← Book details Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 161

Sashe 29

Abunda Ke Boye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hanklin juma sosai ya tashi da jin wann furuci, saida suka ganema cewa bada saninsa yaran suke karatu ba aikuwa su suka hau fede mai biri har wutsiya na batun karatun da su inayah da ayaana sukey, komi da komi saida aka gayama juma abaibai wanda tun bai bar wajen ba mazan dake wajen aka fara yaɗa labari nacewa juma cikakken lusari ne baida gindin haifan yaya maza gashinan ashema matarsa taawure tafi krfinsa akan harkan gidansa da yaransa taje tudu ta saka yaransa a makarantar kafuraye batare da izininsa.

ranar kamar kan juma zai fashe da feshin wuta haka ya kamo hanyar gidansa da gudu idanunsa sunyi jajizir ruwan saman nan da aka fara sabo kaf akansa ya kare...

yana dawowa gidan ya shiga turakarsa ya dau wata igiya ya cusa a wandonsa snn ya dau wata addansa mai kaifi akan yau xaima tawure dukan mutuwa snn ya sare kafafunta dashi..

hakanan yaci nemansu agidan har wajajen daya saura na rana bai samesu ba kuma kwata kwata bai kawo aransa cewa har taawure zatay tsaurin idon kashe aurensu akan ciwon inayah ba, adan dolensa yaje jejo ya nemo kasurkurmin magulmacin nan dandanko, sabida yasan duk tsiya abakinsa kawai zaiji labarin inda taawure takai masa yayansa,

haka ya bazama jejin kmr mahaukaci da kyar ya sameshi, dandanko dayaga juma wujiga wujiga sai yaki sam ya gayamai komi saida ya sha cikinsa yaji labarin asalin meke faruwa tukuna.

bayan yagama jin komi sann yahau kara masa wuta yana cewa aidazu ance masa anga matarsa taawure ta goyi innari sun wuce tudu da kayansu, snn yabi yace ma juma toh tabbas cikin shege ne inayah take dashi sukaje zubarwa a tudu awajen likitocin kafuraye, inba hakama ba, wani irin ciwo ne haka inayah takeyinsa da amai da rashin cin abinci da kuma ciwon ciki me tsanani..snn kuma ace duk saiwoin kauyensun nan ya kasa magancewa...

yace ma juma kawai dai cikin shege innari taje ta kwaso taawure take kokarin boyewa kawai yaje ya dau mataki sabida kar martabansa da kimansa ya kara zubewa a garin majiya.

hakanan ya kara pumpa zuciyar juma da zugi da kuma zargi harsaida yasaka ta karayin baqi qirin da mummunan fushi da kuma bacin rai, daga nan babu wani jira juma ya saɓi sandan sa da addarsa ya wuce garin tudu acikin yayyafi, ya iso around 2pm dede na rana lokcin jikin inayan yafara rikicewa

likita ya fito yana kkrin ceto ranta da taimako da ake bayarwa na emergncy sabida sun riga sun gano cewa chronic appendix ne yake damunta gashi bayan ya girma harma yafara ruɓewa acikintan dolene kawai amata tiyata aciresa agaggauce.

tun bayan sallahn azahr suke cikin wann tashin hankli anata kkrin stablizing din inayah kafin ace zaa nemo motar da zai kaisu cikin birnin kano dan amata tiyatar nan agagguce gashi lkcin ana wani irin kwaxa ruwan sama me yawa da kuma tsawa

duk da zafin ciwo wasiyar hakuri da neman yafiya kawai inayah take nema awajen taawure da ayanah dan ciwon ciki takeji mei tsananin ciwo da bazata iya fasalta azabansa ba,

anata rububin nan ashema kudin tiyatan nasu bai cika ba, gashi taawure bata da waya haka tafita tabar ayana ajikin inayah ruwa na dukanta duk abun hawa sundauke da kafa ta dinga tafiya cikin sauri tay hanyar police station neman hajy mairo dan tabata aron sauran kudin tiyatan agaggauce..

