← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 113

Sashe 4

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jamilu ya washe baki yana faɗin"Eh kaida kasan Sir ko ince kaine ma kake kawo ma komai, akwai magani kala² mun gode Allah ya ƙara rufa asiri ya ƙara buɗi, idan kuna sha'awar ƙarowan ba matsala amma ni kaɗai zanji da komi iya abincin Mutanen bamu ƙarasa cika goma ba, bazai gagara ba sai dai saboda jiki da jini, ƙarowan ba laifi."

Ya ƙarasa mgnar yana juyawa ya nufi hanyar da zata kaisa kitchen.

Fu'adh ya sauke numfashi yace."Za'a karo ɗaya saboda hakan ai, sai ka dinga samun hutu sosai."
Jamilu ya yi godiya yana wucewa.

Hanyar da zata kaika Stairs abin kallone saboda yadda aka ƙawata ko ina da wani irin kwalliya a jikin kowane bangon.

Wasu irin Steps masu masifar kyawu suna ɗaukan ido idan Kanada mugun tsoro bazaka iya hawa Stairs ba dan ka iske asalin ɓangaren Yah Boss.

Wata ƙoface rufe mai shegen kyau, tana kallon yamma, yayin da wasu kofofin guda biyu suke kallon Gabas wato suna kallon ƙofar da tafi ɗaukan hankalina.
Ba ɓata lokaci na buɗe a hankali na shiga bayan nasha wuya wajan buɗe tan Wani tsararren parlon yanada girma.
Wani mayen ƙamshi da sanyi Ac yake tashi a gurin, wasu manyan Sofa ne a parlon masu numfashi, idan banyi ƙarya ba sai nace komi na falon Sama yaso fin na ƙasa kyau duk kuwa yadda aka narkawa can ƙasa kuɗaɗe miliyoyi.

Nan ma wasu irin kalar frame ne kowane kusurwan bango nan ma kalar tsarin yadda suka ɗauki hoton daban dana falon ƙasa.
Anan har sunfi kyau nan ma ko ina suna rungume da ƴaƴansu biyu cikin so da ƙauna.
Wata ƙofa ce mai shegen kyau handle ɗinta ma abin kallo ne.
A hankali na buɗe ƙofar na shiga.

Ma sha Allah
Master bedroom ne nan ma akwai wasu irin lafiyayyun Sofa masu kyau da taushi, wani irin sansanyan ƙamshi mai sanya kwanciyar hankali da nutsuwa yake tashi ga sanyi Ac da ya haɗa da ƙamshin ɗakin ya bada wata irin kalar ƙamshin sanyin daɗi.

Wani irin faffaɗan bed ne wanda ya kusa cin rabin bangon, komai na ɗakin ya haɗu ya tsaru, kana kallon ƙaton Italian bed ɗin kasan ba na ƙananan miliyoyi ba, quilts ɗin ma da suke shinfiɗe saman bed sun isa su saka shagala da kallon tsarin.

Komai na ɗakin Brown ne har Carpets ɗin da suke kwance ƙatuwar bedroom ɗin, babu wani abu da ba kalar Brown bane cikin ɗakin.

A master bedroom ɗin ma akwai ƙaton frame ɗinsu a bango sai wani wanda matar ita dayace an ajiye frame ɗin akan bedside tana sanye da riga da wandon Pakistan kalar da mijinta yafi so wato Brown colour.

Ta yane fuskarta da ɗan mayafin kayan tana dariya, fararen haƙoranta sun ƙarawa hoton kyawu.
Wata ƙofa aka buɗe wadda take nuna bathroom ne.
Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan halitta.

Farin ingarman namiji dogo mai faffaɗan ƙirji jikinsa duk a mirɗe irin ƙirar ƙarfafa, kana kallonsa kaga cikakken namiji, mai ji da kyau da Asalin masu gidan rana.
Shekarunsa na haihuwa 42 a duniya, hakan ne ya saka yake da wani irin farin jini birni da ƙauyika ganin matashi commissioner ƴan sanda ga shi ya jajirce akan aikinsa babu sassauci idan ka shigo hannu kanada laifi.
Amma kana kallonsa saboda hutu da jin daɗi kyan fata zaka zaci bai fi shekaru 34 zuwa da 35 saboda sam shekarunsa basu nuna ko kusa ba, shiyasa ake alfahari da ganinsa matashi a matsayin shugaban ƴan sanda, idan ka kalli Suhaima yadda take da saurin girma bazaka ce ya haife ta ba.

