← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 113

Sashe 83

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juhainah ta ƙurawa Suhaima idanunta tana jin ranta babu daɗi, sai dai ba yadda ta iya da ƙaddara shi kenan yanzu ba ita ba sake cewa Yah Boss tana sonsa hakan ya haramta gareta dan tanaji a cikin zuciyarta Yah Boss akwai dalilin da ya saka take masa son so, ba banza ba ALLAH ya jarabceta, dole sai ta bincika koda a ɓoye agun manyan malamai taji zaka iya yiwa yayanka uwa ɗaya uba ɗaya son da ita take wa Yah Boss, dan yayi yawa ya zarce na uwa ɗaya uba ɗaya, so ne ƙauna ce ta aure ba ta jini kawai ba, ƙaunarsa take da dukkan zuciyarta...

Surayya ta rangaɗa guɗa tana washe baki ta rungume Juhainah tana faɗin.
"Alhamdoulillah! Yau Ubangiji ya amince Aunty J ta zama matar yayana har abadan congratulations Aunty J I love you"
Juhainah ta saki murmushi tana rungume Surayya da Suhaima.
Dijeh ta washe baki tace.
"Alquran Antiya Jihinah kinga jama'ar da suka zo ɗaurin auren ki, hekace wata yal gumna..."
Juhainah tayi ƙamar dariya tace.
"Gwamna ake cewa ko Kice governor Dijeje"
Dijeh ta washe baki tace.
"Ahe ma nakusa gaya dai-dai gomna gobaveno"
Surayya ta zungureta tace.
"Ke dole sai kin faɗi abin birni ne, keda ko school baki taɓa ba"

Juhainah tace.
"Ki shafa mata lafiya zatayi karatu in sha Allahu, zan roƙi alfarma Malam yabar min ita Wlh sai ta zama abun alfahari, amma da sharadi Dijah zaki daina faɗa da ɓarna, dan Surayya ta faɗa min ɓarna kike da faɗa sosai, kina dukan ƴaƴan mutane."
Dijeh ta washe baki tace.
"Ƙwaranƙwatsi dubu na daina Antiya Jihinah ina sonki zan zamna gurunki nayi karatun ahe ma bakisan yada kike birgeni ba"

Juhainah tayi murmushi tana rungumeta tace.
"Nagode Ƙanwata Dijah."

Suhaima ta kalli Dijeh kallon irin na Yah Boss idan baka masa, ta taɓe baki ganin ƙatuwar baƙauya da jikin ƴan gayu kuma tuliya da ita, sai surutun tsiya.

Juhainah ta kamo hannun Suhaima tace.
"Babie Suhaima je amso min wayan Maah."

Suhaima ta beƙa mata wayar ta tace.
"My Aunt ba ga tawa ba, Yah Jamal zaki kira ne?"

Juhainah ta girgiza kanta ta amshi wayan tana faɗin.
"A'a gaskiya Yayana Daddy ki zan kira ince masa nayi fushi bai tayani murnar aure ba"

Surayya tace.
"Please ki barsa Aunt J anjima Wlh yana tare da baƙi zaki raba masa hankali a biyu"

Juhainah ta turo baki gaba bata dai ce komai ba, ta shiga gun messages ta saka numbersa da ta haddace akanta tana fara sakawa My Dadd love ya fito ta fara tura masa da saƙo.

*"🥺Hey My brother Habiby😭, nayi fushi baka kirana kace min congratulations Aunt Bilkisu mun aurar dake ba, kansa zanfi kowa murna na fara jin tayani murnar aure daga bakinka, Sbd kai Jinin jikinta ne kuma zaɓin zuciyata😭"*

Ta tura masa.
Lokacin Yah Boss yana rumfar hutawa wacce take da wani irin sanyi ga furanni sai ƙamshi suke.
Yana tare da baƙinsa an kawo masu Lafiyayyun abinci launi daban-daban.
Special Phone ɗinsa tayi vibration ta kawo haske ajiye gabansa, akan farin tablin da yake zaune akan kujerar.
Yana ganin sunan Suhaima yasan waye me aikin.
Wayan ya ɗauka a anutse ya buɗe ya shiga gun message ɗin.
Anutse ya karanta saƙonta, ya girgiza kansa ya tura mata amsa.

