← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 161

Sashe 77

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

itade sultana ta jima da lura da yadda ayaanah take saukin gane kowani irin turanci in anmata duk dama bata taɓa amsawa ba amma tajima da lura kmr tanajin turanci sosai. su hudunsu suka zauna a shashen ammi karama tun ana jimamin kukan mutuwar inaayah har aka dawo hirar sabon shagon abinci, tun anan ruthy tafara ma ayaanah tayi akan itama ta dage kawai tana zuwa restaurant in hajiya mairo dansu na koyan abinci kala kala atare tunda wannan restaurant din na birni ne, kuma na yan gayu, snn za'a kawo smart profesionl chefs da food servers zasuzo suna musu marketing kuma suna dafa abincin zamani da zaa na sayarwa wa masu kudi sosaiz duk wani shirye shiryen upgrade da ake shirinyi ma restaurant din duk ruthy ta gaggaya musu komi na yan gayu za'ayi, can hardai abun yafara bawa ayaanah sha'awa saidai batace mata eh ko aa ba sabida tana tsoro batasan ko ibaad zaizo ya bari tana zuwa ba.

daga dayan bangaren kuwa wani sabuwar hira akan bude tsakanin hajiya mairo da surukanantan tare da hajiya hajara acikinsu tanakan basu labarin halin data shiga da yan kidnapping acan tudu kusan kowa yana mata jaje saidai na ciki na ciki.. domin kuwa sauran matan duk basu wani jin dadin yadda hajiya mairo takeyima fatima kallo kmr yar cikinta na asali ba a amtsayin surkuwa ba,wanda kusan duk tafi maida hankli kanta acikin hirar

...gajiya da jin hirar kauyen ammi babba tay maza maza ta miƙe tayi excusing dinsu taje can can waje tafara bada workers dinsu sabbin oda akan su fara shirya kayan da zasu bukata na abincin dare dan harda baƙin suma za'a kai musu nasu da wuri tunda yau sukazo.

bada son ranta ba tafito amma sai taji hakan ya fi mata, gara tay aikinta na babban mace acikin surukunayen gidan data zauna tanaji ko tana kallo ana fifita fatima agaban idanunta.

anty safeera kam sam taki ta tashi acikinsu saima kara sakewa datayi ana hiran da ita, dan dama ita batason kayan takura musmn ma ana aikin gida kuma duk tsiya itama so take taga ta samu wnn karbuwa sosai awajen hjy mairo kodama wata rana zata samu matsayi irinna ammi karama agidan itama. duk bata da shkru sosai amma sosai tafi ammi babban nisan tunani da wayo, mostly takanji qishi da hassada akan ammi karama amma ko kadan bata nunawa bare zafafawa, she still respect her nd she look up to her secretly dan ganin itama takoyi hali me kyau na kama zuciyar yan gidan gaba daya shiyasa ta zamo neutral bata gaba a fili da kowa.

ibaad da bappa zaidu basu shigo ciki ba har su maheer da uncle moh suka dawo akay sallahn azhr atare.

bayan sun idar ne maheer ya fita zaikoma cikin gida sede ganin safiya dayayi tanata leke leken ibaad kamr jelɓe yasa ya kirata tana zuwa ya masifeta akan taje tay sallan snn ta kira masa kulthum yanxun nan

da sauri ta koma ciki aikuwa tana zuwa sashen datagansu su hudu sunata hira wani irin tsaki taja ta hade rai tawuce dakinta dan taje tay alwala, haka tay sallah batace musu uffan ba suma basu ce mata ba nan suma suka tashi sukai alwala a extra room sukay sallahnsu sun idar kenan safiyan tazo tace ma kulthum cewa yaa maheer yana kiranta awaje..

tun kafin kulthum ta amsata tafita waje da sauri ta kara lekawa can kuwa ta hango ibaad yana fitowa daga masallaci da waya a hannunsa kamr zaije ta bakin gate, da wani irin gudu ta dawo gidan taje sashen anty safeera har tana haqi tana isa tace "anty zainab arifah ganan yaa ibaad yana waje kiyi sauri kije naga kamar waje zai fita.."Katse wayar zainab arifah tay tace "safiya kiyi sauri kije kice masa ya tsaya gani nan zuwa abayan ki..wani kifi kifi da ido safiyan tay tajuya tana takawa ahankli dan tasan har abada bazata iya xuwa tace ma ibaad ya tsaya ba dan tasan jininsu baiwani gama haduwa ba tukuna zai iya falla mata mari yace mata magulmaciya..

ahnkli ta dinga tafiya har zainab arifah ta gama shafe shafenta ta dauko gifts bags din tafito ta wuceta ta fita can waje, tana lekawa kuwa idonta ya sauka caraf akan maheer acan gefe yana zaune akan chair kulthum tana nanike ata gefensa ta dan tsuguna kusa daf dashi sunata magana ahankali kmr saurayi da budurwa.

tsabar son taji gulma da sauri tay ta wajensu ta kasa kunne har sanda taji kamar they are actually talking about yadda zai taimaketa tay catching up da wuri a tajweed na qur'anic competition na islamiyarta da aka sata kwanan nan tukunna ta kara sauri tay gaba.

