← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 113

Sashe 99

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jamal abu ba sauƙi kamar zai yi hauka cikin gidan ma an hanasa shiga bare ya samu daman ganin Juhainah.
Zarah kuwa jin shiru Yah Boss bai koreta ba tayi zaton an maidata ta miƙe ƙafa taci gaba da zamanta, shi kuma yabawa banza ajiyar ta, bata ma san baya ƙasar ba.

Surayya tana can tana jinyar rashin Juhainah, tafi son ta barta har ta fita daga shock ɗin da take ciki.
Dijeh kuwa ganin anyi haka Malam yace zai tafi da ita Mamy ta hana tace tasan halin Juhainah zata nemi yarinyar daga ta fita daga tashin hankalin da take ciki.

Ai kuwa haka akayi bayan sati 3 Juhainah ta warke ras ta fauwalawa ALLAH komai, damuwarta Yah Boss da akace baya gari sam batajin daɗin rashin nasa.
Ai kuwa randa ta cika kwana 22 da saki ta kafa rigima sai anje an kawo mata Dijeh ai amana Baba malam ya bata kuma tayi kewar Surayya.

Maah ta kira Surayya a waya ta faɗa mata, ta haɗasu.
Ai kuwa Surayya harda kuka, taba Mamy wayan.
Mamy jin yadda Juhainah ta gaisheta cikin girmamawa tace Surayya ta kawo mata Dijeh...

A ranan Dijeh gidansu Juhainah ta kwana.
Surayya ta sha mamakin yadda ba wanda ya sauya mata.
Ai kuwa Surayya ta samu damar zuwa gun Juhainah.
A cikin satin da Dijeh tazo gidansu Juhainah aka sakata a school ɗinsu Suhaima duk tsadarta.

Dan Juhainah da Fu'adh tayi magana akaje kayi wa Dijeh komai, aka zuba maƙuɗɗan kuɗi, Yah Boss yace a mata duk abinda take so ko baya nan.

Anyi rashin Sa'a Suhaima bata son Dijeh amma bata son ɓacin ran Juhainah haka ta barta, sai dai bata shiga sabgarta.

Malami na musamman aka ɗauka mata.
Juhainah ma ta koma makaranta cikin ikon ALLAH babu abinda yake bata wuya.

Ana wannan halin Ruwaida matar Mustapha ta haihu ta haifi mace wanda tsaf aka samu Juhainah kamar anyi kaki an ajiye.
Ai Juhainah Karku so kuka farin ciki a gunta duk da yanzu bata wannan shirmen, sai dai shagwaɓa halittarta ne.

Surayya murna kamar ta zubar ruwa a ƙasa ta sha. Lokacin da Juhainah ta koma makaranta duk da bagu ɗaya suke ba, amma idan Surayya suka tashi da wuri basu lecture da yamma, can school ɗin su Juhainah take tafiya, ta jirata su fito sai su taho.

Amma Sbd Jamal da security Juhainah take zuwa school, hakan kawai ya kawo mata sauƙi.

Har yau Juhainah bata taɓa ido huɗu da Jamal ba, shiyasa hankalinta kwance.
Shi kuma karatun ma yana neman gagarasa.
Hakan ya saka Abba ya canza masa gari aka maidasa Abuja.
Mamy da Abba suka ce idan bai je yayi karatunsa Abuja ba, zasu masa baki.
Hakan ya saka shi tafiya harda kukansa dan son Juhainah na masa azaba, duk ya fita daga hayyacinsa, dan ma yana ƙoƙari wajan istigfar.

Yau tsawon wata uku da kwana goma dai-dai da rabuwar Juhainah da Jamal.
Har yau Juhainah batayi period ba, kuma sam bata damuwa ba, Sbd wani lokacin daman tana wata biyu har ukun Sbd Jinnun jikinta suna mata wasan hakan.

Maah ta sani, itama bata damu ba, tunda tasan haka ƴarta take.
Amma hankalin Maah ya tashi, ganin irin farin da Juhainah ta ƙara ƙirjinta ya ƙara cikowa, bata jiki amma hips ya ɗan buɗe kaɗan, tayi wani irin kyau, ga shi Yanzu bata faɗa abinci sosai sai tea da bread salad, fruits, lemon tsami da sugar.
Ga wani irin fushi da ta tsira yanzu.