ficewarta a asibitin bada jimawa ba Allah yay ma mijinta juma isowa har cikin asibitn da taimakon wasu matasa dake yawan zama daf da kofar gidan hajya mai tuwo dake zaman saka ido dama suke sune suka dada tabbatar masa cewa tabbas taawure da yayanta suxo amma sunbi hjy mairo sunje asibiti tun da jimawa

ransa a matukar dagule ya farabibiyar kwatancen asibitin tun abakin matasan dayake tambaya yaji kusab kowa ana cewa inayah gwarzuwan tudu, shi duk ya dauka gwarzancintan nan a karuwanci ne da tsabar iya bin maza baisan gwarzuwan karatun qur'ani suke nufi ba.

zcyarsa baki kirin ya diro cikin asibiti, daf lokci ciwon cikin nata ya tsananta sai nasiha take ma ayaanah akan karda tay rauni koda ta mutu bata duniyan nan ta tabbata ta tashi tsaye tazama wata jajirtcciyar mace snn ta mata alkwarin zata cika ma mahaifyarssu taawure bban burinta naganin sunyi ilimi sun zama mutanen kwarai.

tsabar kukan da sukeyi rikeda hannun junansu in an intense emotional state basuma san sanda juma ya shigo kansu ba.

ji kawai sukayi ana huci daga bayan su ankuma zaro katon sanda kmr za'a je yaqi a mugun zuciye yana huci yadaga sandan sama zai bugashi akan nurses din dake tsaye duk suka saka ihu suka bar dakin aguje ganin sa gabjeje babu wacce tay gigin taresa. dayaga haka sai girman kansa ya kara hautsina yafara dirin masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yabi ya haukata asibitin da zage zage

ayanah ta mugun tsorota, yadda kasan zucyarta zai fice daga kirjinta ya fice, amma haka ta cije ta ki sam tatashi ajikin inayahn tabi ta rungumeta tana kuka mai mugub karsashi wanda hakanne kawai yasaka bai kai musu dukan atare ba.

muryansa kamr zai tada asbitin yake kiran taawure kamr wani tabbabe yanamai zaginsu yanamai cewa inayahn karuwa tsinanniya kawai, yar bariki irin uwarta, yace wallh kinyi asara innari Ashe dama cikin shege kikayi kuke boyemin keda uwarki?? da yaren buzanci da fulatanci duk ya hada yana tsine mata dashi.

itade inayah kuka takey tana furta innalillah wa inna ilaihi rajiun....idonta a lumshe taki tace masa komi taki ta masa bayani bare ta bashi haquri..

..duk wani xafin xagi me tafe da amon muryansa dayake saukewa aknsu ji take kmr ranta yake zarewa dan zafi.

ayanah da tsabar tsoronsa ma bata iya masa magana ido da ido amma yau babu irin tsaurin ido da yaren da bata masa rantsuwa da bayani dashi ba.

tabi ta rungume inayah sosai tana kareta dagashi cikin kuka mai rauni, tanacewa baba ciwon appendix ne yake damun adda inayah ba cikin shege ba

hargagi yake ko ajikin sa kamar baijinta tanakan maganan ma ya ficokota ya tureta ya faffala mata maruka masu karfi, yaki sam yaji komi, shide yanaso ne ma yaga kawai ya gwada ma inayahn sandansa ya kashe ta,

dakyar likitan da wasu maza suka shigo suka samu suka rirrikesa snn aka kwace sandan daga hannunsa, ahakama sai zagin yaransan yakeyi kamar bashi ya haifesu, anfi minti ashirin ana wann hayaniyar da juma...

