← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 161

Sashe 43

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tana karasowa gabansa ta sulale kasa ta durkusa bisa ladabi da sanyin muryanta dake rawa rawa tace "i..ina kwana...?da fara'a sosai bappa zaidu yace lafya yannan tashi. tashi ki zauna akan kujera mana ai nan kamr gida ne...tana zama da tausayi a muryansa yace "ya jikin naki..kamar zatay kuka tace..lafiya..da sauki..

daga nan yafara mata gaisuwar ya hakuri snn ya tambyeta wasu abubuwa game da mahaifyrtan kadan kadan take amsashi a raunace

ibaad yay excusing dinsu ya koma dakinsa feeling relieved tunda ya damƙata ma bappa ita kuwa ganin ibaad ya tafi baiko kalleta ba tuni sai taji tsoro da raunataccen kuka yazo mata tafara ma bappa zaidu hawaye sosai. ibaad kuwa yana shiga dakinsa baiy wata wata ba ya faɗa wanka baikara sanin me suke ciki anan ba.

daga falon kuwa babu irin nasiha da hakurin da bappa zaidu bai bata ba dakyar tay shiru ta dena kukan, after assuring her to calm down, kuma shima kmr ubane agareta snn ta dauka nan kamar gida tazo suduka zasu riketa har saita cimma duka burikan rayuwarta..

dakyar nasihansa ya shiga kunnen ayaanah har taji dan dama dama aranta ta sake jikinta kadan dashi, ganin ta samu nitsuwa ta kuma fahimce shi sai ya miƙe tsaye da niyyar shiga cikin dakinsa domin dauko babban wayarsa, yabarta ita daya a falon tana zaune da hot cup of herbal tea daya bata tana shansa ahankli ahankli.

yana shiga daki ko minti biyu baiyi ba ayaanah taji motsin mutum abayarta wani irin faduwa gabanta yayi dake ba'ayi sallama ba duk saita dauka ko ibaad ne yadawo da sauri ta aje cup din shayin tana juyowa caraf suka hade ido da ammi babba.

wani tsayuwar cak ammi babban tay tareda furta "innahu man suleimanu wa innahu...a mugin rude tace".... minal shaidanarrajeem. tsayawa cak tay ayayinda kirjinta ya buga da wani irin karfi da tunanin ko gizo ne take gani na aljana a zaune

ganin ayanaahn ta tsura mata manyan idonta a tsorace yasa ta kara dafe kirjinta tanamai kallonta a matsayin aljanar dagaske cos the girl has this rare calm beauty gatadai ba fara bace soll amma ko kadan bazaka kasata a chokolate ko baqar fata ba, kamar wacce zata cire hanjin cikinta take kallonta musmm dataga kayan yarta sultana ne ma a jikinta

kallon da ammi babba take mata yasa ta miƙe tsaye da tsoro da kuma ɓarin jiki sai batace mata komi ba...

haka ma ammi babban ta dauke kai cikin dauriya ta wuceta da kokon to aranta. dakin mijinta ta shiga da sauri sauri kmr ankorota tana cewa Baban maheer, baban maheer..kazo kaga wani abu wani halitta fa nake gani a falonka kmar aljana amma kuma kayan sultana ne ajikinta ni dan Allah kazo katayani gani, katse wayar dayake yay ya daga kai ya kalli matar tasa yace "calm down raihanatu Bakuwa ce" cikin sauke tumin ajiyan zuciya ta d'an yatsina fuska tace "Bakuwa kuma? Daga ina? Kuma ina za'a kai ta?.... Yace "Eh bakuwa.... Daga Tudu. kuma nan gidan zata xauna for a while in sha Allahu rabbi.... Da mugun mamaki tace "toh? kuma Yar wacece ita din? Yace "itama jikar hajiya ce acan tudu..."

A mugun kufule tace "jikqr hajiya? Plss duk jikokin hajiya basu wuce maheer, sultana, mujaheed, kulthum, zainab arifah, safiya da ibaad ba... kawai ka fito fili kagaya min ina ka samo wann yarinyar? yace "Gashi nan na gaya maki, what else did you want to know, me kuma kike son sani...

kamar jiran tambayar take ta mayar masa da amsa da sauri tace "Manufar kawota gidan nan, sannan mun hada wani dangantaka ne da ita da zakace zata zauna anan for a while??"

Ya gyara zama yace "raihanatu yarinyar nan zata zauna damu ne na wani d'an lkci tay jinya kafin hajiya ta gama parking ta dawo kano, dangantakar mu kuma shine kasancewar ta yar uwarmu musulma kuma yarinya karama datake bukatar taimako da kulawa.

kallonsa ta dinga yi looking amazed, confused, and mad at the same time....

tay rau da ido bluntly tace sannu philantropher, the great humanatarian indeed,ohh dama itace wacce ibaad din ya je kauye ya dauko? ni ban gane abinda kke nufi ba, dama kiransa tudu akayi dan ya dauko mana wata karin responsibitliy while we already have enuf ko kuwa a ina kasamo wannan yarinyar nifa bangane komi ba"

jin ransa ya fara baci da tmnbayoyintan sai Ya mike tsaye yace raihanatu ki saurareni, wann umarnin hajiya ne, nd all that aside, she is sick, jinyarta zamuyi anan ynzu..."

azafafe tace toh fine...anji umarnin hajya ne..amma baga kaninka muhammad ba? safeera ce karama ya kamata sai bata ajiya ko akai ma waccan makirar matar..meyasa zaa kawota gidanan nan inba tsabar anraina min wayo ba, ko gidan miji na ya dawo babban opharnage ne bansani ba da za'ana kawo tarukuce ana laka min dan kawai anga bana aikin gwamnati.

batare daya kalleta ba yace " "sanin kanki ne safeera tana zuwa school, snn tana aiki ta same time, fatima kuma kinsan bata zama ynzu sabida aikin bude foundation innan ya riga ya gabato da zafi zafi, ga kuma yarinyar bata da lafya, kinga kuwa dolene anan gidan zata zauna mu hadu muyi jinyarta har sai hajiyn ta dawo sai akaita can...tunda nace mimi yarinyar nan ba zaman har bada zatay agidan nan ba you have no reason to be over reactive.

