← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 113

Sashe 111

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai Aunty Sumy bata san lokacin da fasa ihun farin ciki ba, harda taka rawa daman tsaye take gaban Khabir mijinta yana shirin fita kasuwa.
Riƙeta yayi yana dariya yace.
"Honey ya dai?"

Rungumeshi tayi tana faɗin.
"My Honey Autah Bilkisu ta haifa mana ƴan biyu, mata."

Khabir yayi mata addu'a yace.
"Ah Honey taka rawa gaskiya.
Muje na ajiyeki asibitin, koda motarki zaki fita?"
Sakinsa tayi tace.
"A'a muje Honey ka ajiyeni"
Shirya wa tayi ta shirya little Sadiq suka tafi.

Khairat ta zauna kusan Maah ta kira Surayya.
Lokacin Surayya tana school, da yake tanada number Mamy ta kirata.

Mamy tana ɗauka tayi sallama Khairat ta amsa ta beƙawa Maah.
Bayan sun gaisa da Mamy ta bata Labarin haihuwa.
Ai Mamy tsabar murna kukan farin ciki ta saki, tana faɗin.
"Alhamdoulillah! Allah kaine abin godiya gamu nan zuwa"

Mamy suna sallama da Maah ta kira Abba ta sanar da shi, ta kira Wasila ta faɗa mata ta kira, Abdulkarim da Nazir ta sanar dasu.
Kowa murna yake, Ance abar Jamal sai ana jibi suna.
Abdulkarim shi yazo ya tafi dasu Mamy dan shine matsayin uban tunda mahaifin Babies baya nan.

Juhainah ana gama mata ɗinki aka shiga danna mata mara jini na fita.
Nan ma wata irin azaba taci, haka ta jure.
Baby's an gyara su tsaf an saka masu kayan sanyi ɗaya pink ɗaya blue tunda ba'a san Twins bane, ba'a siyi iri ɗaya ba.

Maah tunda aka kawo mata yaran take kallon su haƙiƙa juhainah tayi ƙoƙarin fito da wannan yaran ma sha Allahu.

Cikin awa biyu asibitin sai Ma sha Allahu, iyalin Kawu Nasiru ma sun zo, Haj Lubnah tana nan aka fito da Baby's.
Su Haj Jamila and Karimah manyan ƙawayen Maah, sune bayan an fito dasu suka iso.

Mamy baki yaƙi rufawa tana rungume dasu,tace.
"Wlh dukansu Jamal ne basu yiwa Ɗiyata Bilkisu kara ba"

Abdulkarim yace.
"Kawo su ayi masu addu'a da huɗuba, Abba wani suna za'a saka masu?"

Abba yana murmushi yace.
"Hassana da Hussaina, ai har na raɗa masu sai dai ka tisa, abarmasu halattaccen sunansu"

Abdulkarim ya amshesu cike da sha'awa ya masu addu'a ya sake masu huɗuba a kunnuwansu, da Hassana da Hussaina.

Kowa amsar Baby's ɗin yake.
Maah gun ƴarta ta tafi.
Bacci take na wuya an saka mata drip.

Yah Boss bai samu zuwa ba sai bayan sallar juma'a.
Lokacin Maah har ta yiwa Juhainah wanka taci farfesun hanta da ƙoda, tasha magani yaran basu samu ruwan Nono ba, har yanzu baizo ba, haka ta koma bacci.

Ai su Suhaima suna zuwa daga school sai asibiti.
Surayya ma kamar tayi hauka dan murna ganin ƴaƴan nata, ai kuwa ko motsin yara bata so tana manne dasu.

Sai dare aka saki Juhainah, cikin ƙoshin lafiya ita da ƴaƴanta.

Kowa yazo banda Hanifah tunda bata sani ba.
Khairat sai bayan da suka koma gida Fu'adh yazo ya ɗauketa, suka tafi gidansu tana masa santin Baby's ɗin, yana mata dariya yace zai bata ita ma...

Bedroom ɗin Maah aka shimfiɗa mata katifa ƙatuwa.
Yaran kuwa wasu gadaje ne biyu masu masifar kyau da tsada, Yah Boss ya saka aka kawo da katifar su, da Net.
Suna dawowa Maah ta mata kunnun kanwa, tasha ba laifi.
Ruwan Nono ya fara zuwa kaɗan².
Yanzu ma zaune Juhainah take, Maah zaune kusanta riƙe da Hassana tace.

