← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 161

Sashe 107

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dakyar ta cire batun hoton aranta ta dukufa shirin zuwa karatu duk wani abu na yar gata an mata har saida ya rage kwana biyu kafin ta wuce snn tazo gidan ta musu sallama, kowa a shashensa. anan ta nace musu wai saidai ayaanah ta karbi wayarta ta mata hoto
ita da ibaad, ayaana kuwa ta karba ta musu pictures guda biyu, zama tay awajen tana editing din hoto dan ya kara kyau bayan ta gama ganin ita daya ne anan ta miƙe kai tsaye ta shiga room dinsa bataga kowa aciki ba har da zata juya kuwa sai caraf taga hotona guda uku half opened acikin envelope akan table dinsa da sauri ta bude taga the same pictures ne nashi da ayaanah data yayyaga sune anan batama san ya akayi ya samu copies dinsu ba..

kirjinta atake ya fara mata zafi tay sauri ta fara cusa su a envelope din da alama zata dauke taje ta konasu agida har tagama tattarawa zata saka a jaka kenan taji mutum akanta tana dagowa taga ayaana ta kura mata ido fuskarta ba asake ba tace "anty zainab in kin gama gani kibani yayana ne yace inkawo masa pictures din zai tafi dashi gida kuma sauri yakeyi...

ranta bai so ba ta miƙa mata..
ayaana ta bude hotonan tana kalla agaban zainab arifah tana murmushi basuce ma juna uffan ba, har ayana ta gama ta juya wani dan uban tsaki zainab arifah din taja ta fito batace ma kowa komi ba ta wuce wajensa sai taje ta same ayaanah still tana tsaye ajikin motarsa suna magana bata san me suke fada ba

haushi yasa kawai ta shiga nata motar ta daka ma driverta tsawa basu ma lura da ta bar gidan ba. koda da taje gida sosai haushin ayana ya kara tuluwa aranta tana jin kamar duk duniya babu wanda ta tsana kamr yarinyar nan ynx

bata daddara ba ranar da zata tafi haka tasa babanta ya kirashi wai shi zai kaita airpot duk da hakan ya faru har ta wuce U.S hanklinta a tashe yake akan alaqar sa da ayaanah. gashi sunyi da babanta cewa bazatana dawowa gida ba sai once in a while bayan ta samu dogon hutu, tun a jirgi kuma tafarajin inaaa hakan bazai taba yuwa ba, tun bayan graduation innan she bacome so insecured abt ayaanah sai ta fara jin dole ne ma tana dawowa gida akai akai sabida bazata sake yarinyar tagama kwace mata ibaad ita tana can tana karatu ba

tana isa gidanta a manhattan sukay waya da kawayenta iyaka maganan datake musu kenan sai kuma taji duk sun bi bayanta akan tana dawowar kawai in tana zargin ayaanah acewar rukky ai ayaanah tafita komi da komi is only fair if she marked her territory.

bayan kamar wata biyu da wucewar zainab arifah kasar waje daga nan nija kuwa ayaana tafara sauya kalar rayuwarta gabaki daya
schdules na karatun ta da skin care da skills inta na girki duk ta kara kaimi akansu bana wasa ba. dacan bata fiye kashe kashen kudin da uncle moh yake bata ba but the more ruthy tana gaya mata yadda rayuwa take a america the more tana gogewa anan itama. ruthy tana harka da wasu gang ne ita kanta batasan a ina ruthy ta samesu ba they know almost everything abt life kullum tazo shago anan suke haduwa, haka zasuje wajen hair dressing, latest designer da ake dinkin zamani da sauran abubuwa na gyaran jiki na mata tana daf xata y final exams na ss1 aka fara shirin graduation din su kulthum da sultana ranar da suka gama su final exams dinsu aka musu hadadden walima a ranar ne kuma kulthum ta gaya musu cewa yaa maheer yace mata zai aureta but she dont knw what to tell him yace dai taje tay tunani..they kept it as secret basu gaya ma kowa ba saidai su bata shawara, har maheer yay passing bar dinsa yay register nysc.

acikin yan kwanakin nan ibaad yafara batun exams insa na 500lvl yafara clinicals daga lkcin ne kuma ya lura da sudden canzawar da ayaanah tay sosai wanda harshima yasha mamaki irin seriouness da karatu da kuma yadda take bala'in yin wayo tana wayewa harma kamr zata fi su sultana sanin rayuwr kwalisa da kwalliya yanxu. while uncle moh is busy faving ways yana spoiling dinta with gifts dan wata rana har schll dinsu yake zuwa mata da suprise, tuni ruthy ta fara gaya mata cewa ai uncle moh sonta yake yi,ita kuma duk bata dauki abun seriius ba damuwarta yadda zata dawo macen kanta ne ta dan kwace ibaaad a hannun zainab arifah.

