← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 161

Sashe 21

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hajy hamida kuma tafi matsuwa datasan educational level din ibaad bawai dan zai mata amfani ba saidan ta samu wani makafar ci masa mutunci da kaskantar dashi in the future, she was highly expecting to hear some mediocre course. saidai tun ya ce musu medicine mbbs yake karantawa a jamiar Ado Bayero sai taji ranta ya baçi wann karon batama iya boye tsanar da take masa a fili ba..,

cikin furucinta na rainin wayo sai nuna mai take kamar bai kai ya karanta wann course din ba. sai tambayar ya uwaka tay ta haifeka take masa akan karatun. tanamai nuna masa karara cewa medicine yafi karfin brain insa like he cant just afford to be a doctor. tafara masa suggesting su hospitality managmnt, zoology, french, islamic, political science, library science, history, hausa e.t.c..shide ibaad bai iya raina babba amma tunda ya gane salonta na rainin wayone sai ya zamana da daddaya yake bata amsa me kaifi da nauyi wanda yasan hakan yana mata ciwo aranta sosai. duk courses din data kirasu mediocre saida ya gaya mata relevance insu a real life. ta dage masa wai saidai yabar medicine ya karanta wani course dede dashi. shima ya dage da ce mata aiwann dinne ma kawai dede dashi.

duk wadatar da bappa zaidu yake dashi na kudi da rufin asiri still zaginsa takeyi tana cewa wai aibazai iya ilimantar da yaransa snn yazo yq ilimantar da ibaad dake maraya ba. yanayin datake sakayawa tay zagin hakanan shima ibaad yake sakayawa ya cakka mata amsa tare da mata tambayar ko ta taɓajin bappa zaidun yazo gabanta ya durkusa yana nemam taimakone akan harkan iliminsu

it was so clear dat jinin hajy hamida sam bai hadu dana ibaad ba.

ganin hirar tasu is bcming a bit awkward yasaka prof ya fara kawo batun karatun zainab arifah, ryt in d midst of their heated conversation yafara yaɓa ilimin yarsa yana nuna cewa itama yar baiwace, kuma business kawai zata karanta infact sai takai matsayin higher doctorate, yace yarsa bata bukatar dagewa sabida ilimin gidansu ta gada, amma shi fa ibaad din nuna masa sukeyi baida wann gadon ilminin dolensa sai yadage. duk dai yabi ya rasa menene takamamen abunda yasaka mutanen nan suka kirawoshi gidan su dan banda baqar magana da cin fuska baiga abunda yake karba a hannunsu ba.

har saida suka gama kammala cin abincin snn prof ya fito fili ya fara masa magana akan alakar sa da zainab arifah cikin sakayawa, sai yake nuna masa tunda yafi aminta dashi yana buktarsa da yadinga sake fuska wa yarsa zainab arifah dan tadada sanin danginta with his supervision. wasu kalamai, da karairaye da cin fuskar daya gaggaya ma ibaad akan familynsu ma hankli bazai dauke ba, its obvious gani yakeyi kamar kowa ne yake masa baqin ciki akan daukakar da Allah ya basa kuma kudinsa akeso ba shi ba.

ibaad yay shiruuu harsaida prof ya gama kushe kowa adangi ya koshi snn yabashi baki....

nan ne kuma hajiy hamida ta fara kawo nata surutun cikin irin hikimarnan na mata dan ita haryau bata yafe dukan dayay ma yarta ba, kai tsaye ta fara kawo masa batun dukan dayay ma zainab Arifah kai tsaye tafara cak cakka masa magana wai "sun yafe masa ne sabida sungane ba lefinsa bane lefin uwarsane data tarbiyantar da namiji kamrsa me dukan mata tun yanada danyen shekaru.

wann maganan sosai yamasa zafi aransa musmn yadda prof ma kansa yake cewa ai ammi karama a danyen shekaru aka aurota bata da wayo hala ma mahaifin ibaad dayake raye dukanta yakeyi agaban ibaad shiyasa itama bata san yadda zatay ta tarbiyantar da danta namiji ya dawo ɗa na gari ba.

ganin ibaad yadena cin abinci yay shiru baice musu komi ba, jikinsu yafara basu hala ransa ya baci ne,

sai kawai suka wanye cikin hira suka ce ma zainab arifahn wai ta bashi hakuri agaban su dansu tabbata cewa komi ya wuce tsakaninsu. dakyar zainab din ta amince tacemai yay hakuri wanda dashi da babu kusan duk dayane dan abune anayi ana masa iyeyi, gashi tsabar iya manyance da shagwaba irintata wani bin intana magana ma basajin metake cewa.

ibaad sosai yagama gane yanayninsu, mutane ne marasa mutunci, ya lura so kawai suke sukulla wata friendly alaka tsakaninsa da yarsu zainab arifah amma bawai dan son ransu suka nemeshi ba. they want him to blindly tolerate zainab arifahs spoilt brat behaviour, ace kome tace masa kar yay mata tsawa, fada, bare duka, he can clearly read what is behind their selfish fabricated gestures and intensed fake smiles amma dake shi yarone duk sai ya danne abun aransa ya biye musu har suka gama surutansu bai musu rashin kunya ba duk da zagin uwarsa da sukayi wanda duk shi yafi masa ciwo aransa sosai.