"Ɗaga riga Autah kiyi haƙuri tasha alamar Hussaina zata fita haƙura kalli yadda take suɗar baki."

Juhainah batace komai ba, ta janye rigar tata, ma sha Allah mutanan tsaye ƙyam kamar bata haihun ba.
Fara shayar da Hassana tayi tana kafeta da ido.
Bataji daɗin kamar yaran da Jamal ba, taso ita suka biyo, ko cikin danginta.
Daɗin abun ma da Surayya take kama dasu.

Surayya tana riƙe da Hussaina tace.
"Maah duka haƙuri garesu yunwa dai suke ji yaran kirki"

Maah tayi murmushi tace.
"Ai Ni kam daughter Surayya Bazan ga kirki kishiya ba, kinaga Harɗo har ya fara yabawa"

Surayya tayi dariya ƙasa² tace.
"Maah Abba ma fa haka yayi Mamy tace ai kuwa bazata yarda ba kishiya har biyu da tsufanta"

Maah dariya tayi tana miƙewa tace.
"Daughter Surayya wannan ƴan mata zamu ɗauki matakai akansu, bari naje na wanke sauran kayan can na mejego. Ya Nasir shiru mijin naki ba'a samunsa bawan ALLAH? Wajan wata nawa"

Surayya taji kunya ta sadda kanta bata iya cewa Maah komai ba.

Maah tayi murmushi tace.
"Kefa ɗiyata ko a baya babu kunya tsakanin mu"

Maah tana fita Surayya ta matso kusan Juhainah, tana kallonsu.
Juhainah ta shafe fuska da toka tana faɗin.
"Miye?"
Surayya ta danne dariyarta tace.
"Yi haƙuri Aunty ba komai"

Dijeh ce ta shigo da gudu ta faɗo saman katifar tana zama kusan Juhainah tana washe baki tace.
"Aunti zan dinga raino randa babu makaranta, Wlh Aunti kamar bake kika haifa ba Babyn ƙatunane, masu kama da Jamal..."

Juhainah tace.
"Naji tashi ki fita Dijeh bana son Surutu yau, kije dare ma yayi ki kwanta"

Dijeh akwai jin maganar Juhainah ta miƙe tace.
"Aunti sai da safe"

Kai ta ɗaga mata azabar tsotsar da Babyn take mata ma ya ishe ta.
Surayya tace.
"Ai fa wannan mai Shegen kaudin kinada aiki."

Juhainah tace.
"Ba dai ruwanki, amshi Hanan, kawo Sameeha, Wlh zafi tsotsar."

Surayya ta amshi Hanan ta beƙa mata Sameeha, tana faɗin.

Sunan yayi daɗi.
Hanan Tausayi, Sameeha mai yafiya, wow!"

Juhainah a hankali tana runtse idanunta yadda Sameeha take tsotsarta akwai zafi, a hankali tace.
"Ai yafi a dinga kiransu Hassana da Hussaina a dai barsa a sunan yankan"

Daddaɗan ƙamshisa ya kawowa bedroom ɗin farmaki.

Kafin su waiga sai Sallamar sa sukaji cikin kamewarsa.
Juhainah taja hijabi ta rufe ƙirjinta da ƴarta.
Surayya ta amsa sallamar tana gaishesa cikin girmamawa.
Ya ƙaraso ya zauna saman Sofa yana amsa gaisuwar Surayya, kasancewata surukarsa.

Miƙewa Surayya tayi, da Babyn rungume da ita, ta kaita ɗan gadonta ta kwantar da ita, ta saki Net ɗin.

Fita tayi taja masu ƙofar ta koma parlour dan ita kam ta ƙauro sai bayan suna daga nan zata dinga tafiya school.

Juhainah juya masa baya tayi, Sbd kunyar da taji.

A hankali ya furta.
"Juyo muyi magana bana son wannan rainin hankali naki, kin sauka lafiya Alhamdulillah!"

Cikin tsiwa tace.
"Bana juyowa, ai muna iya maganar da zamu yi a haka"
Miƙewa yayi anutse ya nufi katifar.
Gabanta ya tsaye.
Lumsassun idanunsa ya kafe a kanta.
Kanta ta kawar tana hawaye.

Gabanta ya duƙa ya saka yatsun sa biyu ya ɗago haɓarta.
A hankali can ƙasa ya furta.
"Kina jin kunyata ne Sbd kina shayar da Babyna?"
Idanunta ta saka cikin nasa.
Fuska ta haɗe tana janye idanunta ta turo baki gaba, batace masa komai ba.

