← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 161

Sashe 46

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

anty hauwa na dariya tace aa doter haka kuma zamuyi dake ko kin mantani ne jiya fa awajena aka ajeki shiru ayaanah tay tacigaba da kukanta daga irin kallon da ibaad yake mata tasan ransa ya baci, ya kalli anty hauwan yace mumy pls excuse me' tanacewa sure, ya jawo ayanaan gefe cikin zare mata ido yace" uban me yasa kike min kuka ynxu waini sa'anki ne? ko in maida ki gidane ki zauna da wajen waccan matar ta rika zunguri?da sauri sauri ta girgiza mai kai tana zubar hawaye sosai.. yace toh meye damuwarki...muryan ta asakrfe da kuka tace"..karka tafi..nifa tsoro nakeji, yi yay kamr zai wanka mata mari dan wani bin har mamakin kansa yakeji ganin yadda comon hawayenta yake sawa zucyarsa da tempernsa yakeyin mugun sanyi har yana saurin daga mata kafa har haka batare da ya masifeta ba.

...ahnkli yace "Dake dodonni kika gani anan ba mutune bako ke nifa banason iskanci da shegen son kukan banza..."ga anty hauwa nan zata kula dake duk abunda kikeji kigaya mata, inkika sake kiky fitsari ajikinki duka zan miki kinji ko!. tace toh yace good girl..bazan jima ba zanzo na daukeki anjima .da muryan kukan takuma ce mishi "toh" jawo hannunta yay direct ya kara maidata wajen anty hauwa yace "toh mummy gata nan she is good nizan tafi..
da fara'a ta amshi daya hannun ayaanahn snn ta wuce da ita ciki, yana tsaye har saida suka bace ma ganinsa snn yafito ta samu maheer baya wajen da motar..

yaciro wayarsa again dialing numbersa yafaray bai dauka ba sai can after like 12 minute saigashi nan ya dawo da ledojin chops har guda biyi he bot all kinds of expensicve fancy chokolates da hot fried chips da egg sauce da katon cinyar kaza akai, yace sam sam saidai subada ayaanah kafin su tafi

bada son ran ibaad suka koma ciki da abincin ba, haka yajira maheer ya kara lallabta akan taci dan ta samu sauki snn suka wuce suka nufi makaranta

har cikin building din medicine yakai ibaad dake yau normal lectures yake dashi yana sauka shima ya wuce nashi business din..

ata fannnin aayana kuwa duk wani abunda maheer ya siyo daga zarar ta saka acikinta aman shi kawai takeyi duk saitabi takara jigatuwa tabi takara galabaicewa jikinta ya niqu yay laushi sosai

har saida anty hauwa ta dauki dubu goman da ibaad ya bayar ta aiika security awaje akaje aka sissiya mata oranges banana da apples kafin nan tasha su sai taji dama dama har wani nitssatsen bacci yazo ya dauketa abazata.

2pm Crescent International School (CIS) Kano

Kararrawar tashine yq cika harabar makarantar Crescent International School ayayinda tuni Gate ɗin schl din ya cika da mahaukatan motoci wasu masu tinted ga direbobi na shigowa bisa layi kamar suna jiran yayan gwamnoni da sarakuna su fito.

Zainab Arifah ce tafara fitowa daga cikin ajinsu dan ita bata tsayawa har sai malami ya sallamesu ya fita, ana buga bell din tashi kawai zata dauki bag pack inta tay waje batare da ta dau permission awajen kowa ba

last subject da sukayi was literature in english luckily she loved that subject, a yangace tafito kofar ajinsu tana tafiya ciki wata mayyar big girl catwalk ko ina ta ratsa sai an juya an kalleta dakyau dan hatta Uniform ɗinta ta zaɓar mata yadi me tsada na musnm akayi da international tailor nata daban bakaramin amasar dirin jikinta yay ba dan tana dan girman jiki, customised iPhone ne a hannunta ta rike tana fliging dashi iska

tana isowa gaban science class manyan kawayenta Nala da Rukky suka fito batare da sunce ma juna komi ba sukahau binta abaya kamar fadawa suna wani irin takawa a kasaitance kamr bazasu taka kasa ba suna masu exchanging din murmushi mainuni da cikakken biyayyyar su ga duk wani umarnin sarauniyarsu zainab arifah mansur

suna daf da isa tsakiyar quad-angle nala ta ji wasu ɗalibai biyu suna faɗin hmm kiga Waccan sabuwar student ɗin bura uba kun ga jakar hannunta kuwa? super expensive luxury Designer ne fa irin na zainab Arifah.” wani cak Zainab arifah ta tsaya ciki juya idanu ta juyo a hankali kamar wacce takeson gano wanda yakuskura yay wannan maganan...

Kafin ka ce me, nala har ta hango musu wata sabuwar yarinyar acan bakin assembly block tana tsaye hannunta rike da Jacquemus bag pack, same colour same model exactly irin na Zainab’ arifah. rai amugun bace rukky tace what....kunga min wani kuturin bala'i?

murmushi mai haɗari zainab arifah tay ta kalli yarinyar cikin tabe baki tace girls just look at this audacity.

suka kalli juna cikin yatsina fuska suka karasa walking slowly kusan all eyes on them

jawo hijabin yarinyar da karfi rukky tay tace “kee Ki zo nan.” batare da bata lokaci ba Sbuwar yarinyar tajuyo garesu a hankali tace yess?

wani dan uban walaknccen kallo Nala ta mata kafin tace kin san jakar da kika riƙen nan nawa ce?

yarinyar ta daga jakar cikin rasa na cewa..ta zuba musu ido tanata kallonsu a dan tsorace

Rukky tayi dariya ta kwace jakar lallatsa snn tace “hmmm Yar kasuwa! Copy copy!”

da sauri yarinyar tace look, i dont knw what u guys are talking abt nide Daddy na ya siya minshi daga Dubai..

cikin katse ta da murmushin rainin wayo zainab arifahn Ta ɗauki jakar da yatsa daya ta juyashi awalaknce sann ta sake shi akasa ta hau kai da shoes inta ta tsaya tana takawa kamar ba komai ba

cikin yatsina fuska tace “Fake ne, ko da ya zo daga Dubai, ai musan cewa akwai Dubai na talakawa.”

