sosai take tursasa kanta tana koyan abubuwa da ake musu acikin catering school din musmmn da professionals aka kawo wajen suna koyarwa, gashi ruthy tazo ta gamu da mazan kano tawani irin bude ido ta zama yar gayu sosai, ita kanta ayaana mamakinta take sha, most of the time ita dayanta take zuwa shagon ta dan jima tare da ruthyn tanamai koyon wasu dabarun girki na zamani dana gargajiya sabida su kulthum sunakan shirin su waec da su jamb dinsu, gashi ko first term ba'ayi ba tukuna.

yanxu haka ss1 ayaana ta shiga ta zama big girl now amma Girma yazo mata da kalubale kala kala sabida wann matsanancin slim shady coca kola shape din da jikanta ya fitar dashi, yakasance kamr ita ta jera halittar jikinta dede wa deda,nononta da suka tashi fitowa so full nd round, hips dinta yadan baje dakyau yabata perfect curvy model shape, kyanta ya kara bayyanna sosai dake tana balain samun kulawa. ..

wani irin silent soyayya mujaheed yake nuna mata wanda haryau bata dago ba, haka a wasa wasa zata ga zai tura mata morning nd evening tex kuma ta amsashi itama duk da tunanin cewa sabon da sukayi da kirkinsa ne kawai yayi yawa ba komi ba.

hakama duk takuri da shige shige da wahalan saye sayen kayan duniya da unclle moh yadage yake kan mata Allah baisa ta dago meyake nufi da ita ba, itade tasan duk gidan babu wanda yakaishi bata kudi da kashe mata kudi..daukawa tay Haka Allah yay shi da son kyauta. hatta wayar da ibaad dinma ya siya mata yanxu kusan sau biyu kenan yana canza mata da latest iphones ynxu haka dai kowa dai ya zuba masa ido ne ba acemai komi...ko ibaad ma saidai ya kalla abun ya dauke idonsa duk dama haryau komi ayaanah zatay arayuwanta sai tazo ta tambayeshi shide kawai harkan uncle moh ne baya sake ya shiga dan ynxu ko ya gaishesa da kyar yake amsashi..

wani boyayyar haushi uncle moh yake fama dashi, dan ya jima yana lura da yadda ayaanah take bala'in daraja interest in ibaad at heart..

Zata ki sam tazo jikinsa amma bai taba ganin taji kwuiyar ko kunyar yima ibaad wani abu ba

sabida schl da business na Q4 yasaka ibaad bai samun time na kowa amma duk abunda yakeso sai yaga shi kawai ayaana take koya, duk wani fav food dinsa ta san recipe dinsa awajen ammi karama, nd she love to be the one to take food to him inyazo koda bazaici ba zata kai masa har daki, dan zcyarta yana cikene da uban damuwar canzawar dataga yayi ayan shekarun nan musammn bayan matsalar su da uncle mohd sai bata gane komi ba.

saita rike cewa lallai hala zainab arifah ce take dauke masa hankali tunda tasan ana ma zainab islamiya a gida
...hakan kuma take rayuwarta da wann tulin fargaban ta dora ma zuciyarta akab zainab arifah.

girma da gogewa yasa zainab Arifah din ta zanca itama, inzatazo gidan wani irin kure adakar wanka takeyi, musmn ma da ynxu ta gama secndry schll ita dinta next week kuma ake shiri zaa musu grand ceremony snn nan da sati uku zata bar kasan nan.

ayanah na makale da murnan zainab zata bar kasan ta kyale mata yayanta, batasan itama zainab arifah din itama adame take da rashin samun kan ibaad da takey arayuwarta kwana biyun na ba.

dukan su they are woried abt canzawarsa amma kuma kowa yana zargin kowa batare da sannin su ba shikuma yana can baima san sunayi ba dan daga harkan schll dinsa sai business dinsa daya sako agaba musmn ma da yanzu suka dawo sun shaku da su jamal sosai...

business dinsu da suka fara tun a watanninsa na biyar suka fara samun agro revenue amma dukansu basu taba ba, awatan su na tara suka fara small cold chain distrubution shi dake a dubai ne jamal ne yake dubawa sosai nd all the land da suka siya sunyi securing, kusan komi dai ya tsaya da kafarsa saura kawai yay karfi.

1rs year suka fara samun return na kudadensu they make 39million naira each cos of the transction na cold chain in dollars yake zuwa musu, sunay suna reinvsting har saida suka bude rep. office a dinsu a dubai, snn suka fara karban monthly flow divisions kowani wata kowa kudi yana shiga acct dinsa ...

uncle moh da harka ya buda masa sosai yakan siya ma ayaanah abubuwa nagani ma fada, haryau shine gadgets,
jeweries ne,kudi ne duk zai bata.. amma haryau baisan cewa ibaad ne ke siya mata duk wani abunda take amfani dashi me matukar muhimmci a matsayinta na ya mace ba, ryt skin nd hair cares, sanitary pad, inner wears, da school items komi shiyake siya mata ammi karama kuma suke saya mata kayan sawa da duk wani abu daya shafi zaman gida most time kuma bappa zaidu ne ke biyan mata kudin makaranta ita da sultana gabaki daya atare, bacin nan duk wani kananan abubuwa ibaad ne yake mata quietly snn yay guiding inta.