Ɗaure yake da towel iya ƙugunsa mai ɗan faɗi, jikinsa na ɗigar da ruwa, ƙamshin jikinsa wanda yake tashi na gel ɗin da ya gama wankan, sai yake ba ɗakin wani irin ƙamshi da ya gauraya da ƙamshin ɗakin.Ɗan ƙaramin towel ne a hannunsa yana goge jikinsa mai cike da gargasa.

Fari ne tass mai dogon hanci manyan fararen kyawawan idanu, masu wani lumshe, bakinsa ƙarami jajir da shi, alamar jin daɗi ya gama sun gina zama, yanada gashin girar ido gazar² haka gashin gira kamar shi yayiwa kansa, haka sumar kansa Allah ne ya basa tamkar haihuwar India haka gashin kansa yake, duk da yana yawan aski amma idan busy ya ɗau hankalinsa baiyi ba, sumar na saurin tasowa.

Yanada dimple ɗaya gefen dama yayi wani irin loɓawa kome yake gurin sai ya loɓa cin abinci ko magana ko dai motsa bakinsa yayi ramin sai ya fito kamar yana murmushi ko dariya, abinda yake wuyar gani kenan, duk da yana murmushin idan ta kama.
Gaban ƙaton madubi ya tsaya wanda ke cike da turaruka da maiyukan jiki dana gashi kala².A gaggauce ya gama shafe-shafensa ya gyara sumar kansa da take samun wani irin gyara da tsadaddun maiyuka da turaren gashin.Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halittar nan, lokacin da na gansa ya saka Uniform ɗin police, na commissioner an Rubuta sunansa ɓaro² Abubakar Yakubu Abubakar Janfar.
Wani irin mugun kyau Uniform ɗin tai masa abunka da tsayayyen namiji maijin kyau da ƙarfi da tsayi, kana kallonsa sai ka sake kallonsa tamkar Balarabe haka ya fito cikin Uniform ɗin, abinka da farin mutum tass, sai dai fuskarshi babu wata walwala duk da babu fushi akan fuskar ta shi.

Tsadaddun turarukansa ya fesa yana duƙawa ya saka takalmin wanda ya ƙarasa fito da kyawunsa, ya ɗaura agogon da tsaya wa faɗin tsadar ta ɓata lokaci ne, amma ko hasken da take a tsintsiyar hannunsa ya isa kasan bata ƙananun ƙuɗaɗe bane.
Yatsotsinsa na hagun sai sun baka sha'awa saboda Rings ɗin diamond da gold ɗin da suke hannunsa har guda 3.Wayansa da ta zama special wadda iya family Janfars kawai yake anfani da ita.
Lumsassun fararen idanunsa ya ɗago yakai akan wayan da take ajiye akan bedside.
Kamar ya tuna wani abun yayi saurin nufar wayan da wani irin daddaɗan sauti a hankali ya furta.

"Oh My God! I feel like this girl is a hypocrite and doesn't go to school Let me call Maah."
Ya ƙarasa mgnar yana ɗaukan haɗaɗɗiyar Samsung ɗin yana ɗauka ya nufi hanyar falo yana wani irin taku mai tsayawa a rai.
Number Maah ya kira tana Ringing ba'a ɗauka ba. Idanunsa masu haske ya kai kan hoton kyakkyawar balarabiyar matarsa wadda mutuwa tayi masu yankan ƙauna ta raba su.

Lumsassun fararen idanunsa ya zuba mata babu ko ƙiftawa yana jin bugun zuciyarsa na tsananta akan azababbiyar ƙaunarta a hankali ya iso bedside in ya rusuna ya sanya farin tattausan hannayensa ya ɗauko frame ɗin ya sumbaci goshinta ya saita jajayen lips ɗinsa akan nata pink lips ɗin ya ɗora bakinsa yayi kissing bakin nata da take dariya a hoton.
Rungume frame ɗin yayi na tsawon minti 2 ya maidasa gun zamansa ya miƙe tsaye yana kallon kyawawan ɗiyansa Suhaima da Al'amin.
Tausayin yaran yake ji mutaƙa na rashin nagartaciyar uwa da sukayi, hakan ya saka yake ji har abada bazai sake ƙara aure ba, zai kula da ƴaƴansa ya basu tarbiyyar su samu ilimin addini dana boko har sukai ga aure, sanin kansane ya'yansa basu da wata matsala tunda suna gidan iyayensa, ga kulawar ƙannensa ga kulawar iyayensa ga Nanny's ɗinsu Halima da Amina.