first time da zainab ta fara zuwa hutu iyayenta basu so ba amma ta nuna masa bazata iya zama acan haka ba babu yadda suka iya suka kyaleta, kullum tazo gidan she will only provock the situatuon na wann silent jealousy war dake tsakanin ta da ayaanah, zainab tana ji dakanta cewa tana da komi na duniya, ayaana kuwa tana amfani da wann daman tana dada shaping brain da sense of fashion inta.

kafin ayaana takai ss2 maheer ya gama nysc da zai wuce karatunsa aka hada harda hidimar birthdaynsa akayi masa home walima me dadi ranar haka sultana da ayaanah suka zuga kulthum har saida ta amshi batun aurensa yabata kyautar axurfa ring me shegen tsada few weeks after that ita da sultana suka fara level one a bayero university shikuma ya wuce canada karatu...

rayuwa ya zamana basa wani haduwa sosai da ayaana inba agida ko wkends ba wanda yasa ynxu ayaana tafi shakuwa da ruthy sosai sabida suna spending much time insu atare a shago da kuma cikin kawayen ruthyn da suke nuna ma ayaana wani duniyar yan matanci da batasan dashi ba.

she is almost 16 amma sosai jikinta ya habaka silent rival competition dinsu da zainab arifah har sai ya baka dariya
musmn da zainab taxo ta fara jin kamar kanta zai kunce idan ta dawo taga canji ajikin ayanah,kmr yadda akata ririta ilimnta haka taji ana ririta na ayaanah, nd nala is alwys trying to copy ayaanah's fashion sense. gashi dai normal laces da atampa take sawa amma yadda take zagewa tay styling dinsu da dinkin zamani yabi jikinta yasa suka fara kishi da ita sosai

ya zamana ko zainab tana school a can america amma
hanklinta sam baya kwanciya, she was so intimadated da ayaana, professional gym din datake zuwa acan U.S tana gyara shape na jikinta duk sai taji ya fara kasa mata, yadda take ganin jikin ayana yana transforming into hour glass shape dake itama suna fita gym din time to time haka da su ruthy. ita kuma tay tay nata ya canza amma inaaa.. she started to think abt cosmetic surgeries. inda zata biya millions of naira agyara mata shape inta ya dawo me kyau fiye da na ayaanah, still duk wnn bai isheta ba har gidan su tasaka mum dinta hajiya hamida akan lallai ta kirawo mum ramlat collection itama aka siya mata atampopi da leshuna irinna ayaanah. babu abunda basu siya ba aka bawa fashion profesionals suka mata dinkunan zamani yet still duk hanklinta bai kwanta ba.

within dis time business din su ibaad yay flourishing sabida they are well connected and highy marketed by strong business routes he bot his first personal cars ayayinda yake kan kkrin shiga final year yana xuba kudi me yayiwa ma mum dinsa hidima snn ya kuma bude ma ayaanah clothing line online business tana saida imported gowns wanda ko ammi karama ma bata gayawa mata komi da komi akai ba dan harga Allah bataso uncle moh yaji labari bare yay wani abu akai, kanwarsa safiya kuma ya bata kudade itama tanayin nata beaded bag business din agida.

hanklin uncle moh ya fara karkata sosai wajen batun fayyace ma ayaana sirrin dake zuciyarsa da zimman next year tana gama secndry school sai aurensu, haka kawai ya tsira nunawa anty safeerah wata kalar soyayya me ratsa zuciya kudinsa yake zuba mata har kamr baisonsu trying to trap her dan kar yazo ya kawo batun aure ta kawo masa matsala dan ji yake babu amount of borin da zata masa da zaicanja shi ya fasa auren ayanah musmn ma yanxu dayaga ta bude ido ta wayewa sosai

the same week ayaana tafara lura da wasu dabiun ruthy da bata gane musu ba, dan dacan dai ta dauka kasancewarta ba musulma ba yasa take harka da maza but now is becming totally difenrt wasu irin mata da gayu take harka dasu kmr yan cult, nd it feels like she is sleeping with both of them. saidai abune da ta kasa samun wani evidence akansu dan ruthy bata sakewa ayaanah tazo dakinta ga tana aikata wasu abubuwa da ba daidai ba. ita ta koya ma ayaana abubuwa da da wuyane akoya mata su a gida kmr su amfanin saka jigida, full nd elaborated explanation of what female libido is, vaginal care,art of seduction da sexual feelings,har yadda ake aski na maza, she will alwys tell ayana ai intay aure wyann abubuwan zasu mata amfani musmn ma da ynxu da iyawa matan bariki suke kwace zuciyar mazajen wasu, ruthy ta jima tana so ayaanah ta fito fili ta bata labarin alaqarta da uncle moh in aurensa zatay dagaske saita nuna mata hanyar da zatay handling babban mutum dan tunda suke da ita ta lura kmr shine yake yawan bata kayan duniya da kudi amma kuma haryau sai taga ayaanan kmr hanklin ta ma bai kasan gabaki daya.

ayaana bata wani jin maganan kowa inba na ibaad ba, ruthy ta kasa gane mata sam gani take kamar game dinta agefe amma kuma tafi damuwa da wani daban wanda yake da budurwansa da zai aura.
Chapter 107 · 0% Book details