samu tay ibaad ya jingunu da jikin motarsu yanata latsa wayarsa da alamar chating yakeyi, tana isowa caraf tazo zata leka cikin wayar batare da ya daga ba ya mata wani irin mugun kallon da saida kirjinta ya tsaya cak taja tatsaya tana kallonsa, kallo daya yamata ya kuma dauke kansa ya mayar kan wayan, budan baki tay zata masa magana cikin datsar numfashin ta yace ke wai baki sallama ne?? ta dan turo bako tace "my bad, asallam alaikum
..saida yaja mata aji snn cikin hade rai ya amsata ciki ciki

..cikin sauke ajiyan zuciya ta rage murya tace"can i talk to u for a min? idonsa nakan wayan yace "ure already talking, so? cikin wata yangatacen rolling eyes tace "i bot u some gift ne sabida ranar naga kamar ranka ya baci da wanda na siya ma sister dinka, naga kuma kamr kyauta ma kayi dasu ko? kmr bazai amsa ba can kasar wuyarsa yace is dat all?shiru tay sounding abit off tace "no. inaso ne ka karba, ..ibaad, pls accept this one cos i am sure zaka so shi. batare da ya kalla komi takeso ya karban ba yace 'thanks" batace komi ta mika masa dakyar ya karba kai tsaye ya aje akan motar baiko kalla meye ne ba..

cikin hadiyat zuciya tace daddy yace he will talk to u abt you home schooling me na karatun islamiya...has he? yace 'nop" ahnkli tace..okay, i just want to know if ure okay with it bana son na takura maka, dama daddyna ne yace kaiine kawai zaka iya koyamin addini agida and kawaye na sunce..tun bata karasa kalaman ba wayarsa ya fara kara kai tsaye ya dauka yakai kunnensa yay sallama anitse

mujaheed ne ya kirasa yanakan rokansa akan yazo ya daukesa a airport sun riga sun sauka..yana amsashi da toh ya katse wayar yamata kallo daya yace "are u done cos i am heading out now".ranta baiso ba ahnkli tace ohh to where can i come with yoi? kmr bazai amsa ba yace "airpot, nd no thanks...cikin kyabe baki dan yangace tace its okay, toh zan jira kawai sai inka dawo zamu karasa srn maganan...baice komi ba yana bude motar ta matsa gefe tanata kallonsa har ya zauna zai kulle kenan snn tay sauri ta dau gift bag din ta saka masa akan seat din gaba snn ta kama hanya ta wuce cikin gida...

baiko kalle inda tay ba ya dauki wayarsa yanata so yakira maheer dan suje tare saidai ganinsa da kulthum dayay acan gefe suna magana sai ya fasa, ya kunna motar ya tafi shidayansa abunsa..

sai har da yay nisa a hanyar aiport snn yay ma maheer din text akan idan yagama ya samesa acan minjibir along gezawa road cikin PortoGolf Resort bayan asr prayer.
maheer bai ma ga text dinba sai har daya gama hirarsa da kulthum aka fito daga sallan asr snn ya gani. zai karbi key din babansa kenan yaji bappa zaidu suna hira uncle moh

he is obessed nd still on ayaanahs matter, casually yake gaya ma bappa zaidu cewa ai ayaanah tamkr iri ce, da irinta kuma ake gyaran zuria shiyasa bai kamata su aurar da ita wana waje ba. shide bappa zaidu bai cewa komi ba dake kele kelen duniya ba'a agabansa yake ba.

shikansa yasan ayaanaah is exceptionally beautiful amma baida raa'ayin dole a tursasa wani yaro ko yarinya agidan ace dole yay auren dangi ko hadin gida sai kwata kwata bai dau maganan uncle moh din da muhimmanci ba.

dama kuma yasan halin kaninsa, shi dan boko ne wayewan ta masa yawa akansa, rayuwar turawan nan na yin abu anyhow yasaka agaba.. he is more obsessd with materials things, kai ko anty safeeran ma ya aurota ne sabida big girl slay queen life inta, da kuma arxikin gidansu, da farin fata da kyanta me yawan daukar idanu. uncle moh har ya gama zubansa akan ayaanah bappa zaidu bai basa wani kakkawaran amsa ba, har maheer yazo ya amshi key ya bi bayan ibaad.

yana zuwa resot din kuwa ya samesa tare da mujaheed suna zaune har sunyi odern burger da lemonade da alaman basu jima da dawowa daga airpot ba, da dan murmushi ya miƙa ma mujaheed din hannu suka gaisa snn ya tambaye ibaad akan meyasa basu wuce gida MJ din ya huta acan ba, shikuma dama delibratry yay convincing mujaheed harda bashi kyautar gift bag da zainab arifahn ta basa ko budewa yaga meye aciki baiyi ba dan kawai su zo nan suhuta sabida ko kadan baison ya koma gidan ya sake gamuwa da zainab arifah cos she is seriously annoying him

da sukaga kamr baza su wani ganema bayanin sa ba shine kawai maheer ya jonasu suka xauna anan suka fara hiran games din da mujaheed yaje south africa sukayi MJ yanata nuna musu hotuna da videos awayansa can da suka gaji suka shiga sashen da akwai pools da snooker games acikin resort din, anan suka balain bata lokacinsu har saida aka kisa kiran magrib ya tabbata by now zainab arifah ta wuce gida snn yafara matsa musu akan su dawo gida.

suna isowa kuwa aka kira sallahn, dede lokcin su hajiya mairo da anty safeera da ammi karama sun rako hajiya hajara da ruthy waje kenn har ansako musu abincin daren a cooler suma sun wuce gida kenan..
Chapter 77 · 0% Book details