Wani muguwar dariya su nala suka fashe dashi dedekun studenr dake kallonsu suma suka jonasu suna dariyar.

ganin sun jawo enuff attention na mutane akansu yasaka zainab Arifah ta cire nata jakar wadda take limited edition ne, sam ba a samun irinsa face sai anyi ordering insa through elites personal shopper.

atake ta miƙa mata mata jakar tace gashi Ki rike wannan, koda walakntattun hannun ki zasu taba original, snn Ki san cewa ban cika zama da abunda da ake yin kwafinsa ba.

hawaye ne ya cika idon yarinyar ta tsaya cak da jakar hannunta kmr zombie ayayinda sauran yaran suketa mata dariya ana nuna ta in the most embrassing way kowa yana mata dariya

nan Sai ga wata makirar black colour V8 Land Cruiser ya tsaya agabansu, Direba ne ya sauko agaggauce ya buɗewa zainab arifah kofar baya..

Nala tace yesss the Queen’s chariot has arrived.”

fuska a dore Zainab ta juya ta shiga car din ba tare da ta kalli kowa ba har saida ta zauna a owners coner snn ta sauke glass kasa Fuskarta a matukar daure ta kalli yarinyar snn tace let dis be a warning, i set the standard, not you..sabida haka karna kara ganinki da irin kayana a makarntar nan.

tana gama furta hakan ta rufe glass din motarta tare da odering driver to drive her away atake ya kunna motar ya wuce da ita gida..

suna isa gidan tun be gama bude mata motar ba ta turesa gefw ta sauko fuskarta dauke da matsanancin fushi

kai tsaye ta wuce cikin main mansion dinsu ayayinda kusan duka masu aikin gida da kuma personal maids dinta suka hau gaisheta tay banza dasu..

tun daga falon ta fara cire kayan jikinta tana zubarwa akasa maid dinta elizabeth tanabi tana tattarawa...

harsaida ya rage daga ita sai pant da bra snn ta shige room dinta a wani irin yanayin fusata ta banging kofar saida ya shiga security lock dakansa..

haka masu aikin kulawa da ita suka taru a kofar kowa yana mata magiya ana ta lallabata ana bata haquri duk dama basu san meya bata mata ranta haka ba.

can da suka isheta rai bace ta ta bude kofar tare da watsa musu rowan gora a fuska da jikinsu cikin tsawa tace musu "go awaaaay..kudena damuna, bana son ganin kowa anan wajen...just get ouutttttt...

gabaki daya gidan saida ya dauka da karfin muryanta sikinini masu aikin sukabar wajen kowa da abunda yake ransa dan bayau aka fara ba...

zainab Arifah yarinyace sa ak mugun sakalta ta couple with a bastard level of ego and ill manners...

elizabeth ta sauka da gudu kamar ankorota wanda tsabar girman gidan it took her almost 10 min kafin nan ta iso sashen hajiya hamida dan ta sanar da ita abunda yake faruwa

tana shigowa kofar falon sashen saida tay sallamar kamr minti biyar kafin nan hajy hamida data ci wani dan ubansu kwalliya tasaka wata arniyar gown na tsadadden original bazin shadda tana cin apples tana kallon wakokin mali cikin shakawata ta bata izinin shigowa ciki..

zubewa elizabeth tay agabanta cikin girmawa tace ranki shi dade hajiy zainab arifah ta dawo amma kamr tana cikin tsananin fushi duk ta kore mu taki bude kofar bare na hada mata ruwan wanka ta sauko taci abinci.

cikin yatsina fuska hajy hamida tace "and so?..cikin daka tsawa tace "ke tashi kawai kibarmin nan cos i cant deal with her anger issures ryt now, kujje kujira in babanta ya dawo saiku samesa kugaya masa halin da yarsa takeciki.. just get lost haba mana duk tsamin jikinki ya cikamin ciki wann uban warin da kikeyi elizabeth ai zai iya sani inyi amai..

jiki a sanyaye elizabth tace i am sorry ma..i take my leave.....

komawa tay sashen ta nemi waje ta zauna ata kofan zainab arifah tana Allah Allah prof ya dawo da wuri kafin wani abu ta faru da yarsu su walakantata.
#surayyahms/2025
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*

*WATTAPAD @SURAYYAHMS*

*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*

#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025
[13/11, 08:20] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: 2️⃣0️⃣⏯️ABUNDA KE ƁOYE/surayyams💫
maid elizabeth tafi awa biyu tana zaune cikin yanayin lura da kowani irin motsi da zai fito daga kofar zainab arifa, with few oda kitchen maids wanda time to time suna lekowa cikin sintiri a sashen kowa na fargaba tareda jiran zainab arifah din tasauko daga fushin datakeyi wanda sukansu basusan musabbabinsa ba,
Chapter 46 · 0% Book details