← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 161

Sashe 159

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fuskar tsohuwar ba asake ba takalle bappa tace "zaidu maganan nan fa ya kare bama sai anje ga tozarta zayyanu agaban mutanensa ba tunda abunda kuke gudu kenan, dolene kawai ayi auren Ayanaah ayau din nan, babu wata zancen guduwa ko fasa shi, tunda shi wanda ya sakar mata fuska ya mata alherin shi ta cutar ta tozarta, yau koma uban waye mukaga dama dashi za'a a daureta yau, inyaso taje can can gidansa ta karashe rayuwarta dashi inma kashe kanta zatayi a dakin miji gara tay da akanda tazauna min agabana ta cigaba da tonamin asiri tay karuwanci a birni ubanta juma nacan kauye yayimin dariya, aure kam kamar an daurashi ayau ko tanaso ko bataso

wani irin shiru wajen yakara daukawa a falon ayayinda fuskar sauran matayen looks soo soo confuse da furucin tsohuwar duk da alama basu wani gama fahimtar inda maganan tsohuwar ya dosa ba, to da waye kenan za'ayi ma ayana auren dolen? da mujaheed ne ko wani ne nadaban daga waje? saidai tun kafin dayansu ta budi baki tay tambaya bappa zaidu yakalle su duka biyun fuskarsa ba a sake ba still cikin gyaran murya yace ya kamata kubami wuri zanyi wata magana da hajiya"..

babu tantama kowaccensu suka mike tsaye cikin hadiye tambayar dake ransu snn suka fice waje.

Ammi babba nan tay sashen abty safeera da uban sauri dan taje ta yafa mata gurmi

ammi karama nan tanufi dakin Ayaanah kai tsaye jikinta duk a sanyaye, ta iso kofar dakin Ayaanah bata sani ba, kife kai tay akan gadonta tana ta kuka me karsashi gashi ita kanta tarasa amsar da zata bawa kanta, kanta duk ya kulle, she was like is this actually happening to her abu ne da batay tsammani ba sai gaba daya sai taji ta fice hayyacinta, she wish zata bude idonta taga mmmunan mafarki kawai take,

kwankwasa kofar dakin da akay da dan karfi yasa tadaga idonta da sukayi jaaa suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi tabude har akagaji da Knocking aka bar wajen.

Sai can wajen after good 40 mins data dan dawo hayyacinta tana xaune saman gadon kafin ta jawo wayarta da kyar da kamar zata bude sai taji xuciyarta ya kara rauni, MTN sim card dinta take son cirewa ta karyashi sai taga tarin missed calls din kawar aikinta Ruthy yafi guda talatin da wasu irin zafafan text messages da ya ninka calls din daga wajen ango to be din nata, ko wani message data bude zance daya yake yi, " i once trusted you, nina miki kaza nina miki kaza lokcin baki da kaza..kinci amanata ayanah, bazan yafe miki ba.." kowani kalma da ya rubuto mata suna daukene rashin mutunci da gori, tsana da zafin cin amana da butulci dayake famr tunanin tay masa.

wasu irin raunattun hawaye suka shiga bin kuncinta bawai dan zafin words dinsa ba sai gani datay wai har ya aminta da komi dayagani akanta kai tsaye, dan tay tunani in akwai wani wanda zai iya bada kwararren shaida mai kyau akan iliminta da tarbiyanta da shine mutum na farko da zai bayar, ita ko kadan batay tsmmanin cewa ya jima yana zargi da kallon ta a matsayin wance tasan maza ba ashe shaida kawai yake jira dama

fita tayi daga Inbox din hawaye me zafi na sauka a idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da gori masu zafi aciki, gashi shidin ba yaro bane bare tace ko yana furta kalaman nan ne da gigin yaranta wai yau namijin da ake ikirarin zai aureta ya rufa mata asirin kenan yake kirarta watsatsiya karuwa hmmm.

kirijnta taji kamar sai fashe badon fasawar auren na sao dan zafin kazafi da bata suna, Kashe wayar kawai tayi ta ciro sim card din ta karyashi into 2 pieces kamar yanda tayi niyya snn tajefar da wayar can can saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, sam batay tsammanin haka kwakwalar maza ke aiki akan zargi ba dan wasu tsauraran maganganun nasa ya mugun tsaya mata a zuciya.