Abu ƙalilan sai tayi ta fushi tana bala'i.

Maah tsaf tasan cikin ne yazo da yanayin.
Farin cikin Maah ɗaya da babu laulayi sai na fushin. Ba zazzaɓi ba amai ba ciwon komai amma akwai saurin fushi, har gaba sai ta tsiri maka ba dalili.
Maah tana kallonta dasu Khairat, idan suna parlour, tunda ita tana gun Maah ne tunda suka rabu da Jamal.
Amma wani ikon ALLAH bata iya fushi da Maah da Papa, sai wani lokacin ayi masu shiru.

MAAH tana jin tsoron Juhainah ta san tanada ciki ta ɗaga masu hankali ta rasa ya zatayi.
Marata har ta taso kaɗan, kana kallon Juhainah a yanzu kasan ciki gareta tunda ya shiga wata na 4.
Kullum Maah sai tayi addu'a kar ALLAH ya ba wata ikon ganewa acikin ƙawayensu na school a tayarwa ɗiyarta hankali.

Maah cikin dibara ranan wata weekend takai Juhainah Special Clinic Janfar Dr Nafisa ta gwadata, result ya fito ciki wata 3 da kwana 18.
Ɓoye result tayi, tun hanya Juhainah take rigima gwajin me aka mata Maah tace tana zargin tanada shawara ne, amma Dr Nafisa tace batada komai.

Ai a ranan Maah bata kwana ba sai da ta tafi gidan su Jamal ta ba Mamy result.
Mamy harda kuka tayi na farin cikin wannan abun, yanzu ta ƙara imani da ALLAH iya wannan rabon ne ya saka aure tsakanin Jamal da Juhainah.

Abba da ya gani yayi farin ciki sosai yace amma baza a faɗawa Jamal ba, a rabu da shi yayi karatunsa a Abuja a nutsu, dan yanzu yadda yake son Juhainah idan yaji akwai cikinsa a jikinta an shiga uku.

Maah picture ɗin result ɗin ta turawa Yah Boss, yace taja ta faɗa gidansu Jamal Juhainah a barta har yazo ya kusa cikin sati me kamawa zai zo.
Sai lokacin Maah take faɗa masa ai taje ta faɗa masu result ɗin a gunsu, kuma sunyi farin cikin da bata taɓa zato ba.

Maah da kanta ta jawa Surayya kunne akan karta kuskura ta faɗawa Juhainah maganar ciki, ta barta a bata san tana da ba.

Zarah
Yau dai ta tabbatar ita da banza ɗaya a wajan Yah Boss, ta kuma san bai maidata ba.
Ganin zaman bazai mata ba, tunda yanzu ta fice lokacin da zai maida ta da baki, ta tattara ta tafi Jigawa cikin matsanancinyar damuwa, duk irin katafaren gidan da take ciki, taci mai kyau ta sha mai kyau Zarah ta rame tayi wani iri da ita

Hajjah Mama taji zafin abinda Yah Boss yayi, amma batace masa komai ba, haƙuri taba Zarah ta mata addu'a da fatan Alkhairi.

Fu'adh ya gama da wajan Zuby ganin Ammar ɗin ma yabar Juhainah.
Duk da yana labarin mutuwar aurenta.
Raudah ranan da labarin mutuwar auren Juhainah ta sameta tace shi kenan ai yaron nan ma ya biyata, tabarta taji da ciwon zuciyar sakin ma bayan kwana ɗaya da aure.
Ammar kuma har yanzu yana haƙon Raudah yace sannu² bata hana zuwa.



Yau ta kama weekend dukkan su suna gida, Maah ta fita maƙota bayansu anyi rasuwa.
Juhainah Khairat Suhaima Al'amin Dijeh.
Shirye-shiryen bikin auren Khairat ya fara Sbd gobe Yah Boss yake shigowa asabar mai zuwa za'ayi ɗaurin auren, ya haɗo laifi daga can na kece raini, Sbd shi a rayuwa babu abinda bazai yiwa Fu'adh ba.