*"I have your phone with me, how should I send you the message Aunt Bilkisu?
Congratulations May Allah bring you goodness and peace, Aunt Bilkisu the bride"*

Juhainah tana ganin saƙo ya shigo ta buɗe ta karanta tana murmushi, ta goge hawayen da suka fara Zubo mata, ta tura masa.

"Aameen Yah Boss My blood thank you, yau bazan dameka ba, kana tare da baƙi Please ka kula da kanka kaci Abinci sosai ka kwanta da wuri ka huta, yau ka gaji sosai.
Amma Please ina son naji muryanka a matsayin ɗan uwana karka hanani My blood na kira ka yanzu ?"

Yana ganin saƙon bai buɗe ba ya maida hankalinsa gun baƙinsa, suna tattaunawa dan akan yau duk zasu bi jirgi da yamma su koma.

Har tsawon mintina 10 Juhainah tana jiran amsar Yah Boss bai maido ba, sai juyawa wayan take, ta gaza jurewa ta miƙe ta shiga bathroom dan kar su Surayya su mata faɗa ta dame shi.

Tana shiga ta danna masa kira.

Yana tsaka da magana da baƙinsa kiran ya shigo.
Sai da ya kusa katsewa yayi picking call ɗin ta Glass idanunsa.

A hankali ya furta.

"Why are you worried Bilkisu?"

Wani irin marayan kuka ta sakar masa a hankali yadda bazai fita sosai ba, cikin kukan tace.
"My brother Habiby tambaya kake me yasa na damu? Ni Ba ni da irin zuciyarka, kamin addu'a Allah ya bani irin zuciyarka, nasan zan zauna lafiya.

Me yasa baka tausayi na? Me yasa baka bani mahimmanci a acikin rayuwarka? Me yasa kake ɗaukan komai nawa shirme? Me yasa nake maka wannan soyayyar? Me yasa nake jin zan iya bada rayuwata akanka? Wlh Yah Boss zan iya mutuwa saboda kai.
Kaine ka sakani wannan auren bana sonsa Wlh bana ƙaunarsa Bazan...."
Katseta yayi yana miƙewa yabar rumfar.

"Bilkisu! Calm down, Please be quiet, stop crying, it's enough."

Shiru tayi tana goge hawayen fuskarta.

A hankali ya furta.
"Thank you My sister, Karki sake kuka Kinji?"

A hankali tace.
"Naji Yah Boss jinina."

"Yanzu me kike so nayi bayan Kinsan uwar ɗaya uban ɗaya? Please ki rufa min asiri, Kinsan yanzu kalaman ki haɗari ne akwai aure a kanki? Kiyi haƙuri ki zauna lafiya da mijinki, wannan alfarma nake so kiyi min Ƙanwata idan dai kina sona da gaske Please"

A hankali tace.
"Shi kenan nayi Sbd kai"

A hankali ya furta.
"Thank you so much My sister, bye ina tare da baƙi"

A hankali tace.
"Bye My blood Habiby, ka kula da kanka Please."

A hankali ya furta.
"I promise you that my sister, Bye."

Cikin farin ciki tace.
"Nagode my blood bye"

Ta ƙarasa maganar ta katse kiran ta fito fuska kame Sbd kallon da suke mata, bata son kowa ya mata magana a wannan lokacin, Sbd zafin da zuciyarta take.


Alhamdoulillah! Biki yayi bikin ya wuce duk yadda zan zayyana Sbd tsayawa zayyanawa ɓata lokaci ne zaici waje ne, amma kam gaskiya anyi bikin Autah.
Da yamma bayan sallar la'asar akayi walima, wa'azi mai ratsa zuciy Maah ta kawo Juhainah ta zauna taji sosai kuma da gaske jikinta yayi sanyi harda kuka tayi, gudun kar ciwonta ya motsa ta kamata suka koma ciki, Umma Hanifah kuwa jikin ba sauƙi, dan tana fara jin wa'azin Malama Jiddah ta tsame tabar gurin wai kar a karya mata da zuciya.

Ko gidansu Jamal Alhamdoulillah bikin ya masa sunansa bikin ba ƙarya.
Suma walimar maza da mata akayi wanda Mamy ta matsa masa sai anyi dole akayi abun kuma ya ƙayatar dan jikinsa yayi sanyi ba kaɗan ba.