Knocking din kofa aka sake yi, ta kalli kofar sai kuma tamike a hankali ta nufi kofar ta budeshi ahankli, ammi karama ta gani tsaye suna hade ido nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta tabi ta sunkuyar dakanta kasa cikin sanyin jiki

ammi ta shigo dakin ta kulle kofar ayaanah ta bi ta da kallo harta nemi waje ta xauna agefen gado snn ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya me tafe da hawaye tace "Ammi don girman Allah kiyi hakuri, nasan kema zakice na tozarki wallah bansan komi akan wann abun ba.

ammi ta sauke wani ajiyar xuciya ahnkli cikin nitsuwa tace "Ayaanah i am not here to judge you, bare ma ai an riga anyanke miki hukunci auren nan naki bazai fasu ba, su hjiya sunce za'a daurasa a yau, kuma tun da har bappanku ya amince da wann hukuncin da hajiya ta yanke miki kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasu ke dai naki addu'a, nima ina nan ina taya ki da shi..

wani irin numfashi me karfi ayaanah taja abazata wasu sabbin hawayen da bata san dasu ba suka cigaba da sauka mata yuuu amma batace komi ba

cikin lallami ammi karama tace is okay kiy hakuri ayaanah snn kisani nobody is perfect but as long as we learn from our mistake ai shikenen, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji everything will be alright kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya isa miki da ya janyo miki wnn masifar harda kuma auren dole da wanda ba musani bama tukuna.

a mugun mugun rikice Ayaanah tadan mike tsaye is like sai yanxu kunnenta ya farajin batun wani auren dolen da ammi ta ambata..

atake jikinta sai ya fara rawa cikin dafe kirji tare da sakin birkitacen kuka me tafe da rudewa tace "ammi Auren dole da wani wanda baku sani ba kuma? auren dole fa kikace again Ammi? dama badashi za'a daura auren ba kuma.?

jiki a sanyaye ammi ta dan gyada mata kai tace shikam ai yace ya fasa saidai wani to wanin ne bansan ko waye ba.

a mugun ragwabe ayaanah ta fado kasa tare da durkusowa kasa cikin kuka mai kara, tarike hannun matar tana cewa dan Allah kar ayi min haka Ammi wllh xan iya mutuwa, ammi talk to him plss ai bappa yana jin maganarki sosai, dan Allah kiyi ma hajiya magana i can explain myself wallah wallah bansan komi ba, basai sun min auren dole ba nasan zata saurareki kodan karamin lokaci su karamin i will find a way out of this.

cikin runtse ido tare da jin tsananin tausayinta matar tace nima basu gaya min komi akai ba, amma dai mujaheed is on his way. kinga tunda angon shi yace ya fasa i have no idea what they are planning to do now, ga dai su can a falo inaga by now kuma inaji kmr ma har ma an daura. i am very sorry dear, kisani cewa I trust you. but i think wann ne kawai mafita agaremu duka gwara amiki auren kawai. snn koma waye suka miki auren dashi nasan dai bazai cutar dake ba Allah yasa shine miki mafi alheri.

Ayaanah ta dada rushewa da wani tsumammen kuka cikin mugun tashin hankali take cewa "Na shiga uku Ammi, yanxu baxa ki iyayin komai akai ba?auren dole fa zasu min da wanda kemafa kince baki san shi ba, ya xan yi da raina idan hakan yafaru, wallh ko ya mujaheed din ne bazan iya aurensa baa innalillahi wa inna ilaihi rajiun..."

Mikewa ammi tayi da hawaye taff idanunta da mugun tausayinta aranta tanufi kofa da sanyin jiki ta bude tana fita takulleta da keys ta waje........

*CIGABAN LABARI...*

fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan, tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa wayonta da kkrinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma antu safeera sirrikanta na cewa bokab da ya mata aiki akansu yace har ta mutu agidan bappa zaidu baza mata kishiya ba....

wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya

anty safeera ta share hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya

**********
kafin nan daga falon ba ajima da korar su ammi ba hajy mairo ta sako maganan wanda ya dace 'a maida auren ayaana akansa dan su ceto kansu daga tozarta

kai tsaye tace ai anjima dace mata ibaad yasan komi game da irin abunda ayanaa take aikatawa da rayuwrta dan haka shine ya dace ya riketa inba haka ba babu wani wanda zai aureta agidan nan asamu kwanciyar hankli da rufin asiri dalilai goma da ashirin duka ta jero masa, zaka sha baqar mamakin jin cewa ashe tuntuni taawure ta gaya ma hajy mairo cewa in ayaana ta girma ta hadasu aure da ibaad

tuntuni bata tashi tuna maganan nan ba saiyau datakeso tafito kiri kiri tay weaponising dan kawai asiri ya rufu kar yaranta su tozarta.

bappa zaidu yace shifa bazai tursasa ibaad auren kowa ba har sai inshi yace yana so suna cikin maganan kuwa sai ga su maheer da ibaad sun karaso

hajya bata bari sun zauna ba ta dau waya tace driver yaje maza maza ya karasa dauko mata alhaj hamza ace masa its very urgent.
Chapter 159 · 0% Book details