Dan ko gidan da zasu zauna shine ya siya masa a gine gida mai sunan gida na kecewa Sa'a raini.

Juhainah cikinta ya cike wata huɗu harda sati ɗaya, yayi mata bala'in kyau, ya ɗan fito kaɗan, amman a haukata wai jiki ta fara, kuma tana nan fa a bushenta.

Sanye take da riga da skirt na atamfa, kanta sanye cikin hula, yanzu ta rage saka ƙananun kaya.
Idanunta akan Tv, Film take kallo.
Dijeh tana zaune kusanta tana mata surutu, sai ninniƙenta take.

Suhaima ta kalli Dijeh cike da kishin neman amshe masu Aunty, ta ɓata fuska tace.
"Ke! Dalla chan tashi ki bata gu kin cika ta da surutu ko bakiga kallo take ba?"

Dijeh tsoron Suhaima take kamar masifar.
Ai gum tayi da bakinta, tana harare ƙasa² tace.
"Yo ni anfini son my Aunti ne? Bana tashi toh"

Ta ƙarasa maganar can ƙasa².
Amma da yake Suhaima shegen ji gareta kamar macijiya, karaf taji.

Ai Suhaima ta miƙe tana isowa wa bataga girman jikin da Dijeh tafi ta ba, ta cakumo rigarta ta kwashe ta da mari, ta turota daga kujera ta faɗi saman Carpet.
Dijeh ta fasa ihu.

Sai lokacin Juhainah ta ankare ta riƙe hannun Suhaima tana faɗin.
"My Babie me ta miki? Yanzu my Babie bakya son abinda nake so?"

Dijeh tanajin haka ta fashe da kuka tana miƙewa ta rungume Juhainah.
Suhaima ganin kamar Juhainah tana son yin fushi tace.
"My Aunty J, bakiga ta takura ki ba? Kuma zagina take ƙasa² naji fa"

Dijeh zatayi magana tana kuka Suhaima tace.
"Wlh kina magana sai na naɗa maki mugun duka a gaban Auntyn sai naga kece jininta ko Ni. Kuma ki sakar min uwa ki koma gefe."

Ai Dijeh ta haɗe maganar tana ƙasa da kanta tana kuka a hankali, ta matsa daga jikin Juhainah.
Juhainah ta kamo hannun Suhaima ta zaunar da ita akan cinyarta ta rungumeta tana shafa bayanta a hankali tace.

"Ya isa my Babie kinsan kema Bazan iya haɗa soayyarki da ta My Amiin da wata ba, kufa jinina ne jinin Yah Boss ɗina"

Suhaima ta ƙanƙame Juhainah tana lumshe idanunta hankalinta ya kwanta, bata son duk wanda zai raɓi Aunty J matuƙar zaiyi ƙoƙarin raba su.

Juhainah ta ya fito Dijeh da hannunta.
Dijeh ta miƙe Juhainah ta kamo hannunta tana goge mata hawayen fuskarta, ta zaunar da ita kusanta tana jingina kanta a kafaɗarta.
Khairat dai dariya take masu.
Al'amin ma dariya yayi yana faɗin.
"Aunty J mai ya'ya..."
Dijeh dai sai turo baki take taso ace rungumar da Suhaima ta samu itane ta samu.


Washegari

Ta kama Lahadi

Yau an tashi da hadiri garin ko rana babu, amma shiru ba'ayi ruwa ba.

Can gidan Yah Boss Jamilu yanata girke² tabar Yah Boss.
Daman parlours da bedrooms na gidan kullum sai an gyara basuda matsala, ko da yaushe ƙamshi suke kamar suna gidan.
A can gidan Maah anata shiyar tarbarsa.
Juhainah ta sani amma tayi murus Sbd bai taɓa nemanta ba koda a wayan Maah ne, tunda yanzu batada waya, tana wajan sa, itama wannan karon ta kafe bazata nemesa ba.

Zuwa yamma gidan Maah ya cika da ƙamshin girki, da launin turarukan wutar da aka saka, A ɓangarensa na gidan.
Ana sallar Maghreb jirgin su ya sauka.
Chapter 99 · 0% Book details