Yana fadin haka ya fita daga dakin ya barta a tsaye

.... da wani irin kallon mamaki ta bisa lkci daya cikin girgiza kai da tsananin kishi tace tabdi jamm...kajimin wani irin rainin hankali wato safeera yar masu shi baza'a takurata da rainon ko jinya ba, fatima kuma ai dama farkarka ne kowa ya sani baka kaunar abunda zai taba maka ita. to wallah wallah ba a isa raina min wayo ba. wani za'a gayawa foundation? foundation din banza foundation din wufi ai munsan kaine kabude matashi da kudinka amunafurce shiyasa kake neman nika kawomin wata siyasar banza, wato ma nice yar iskanku da zaku dauko wata miskiniyar aljanar kauye alaka min jinyarta to wallah bazaiyu ba....daga ku har yarinyar sainaci uban kowa agidan nan...

ayaanah dai na zaune sai kallon direction din da masifar ke tashi take yi har bappa zaidu ya fito da sauri baice ma ayaana komi ba banda murmushi me sanyi dayamata ya fice da sauri yay waje domin duba wani bakonsa akofar gidan daya kawo mai wata aika

gaba daya a tsorace ayaanah take lkci guda taji sabbin hawaye ya kawo cikin manyan idanuwanta tana Allah Allah ibaad yashigo....

Bayan kamr minti biyar Ammi babba ta fito daga dakin tana wani cika tana batsewa kmr wata boss take kallon ayaanan tana huci, tana kawo dede kanta ta tsaya, cikin sanyin jiki ayanah ta sulale kasa ta rusuna zata gaisheta atake taji an daka mata tsawa me karfi "Ke maza tashi ki fita ki ban waje kar in illata ki, munafikaaa kawai..."

amugun rude ayaanah ta miƙe da sauri tareda fashewa da kuka tana laluben hanyar ficewa

muryar ibaad ta ji atacan sama da alaman yana waya sai ta tsaya cak tana kuka sai kuma bata gansa ba jim kadan wani kyakyawan mutum ya bayyana agabanta yana saukowa kasa yasha expensive tailored black suit insa irin na typical law student..
#Surayyahms
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[11/11, 21:38] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ⏯️1️⃣9️⃣
suna hade ido da maheer wani irin shirun bazata tayi tabita tsura masa raunatattun idanunta dake famar zubowa da ruwan hawaye masu yawa kamr ruwa a mugun tsorace ta tsaya cak kmr yadda taga shima ya tsaya yakuma tsura mata nashi sexy eyes din in complte awww of her rare calm beauty danko motsi baiyayi at the sight of her dayay freezing dinshi ya tsaya cak kmr an dasa shi da kankara...

sunfi minti biyu suna kallon juna sai can ta sunkyar dakanta ahnkli cikin tattaro makanta wata nitsuwar karfin hali tay shiru idonta na kallon kasa kamr wacce take neman wani abu aka tiles din

ajiyar zcyar bazata ce ta kwacewa maheer yay murmushi me sanyi danko ba agayamai ba yasan wannan ne yarinyar da ibaad yazo da ita, karasowa yay tare da dawowa cikin hayyacin sa ya kalli sunkuyayyen kan ayaanah yana murmushi me sanyi yace "Hi preety one..
shiru tay taki sam ta daga kanta...dada karasowa yay zai dafa kafadarta yana kawo hannunsa tay wuff ta firgita zata arce aguje ya riƙeta, wani dan uban kuka ta fashe masa dashi yace hey hey calm down..ina zakije? tay masa shiru a tsorace take waige waigen baya, bayan shima ya kalla snn yace toh "waya koroki" kara sautin kukan tay yace ya salam toh..ina shi ibaad din? ko wajensa zakije ne,...da mugun sauri cikin kukan ta gyada masa kai har sau biyu..cikin muryan lallami yace" okay, toh zan kaiki, kidena kuka kinji?big preety girl like u ai basa kuka..share hawayenki. dan gyada masa kai tay shisai ya saka hannunsa dake zuba qamshin tonka notes yafara share mata tears dinta dashi yanamai dada kare ma halittar ta kallo, like the girl is so soo perfect nd flawleess, yadda take famar sauƙe ajiyan zucya me nauyi kuma a tsorace yasa bakara min tausayi ta bashi ba...

yana cikin share mata tears din ne sukaji motsin mutum abayansu yana daga kai yaga mahaifyarsa ammi babba ce ta fito ranta a mugun harde

baice mata komi ba ya dan kalleta snn ya kalle ayaanahn sai atake ya fahimce abunda ya faru

jira take taga ya gaisheta sai taga ya wani irin haɗe rai ya kara dauke kansa ya mayar kan ayaanahn yanakan lallashinta ahnkli harsaida ta nitsu snn yace "preety. muje inkaiki wajensa ko..

har ayaanah ta daga kafa cikin daka tsawa ammi babba tace "..maheer!!! yana juyowa tace "babu inda zaka kaita..ka saketa anan inyaso ta tafi duk inda zataje..

kara juyowa yay azafafe zai amsa cikin tsananin bacin rai tare da katse shi da zafi zafi tace "enuf. yau bana bukatar jin lectures dinka see me in my room ryt this minute, maheer wallah bana wasa dakai..kanaji na ko??
Chapter 43 · 0% Book details