bayan kamar awa guda da zuwansa yace musu zai tafi gida..wani irin murna sukaji dayace hakan acikin ransu, amma a fili har wani ɓata rai prof yay yahaushi da masifa "haba haba kai kuma sai kace wanda ake korarka...cike da makirci hajy hamida tafara fada" hmm alhaj ainni gani nayi kamar be wani sake jikinsa da mu ba, he barely eats kuma nace amasa packging din abincin nan yace min a'a, karshensa sai dai azubar kenan kasan dai mu bama cin irin wann local abincin, yo ko maganan kirki fa basu zayna sunyi da yar uwansa ba gashi yanace mana wai zai tafi..

atake zainab arifa tafara hararar mum dintan dan duk wani surutun cin fuska da suka masa yasa ita bata wani ji dadin haka ba. yadda take mutuwar son ibaad ko kadan batason taga ransa ya baci.

cikin katse mitar mum inta da muryan shagwaba tace mummy pls nidai kidena masa fada kibarshi ya tafi hala dai ya dan gaji ne kmr fa daga schll fa ya taho he need to go and rest.

ammkance hajya hamidan tace nd who told u daga schl ya fito da duk wann uban kwalliyar ke kuma yar azarbabi...

ckin rolling idanu ahnkli tace kai mummy haka fa shi yake dressing, nd i have my ways mum
kinsan elder bro na kawata nala kin tunashi? ayatsine hjy hamidan tace eh, tace toh ai ajinsu daya da ibaad so dazu muna chat da nalan ita tacemin a schl suka wuni yau so pls just let him go..okay?

murmushin yake kawai prof yay ganin yadda zainab din take ta kkrin kare ibaad wajen mahaifyarta

shide ibaad baice musu komi ba yama juya kansa gefe kmr baya wajen,can prof yadan kallesa yace toh bakomi sai Ka maida hankali sosai, shi zumunci da karatu kusan shi ne abin da mahaifinka ya fi so arayuwarsa, saika dage snn idan kasamu lokaci ka dinga zuwa kana taimakawa yar uwarka zainab arifah da karatu agidan nan, i know my princess is smart amma ai tana buƙatar kwarin guiwar daga yan uwanta.

babu yabo babu fallasa ibaad yace toh bakomi kawu. ni zan wuce. Nagode sosai da kulawarka. hajya hamida ta ɓata rai ganin har zai juya baice mata uffan ba..

prof ya ma zainab Arifah ido akan tabishi waje, duk dai burinsa baifi yasa zainab taji cewa yana tare da ita akan ibaad ba, dan hakan ne kawai zaisa tay tunanin zata same soyayyarsa harma ta cire damuwar soyayyn aranta ta warke snn tamaida hankli wajen karatunta sosai.

tunda taga babanta ya bata go ahead da rawar jiki ta kama bin ibaad abaya wanda tun basu gama ficewa a hallway din ba suka fara jiyo muryan hajy hamida datake fmr mita da masifa "alhaj kaga rainin yaran nan ko? waima "hajiya" fa yake cemin kamr ni bankai na haifesa ba nide next time yazo gidana nd he stands to greet me wallhi zanci masa mutunci inhaka yake gaida uwarsa atsaye agida toyasani nide nafi karfin yaro kmrsa ya gaida ni a tsaye masifa take ta inda take shiga bata nan take fita ba..

ibaad kuwa tunda ya saka kansa bai kara juyowa ba barema surutunsu ya damesa dan already ransa ya baci sosai. har me aiki tabude musu kofa duhu duhu yake gani bai daga ido ya kara kallon kowa ba, yana ficewa harabar waje zainab Arifa ta karaso da sauri harta jikin motarsa tana haki da wani irin rangwada tace hey ..ibaad, please wait..

Miskillalliyar Ajiyar zuciya ya saki snn ya juyo adan takaice Suna hade ido ta dan sakar masa murmushi maisanyi, sai snn ta tuna zcyarsa a kusa yake baison magana musmn ma na raini so da wurwuri tace mai "salam alaikum, Hi .

kallo ɗaya yamata ya amsa sallamartan a dakile tare da dauke kansa yanamai kawar da idanunsa can gefe.

"i just want to say thank you for coming..

kallonta kawai yay baice komi, da sauri tace "toh ya su anty safeera agida? tun be amsa ba tace ohhh just forget them.. uhm u know, i have been hospitalized. jiya da darema aka dawo dani gida bakaga na canza ba.. i have this..

ganin zata cikasa da surutu banza cikin datsar numfashinta yace toh its okay, saiki koma kije ki huta Allah ya kara sauki..

sounding childish and desperate ta rolling masa ido tace okay, "thank you, thank you soo much for seeing me,wont u like to knw daf ciwon damuwa ne kawao likitta yace yake damuna, nd i have...

ibaad ya mata wani irin dakakken kallo kmr na wanda ake sakashi tsyuwar dole yace ciwon damuwa kusan kowa na fama dashi nd am sure u u ave a therapist by now so why are u telling me?..

ɗan shiru tayi tanata kallonsa kafin can tace mishi umm notin, kawai so nake kasani, kasan ba kowa bane yake iya mantawa da wani abun dake yawo acikin ransa.

kai tsaye cikin datsar numfashinta yace 'toh ke Ki koya mana, Zai taimaka miki fiye da tunaninki. dede nan yabuɗe ƙofar motarsa agajiye takasa cewa komi tanata kallonsa har yashiga motar ya zauna snn takuma cewa thanks for ur time ibaad, it means alot..
..da emotionles face nasa ya dubeta yace "Allah ya kara sauki
..daga haka ya daga glass dinsa ya kunna motar cikin kankanin lokaci ya doshi gate aka bude mai yafita.
Chapter 21 · 0% Book details