Yah Boss bai nutsu ba sai da baƙinsa suka tafi.
Sai yamma sosai yabar gidansu MAAH ya tafi, ya kira Suhaima take faɗa masa tabi uncle Mustapha sun tafi gidansa, bazata jure ganin tafiyar Aunt J ba.
Bai ce mata komai ba, ya nufi gidansa yayi wanka ya nufi masallaci Sbd Maghreb ta yi.

Juhainah kaiwar dare za'a mata gidan miji.

Bayan sallar isha'i aka shirya Amarya Juhainah cikin shigar kece raini, dan tafiya gidanta na aure.
Maah haka kawai ta gaza mata nasiha mai tsayi, Sbd kukan da take ji yana shirin zuwar mata.
Haj Lubnah ƙanwar Maah da haj Jamila and Karimah su suka yiwa Juhainah nasiha sosai, sai Hajiya Mama da Aunty Sumy.
Juhainah da gaske kuka take kamar ranta zai fita, ta ƙamƙame Maah.
Maah ta ɗagota tana faɗin.
"Muje Papanki na jiranki kafin masu ɗaukan amarya su iso"
Daƙyar Juhainah ta miƙe Maah ta riƙe ta suka fito zuwa bedroom ɗin Papa.
Aunty Sumy tabi bayan su.
Papa yana zaune a parlour sa suka shigo Maah tayi sallama.
Papa ya amsa yana kallon su yace.
"Oyoyo Autar Yakubu Abubakar Janfar, Yau dai tilon Autar Yakubu ta girma"
Ai Juhainah shagwaɓa ta motsa ta saki Maah ta nufi Papa ta faɗa jikinsa ta saki kuka abun gwanin tausayi.
Papa ya rungumeta yana buga bayanta yace.
"Yi haƙuri Auntynah Bilkisu, yaƙin mata da kikayi, muma dole ne ta saka zamu rabu dake, amma nayi miki alƙawarin har gidanki zanje na dunga duba lafiyar ki.

Abinda nake so dake kiyi haƙuri ki zauna da mijinki da iyayensa da ƴan uwansa lafiya, ki masa biyayya Sbd aljannar ki tana ƙarƙashin ƙafafunsa, don Allah Autah Karki bamu kunya, nasanki da tsafta da addini daidai gwargwado toh ki linka, kiyi hƙr kiyi hƙr don Allah kar a samu fitina daga gareki, dukkan abinda ya saka ki wanda bai saɓa wa Shari'ar addinin musulunci ba toh ki masa biyayya don ALLAH, kinga nida mahaifiyarki baki taɓa jin kanmu ba, toh kiyi koyi da ita Please Autata..."

Juhainah cikin kuka tace.
"In sha Allahu Papa nayi maka alƙawari Bazan baku kunya ba, ku yafe min duk rashin jin da nayi ta muku da ɓata maku rai da nayi ta yi akan ƙin karatu, in sha Allahu zanyi karatu yanzu sai kunyi alfahari dani, zan zama yarinyar kirki, nayi maku wannan alƙawarin. Zan masa biyayya har tsayuwar numfashi na na ƙarshe, Bazaku taɓa samun damuwar zaman auren da zan tafi ba."

Maah hawaye ya silalo mata akan fuskarta ta faɗo jikin Papa ta rungumeshi tare da Juhainah ta saki kukan da ta gaza riƙewa.
Aunty Sumy ma kukan ya kuɓuce mata, Khairat ma da ta shigo ganin mahaifiyarsu tana kuka itama ta fara.
Juhainah ta ƙara sautin kukan nata.
Papa ya haɗa Maah da Juhainah ya rungumesu yana faɗin.

"Nasan sai kinyi hakan duk nasihar dana maki bakiji ba jiya Zainab? Toh yanzu wa zai lallaɓa wani keda ƴaƴan naki kin saka su kuka?"
Daƙyar ya samu sukayi shiru.
Haj Lubnah da Hajiya Mama suka shigo suma harda hawayen su, Papa duk ya masu nasiha ya samu daƙyar ya lallaɓa Maah da Juhainah suka ƙyale yana masu nasiha, mai ratsa zuciya wanda wanda hakan yayi tasiri a zuciyar Juhainah...
Chapter 83 · 0% Book details