Falon ya fito a nutse yana kallon Mas'ud da yake ƙara gyara parlon, kafin ya shiga bedroom, duk da babu wani datti.
Gaishesa yayi cikin girmamawa.
Yah Boss ya amsa yana danna number Papa ya buɗe ƙofar ya wuce dan sauka downstairs.
Bugu ɗaya Papa ya ɗauka tare da sallama.
Anutse Yah Boss ya amsa yana gaishe da mahaifinsa cikin girmamawa tare da tambayarsa.
"Papa! Ina Maah?"
Papa yace.
"Tana sama Auta bata fito ba taje tashin ta ne, ya gajiya da aiki Abbah?"
Yah Boss ya lumshe idanunsa masu haske yana ɗan jan numfashi ya saita nutsuwarsa a hankali ya furta.
"Am fine Papa, ya ƙarfin jiki? Ina Khairat taje school ɗin ita? Nasan dai my Babies sun tsufa a school."
Papa yayi murmushi na jin daɗin babban ɗansa yadda yake kulawa da ƙannensa sosai ba kamar Auta da batajin magana, matsalar dukan da yake mata ne baya so, saboda ba wata tsoka ne da ita ba.
A nutse Papa yace."Ai ta tafi tuntuni su Suhaima ko ai kasan basa makara basa son shirin Halima ko Amina sai Mom ɗinsu Khairat.
Autah ma inaga batajin daɗi Bari dai Maman naku ta fito mugani ko na kai mata wayan can...?"
Da sauri Yah Boss da yake taka Steps da sauri² ya furta."No Papa zanzo yanzun ai."
Da hira ya fara jan mahaifinsa a nutse yana sauka.Tuntuni Fu'adh ya shaƙo mayen ƙamshin Yah Boss, hakan ya sanar da shi fitowar sa.
Rufe laptop ɗin yayi yana ɗago kansa yana kallon hanyar Stairs ɗin duk da bai ɓillo ba.
Har ya gama saukowa magana yake da Papa.
Yana isowa tsakar falon ya kalli ɓangaren da Fu'adh yake zaune.
Kallon da ya masa har ya gane fita zasuyi ba maganan zama yin breakfast, dan ya gane da mahaifinsa yake waya ganin yadda ya bada nutsuwa gun magana.
Miƙewa ya yi ya kwashi wayoyinsu ya gyarawa laptop zaman kan table in ya biyosa, yana danna waya ya kira Walid yana bada umarnin motar da za'a fito dan fita da ogan nasa.
Kafin su iso compound in gidan Walid ya cika umarnin Fu'adh.Kasancewar su masu Arziƙi Yah Boss babban ɗan kasuwa ne, da duniya ta sansa ba wai ya tsaya iya aikinsa bane, shiyasa Ubangiji ya ƙara ɗaukakasa duk tarin dukiyar da garesa baya wulaƙanta na ƙasa da shi, matuƙar ba kaine ka shiga hurimin shi ba.

Wata haɗaɗɗiyar jibgegiyar mota Black aka fito da ita an gogeta, sai sheƙi take yi.
Yana fitowa ma'aikatan gidan suka fara gaishesa har security's.
Hannu yake ɗaga masu saboda yana amsa waya.Tun bai ƙarasa ba Walid ya buɗe masa bayan motar.
Yana isowa ya shiga tare da Bismillah ya zauna har zuwa lokacin wayan suke da Papa wanda ya jefo masa maganar auren da suka gama hira shi da yayarsa Bilkisu, akan bazai zauna haka ba shekara biyu da mutuwar matarsa amma yaƙi ko bada fuskar da za'a yi masa maganar auren.
Kansa ya jingina jikin allon kujeran motar, yana ɗan lumshe idanunsa masu haske da lumshewa tamkar yanajin bacci.
Chapter 4 · 0% Book details