Ai wata irin zuƙa Sameeha ta mata, tayi saurin damƙe hannunsa tana ciza laɓɓanta, a hankali cikin shagwaɓa bata san ta masa ba, tace.
"Wayyo Yah Boss zafi sosai"

Murmushi yayi yana janye hannunsa ya ɗago fuskarta a hankali cikin raɗa ya furta.

"Ki jure banson ragwanta, haka Maah ta sha wuya kinada azabar tsotsa, shiyasa kike da ci kamar Gara.
Wannan Baby's ɗin nawa sai sun rama wa Mahaifiyata"

Ya ƙaransa maganar yana shafo hawayen fuskarta, a tafin hannunsa, miƙewa tsaye yayi, ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa.
Kallonsa tayi zata masa magana cikin tsiwa har ta mele baki, ya watsa mata wani irin kallon da ta gaza gane kalarsa, taji faɗuwar gaba tai saurin kauda kanta.
Hanan yaje ya ɗauka ya mata addu'a ya sumbaceta, ya maida ta ya kwantar ya miƙe.

A hankali ya furta.
"Bye good night tunda bakya son gani na"

Bakinta gum har ya fita bata iya sake masa fitsara ba, ko maganar ma, dan kallon ya gama kashe jikinta baki ɗaya.



Yah Boss tunda ya tafi bai sake samun dawowa ba, sai ana jibi sunan koda yazo bai je inda take ba, an kawo masa yaran dai ya masu addu'a, da pictures yana son yaran sosai.

Kamar yadda Mamy ta faɗa sai yau ana jibi ta karasa.

Abuja
Jamal zaune yake a parlour yana duba wani BOOKS Sbd sun kusa fara jarabawa.

Sanye yake da ƙananun kaya, yayi kyau sosai sai dai ya ɗan rame.
Fuskarsa kamar kullum ba walwala.
Bai fi mintina ashirin da zuwa daga makaranta ba.
Wayarsa ta fara ringing.
Kallon wayar yayi ganin Mamy ce ya ɗaga tare da sallama.
Mamy ta amsa tana faɗin.
"Albishirin ka Jamaluddin?"
A hankali yace.
"Goro Mamy"

Mamy tace ka Nutsu ka saurari labarin da zan baka..."

Labarin cikin Juhainah da ɓoye masa da sukayi har zuwa haihuwar ta ta basa.
Wani irin ihu ya fasa na farin ciki sai ga hawaye yace.
"Mamy nine nake da ya'ya har biyu Juhainah kuma ta haifa min?
Alhamdoulillah ALLAH shine abin godiya, astagfirullah Wa'atubu ilaikh Ubangiji na tuba ka ƙara yafe min Kura-kuran dana aikita maka."

Mamy tace.
"Jamal an girma sai ka fara shiri gobe kazo jibi ne sunan...."

Sun daɗe suna hira Jamal a daren bai runtsa da idanunsa ba, murna ta hanasa bacci, yaje ya nemi izinin tafiya a makarantar su, an basa kwana uku kaɗai shi ma dan shine uban yayan.

Washegari gidan Maah ya kacame da jama'a ƴan uwa da abokan arziki ma sha Allahu.

Juhainah an mata ƙunshi mai masifar kyau da kitso a dogon gashin ta tayi bala'in kyau.
Haka Surayya anyi kitso anyi ƙunshi ga ankon da zasu saka gobe.

Narka narkan raguna aka kawo gudu uku daga gidansu Jamal, biyu na Twins an yankawa Momynsu taci ta mora.
Ɗaya wanda za'a saka a miyar abincin biki.

Hanifah baki sake bata san komai ba, dan tunda akayi wannan abun tayi fushi bata taɓa zuwa gidan Maah ba.

Bayan sallar Maghreb tana zaune a parlournta, kamar Ance ta kunna data ta shiga WhatsApp, tana shiga ta dinga ganin status yana yawo.
Na Aunty Sumy ta fara dubawa.
Da sauri tace.
"Jakar uban nan, Juhainah haihu aka rasa dan buro uban da zai gaya min a dangi. Kai Zuri'ar Maah anyi tsinannu, ƴan asara, ai kuwa sai naje goben shegu masu mugun hali"

Kashe wayar tayi saboda takaici ta miƙe ta nufi bedroom dan ta zaɓi kayan da zata kece raini dasu gobe agun bikin Juhainah.


Misalin ƙarfe ta da rabi na dare.

Niger Agadez
Chapter 111 · 0% Book details