ayaanah ce ta fara jin daukewar numfashin inayah, ta mike da sauri jikinta na bari tayo kanta tun bata bude baki ba ahankli tajiyo kalmar shahadarta daya kufce mata abaki very faintly.,

akace wai duk inda malaikar mutuwa yazo sai iskan wajen yayi daban wani irin dimmm taji wajen ya dauke mata cakkkk, dan tunda tajiyo wnn numfashin ta na karshen taji kirjinta da jijiyon zuciyatta duka sun tsinke jikinta na wani irin rawa atake ta juyo sai kuma tazube aragwabe ajikin inayah tafara wani irin kuka mekara tana jijjigata tana kiran sunanta kamar tabbabiya..

da gudu likitan ya sake juma ya karaso wajen aka dudduba aka samu rai yay halinsa kowa yana furta innalillah aayana ta zube kasa tana kuka kamar ranta zai fita amma juma ko gizau baiji ba dan ya mugun tsanar asbiti da duk mutanen dake cikinta, anata batun yarsa ta rasu amma masifa yakeyi yana cewa sam cikin shege akazo zube mata tay mutuwar kafirci.

ran kowa saida ya baci a asibitin ko ajikinsa, shi mutuwar inayahn ma dadi ya masa gani yake data haifi shege agidan sa gara ta mutu, hakanan ya fizgo aayana waje, lkcin ana yayyafi sosai ya tsare adedeta ko ciniki baiyi ba ya cusata ciki yaciro igiyansa daga aljihunsa ya daure mata hannunta biyu da igiyan ajikin karfe ta cikin keke, snn ya koma ciki yanamai kara saukar musu da jakar balai yabi har kan gadon ya dauki gawan inayan akafadarsa, itama ya saka acikin keken, duka dashi da yaransa ya debosu agabansa suka kama hanyar garin majiya aganinsa sai ynxune ya cika namiji, snn zai nuna ma kowa tsananin jarumtarsa for once dai zaiyi abunda ya dace akan yaransa bisa tsarin al'adarsu ta kaka da kakanni dan martaban sa da kimarsa ya dawo.

lokacin ruwa aka farayi sabo kamar da bakin kwarya wanda shine yasaka har taawure bata samu abun hawan dawowa da cikaton kudin tiyatar data amso wajen haj mai tuwo akan lokaci ba

ko cikakken minti biyar juma baiyi da dauke yaransa ba ta iso asbitin wujiga wuijga kusab agigice jikinta yay jagwab da ruwa tazo musu da cikaton kudin tiyatar cass har tana haqi, tsabar tausayin data basu da kyar aka samu wata dattijuwar health worker data gaya mata cewa Allah yay ma inayahnta rasuwa snn gadai jahilci da haukar da ubansu yazo yay asibitin kuma ya tafi da duka yaransa gida ynxu

tunda aka fara mayar da maganan kusan kangare taawure ta suma daga tsaye har saida sukaga bata motsi snn aka bambamreta daga sudden shock din data shiga ciki aka samu itama bata ko motsi dan mummunn bugawa zuciyarta yay atake kuma ta suma aka bata gado ana kkrin reviving inta dan karta samu sudden heart attack due to shock.

tundaga hanya ayaanah take rabza kuka mai kara da karsashi, keken yana sauke su juma ya taso keyanta da haryanzu take rabza kuka kamar ranta zai fita wanda duk yawan ruwan nan da akeyi duk jejin saida ya dauka da karar kukanta, tanajin matsanancin tsoron abunda ke faruwa ga tsananin baqin cikin mutuwar addanta na dada gigita mata kwakwala tare da tsinka mata jijiyoyin zuciya..

sun iso gidansu babu takalmi akafara bare dankwali, haka juma ya turata akasa yabi ya kulleta adaki tareda gawan inayan snn ya fito waje ya wuce gari yakirawo mutane dan a masa shaidan binne yarsa da zaiyi bisa hukuncin al'adansu na kauyen, gashinan ruwa fa akeyi sama sama dake la'asr ya riga ya shigo ana neman kusan 4;45pm on dot amma hakannan magulmata da yan son ganin kwaf kwaf suka bazama yana bude kofar ya samu aayana tayita kuka harta sume tay karau ajikin gawar inayah dake dauke da fuskar murmushi.
Chapter 29 · 0% Book details