Dagata bangaren zainab Arifah kuwa wani irin grand shiri ake yi na graduation event dinsu dake tsarukan su ba iri daya bane dana sauran makarantu, dan sungama makarantar da kusan watanni kenan har result dinsu duka sunfito amma yanxu ne ake shirin musu gagarumin graduation ceremony

saboda kebetaccn makarantar masu shi ne sai sunyi shiri sosai sunyi gayyatan manyan
mutane both daga cikin gida dana waje..

Bisaga labarin fitowar result, is no longer a news a gari cewa Zainab Arifah is the e best ever graduating student of her set, asalin madarar guruwa ce by karfi da naci, duk dama gidansu sunyi gadon ilimin amma kokarin da zainab tay a karatu ya samu nasaba ne da yadda take mutuwar son taga ta faranta mahaifinta ransa ta dorasa a wani babban matsayin da dolensa ne ya alfahari da ita

tunda aka san cewa result dinta sunyi kyau wokers din gidan su basu kara samin duwawun zama ba

her pink yar gata graduation dress har kasar MILAN akaje wajen wani designer dinkawa, the whole week was spent on shoping, satin da za'a shiga na spa ne dan haka ta katse komi tun anan aka sallame malamin islamiyarta aka cemai aikinsa ya kare kenan dan ana yin graduation partyn kominta is ready zata wuce karatunta a kasar waje. yadda kasan aure zatay haka suka dau abunda zafi, amata wann, amaya wancan.

a week din spa din nata ne Ibaad yasamu wata urgent call daga wajen mahaifiyar jamal moriki

wani lamari dayazo musu da babban abun mamaki, duk dama suna sane da cewa a satin nan jamal was supose to celebrate his birthday In the U S, sai kuma katin marriage engagement dinsa yazo musu abazata..he is going to be engaged to his childhood sweethrt dinsa mufeeda Bilal yar gidan babban lawyer na babansa dayay musu fighting har suka samu arxikinsu da komi nasu ahannu. His pained gold digger uncles suna kan pushing narritve din cewa jamal har yanxu karamin yaro ne bazai iya running babban kamfanoni ba wasu abubuwan sunaso ne lallai abasu karfi da yaji dan su kwace arzikiin yaron nan., the judge advice them to get him married, cos in the state samunka da stable relshp ko aure yana iya hana wasu kananan premature legal actions yayi aiki akan namiji ko mace and this was the only way for jamal. dan haka atake atake aka shirya aurensa da mufeeda bilal cikin satin nan.

farhan dake sydney shiya fara isa, kafin nan su ibaad da prince hassan suka zo daga nigeria. kwana uku sukayi a U.S aka yi auren jamal kamar da wasa biki yay dadi sosai, it was in a very private nd luxurious way kuma dama can suna son juna sai akay small lovers event acikin private yatch.

bayan sungama supporting abokinsu to the fullest, washe gari suka dawo gida kamr ba ayi ba, kusan jakan designer guda suka dawo dashi na wedding souveniers shi ko bude nasa ma baiyi ya bawa amminshi duka kyauta baisan ma ma waye ta raba ba.

duk yadda ake shirin hidiman graduation din zainab arifa ko kadan bai dara ayaana ba, ta dai ga su kulthum sunyi spa, sun gyara gashi an zabe special kaya..ita da kuma dake Allah Allah ma take zainab din ta bar kasar nan ta kyale mata ibaad sai abun baiwani darata ba.

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[03/12, 17:20] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫
arewabooks@surayyahm.

⏯️3️⃣5️⃣
Graduation day:
Wayewar gari ce mai sanyi iska tana kadawa ahankali kamar ana masa umarni ya nutsu yaurana kokadan bata fito ba tukuna amma dakin Zainab Arifah ya riga yayi wani irin haske da grandier decorations tareda tsadadn fitilu da kyawawan akwatunan kyautuka da aka jera mata a dakin tun jiya da daddare ayayinda take bacci batama sani ba.White nd gold boxes, ga manyan bouquets ga su sabbin bags, heels, sets na jewelries,har ma da wani babban frame da aka rubuta OUR PRIDE, OUR STAR. Congratulations on your Graduation zainab Arifah al-mansur.”Duk dakin ya dauka da sheƙi kamar gift room na royal palace.
Chapter 103 · 0% Book details