Sashe 60
Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kansa ya girgiza yana kame fuska ya furta.
"Alright, I'll leave you if you break it.
Ki tashi kije kiyi sallah."
Ya ƙarasa maganar yana juyawa tare da zuba hannayensa cikin aljihu yana takunsa a nuste.
Da sauri ta diro daga bed ɗin tana binsa ta kamo tsintsiyar hannunsa daga cikin aljihunsa, tana ƙoƙarin zaro hannunsa na dama, da wata kalar shagwaɓa ta fara magana.
"My brother Habiby please kace ka yafe min na zauna gidanka, Wlh bazan ƙara rashin ji ba..."
Cikin wata irin murya ya furta.
"Cire hannunki daga aljihuna, ya watsa mata kallon kashedi, kafin ma ya sake magana ta saki hannunsa kamar zatayi kuka ta nufi bathroom ɗin da gudu.
Anutse ya nufi hanyar fita yana sake tura hannunsa cikin aljihunsa.
Khairat tabi bayansa tana faɗin.
"My brother yau inason zan biya gidan Aunty Sumy daga school, amma kafin adawo daga masallaci zan dawo"
Kallonta yayi a hankali ya furta.
"Ok idan kin shirya kije parlour na zan ajiye maki Kuɗi ki ɗauka, ki dinga kula da driving Khairat"
Cikin farin ciki ta amsa da.
"Ok my brother thank you Allah ya ƙara girma"
A hankali ya amsa da.
"Ameen"
Ya fice ta rufo ƙofar ta dawo ta zauna tana cigaba da duba Books ɗin.
Gun su Suhaima ya nufa.
Ya murɗa ƙofar yaji ya buɗe ya shiga.
Yaran sun koma bacci, hajjah Mama na zaune tana lazimi ya shigo da sallama bedroom ɗin.
Hajjah Mama ta amsa ya gaisheta cikin girmamawa yana zama.
Ta amsa fuska sake tana tambayar sa.
"Ya jikin Bilkisu da sauƙi "
"Eh ga ta can na tasheta tayi sallah"
Ya ƙarasa maganar yana duba agogon bangon dake manna a bedroom ɗin, bakwai sauran minti ashirin.
Ya miƙe ya nufi gun Suhaima ya sanya tattausan hannayensa ya cire mata Duvet yana kamota a hankali ya furta.
"My Babies Oya tashi ayi shirin school yau juma'a ne fa"
Suhaima ta buɗe lumsassun idanunta tana shagwaɓe fuskarta.
Murmushi ya sakar mata yana ɗauketa cak ya direta ƙasa, yana faɗin.
"Oya bathroom Babie kinyi sallah?"
Kai ta ɗaga tana faɗin.
"Eh na tashi fitsari ana sallah sai nayi"
Kiss ya manna mata a goshinta, ta tafi ya zauna a gefen bed ɗin Al'amin ya cire masa Duvet ya ɗaukesa ya ɗora akan cinyarsa yana faɗin.
"Oya My boy Amiin kayi sallah?"
Al'amin ya laɓe jikin mahaifinsa yana faɗin.
"Eh Aunty Suhaima ta tayar dani nayi"
Kiss ya manna masa a hankali ya furta.
"Very good my Babies I love you, muje na shirya ka, Suhaima akwai daɗewa a bathroom kar ku ɓata lokaci"
Ya ƙarasa maganar yana ɗaukansa ya manna ƙirjinsa yana kallon Hajjah Mama ya furta.
"Hajjah Mama zanje na shirya me gidanki. Suhaima! Idan kin fito ki kawo min uniform ɗin Amiin ɓangare na."
Hajjah Mama ta washe baki tana faɗin.
"Toh Abbah sai kun fito"
Wanka ya masa da ruwan ɗumi ya goge shi da tsaf da towel ya shafesa da lafiayyan body lotions nasa, ya gyara masa sumarsa.
Suhaima ta kawo uniform ya saka masa tsaf yace suje maza suyi breakfast kafin bakwai da rabi ta cika.
Yah Boss
Yana gama shirinsa ya fito yau wasu irin manyan kaya ya saka wani Yadi mai masifar tsada Beige Brown ne ɗinkin kawai ya isa kasan asalin tsadar Yadin, ba ƙaramin kyau Yah Boss yayi ba.
Khairat tare suka fita da yaran tace Hamza ya zauna idan an kusa tashi yaje ya ɗauko su, yanzu zata ajiye su sunata murna suka tafi a motar Khairat.
Misalin ƙarfe takwas dai-dai Yah Boss yabar gidan.
Amma sai da ya biya gun hajjah Mama ya bata sallamar baƙin Zarah akan ta basu ai masu godiya, akwai inda zai biya kafin yaje gun aiki yau juma'a ne, shiyasa bazai samu damar sallama dasu ba.
Tai masa godiya tana saka masa albarka, dan a zaton ta yaje jiya sun gaisa.
Tace ya kamata su sauka ƙasa.
Yana riƙe da hannunta suka sauka, ya barta nan parlour shi kuma ya wuce yana amsa waya.
Zarah ko takaicin Yah Boss da baƙin cikin ƙyamar da ya nuna mata taji zafi sosai, amma ta ɓoye taje kitchen ta dafo tea suka gaisa da Jamilu yana haɗawa su Suhaima breakfast wanda zasu yi a gida da na tafiya school.
Haka ta dawo bata bari kowa yaga ɓacin ranta ba, tunda ita ne taja.
Juhainah ko tana idar da sallah ta koma tayi kwanciyarta.
Da misalin ƙarfe 9:20 Am.
Abba Abdallah ya kira Papa lokacin Yah Boss yana gidan ya biyo yayi breakfast Sbd baya buƙatar ganin kowa can gidan nasa akan dinning ɗin, shiyasa bai tsaya yayi breakfast ba, yazo gidansu.
Bayan sun gaisa da Papa Abba yake faɗa masa zuwa yamma zasu zo da ƙaninsa domin neman alfarma, akan a matso da auren Juhainah da Jamal.
Papa dattijon Arziƙi mai dattaku ya amsa da babu matsala sai sun zo ɗin.
Sai bayan da suka gama breakfast, Yah Boss yana ƙoƙarin tashi Papa ya kalli Yah Boss yana murmushi yace.
"Abbah! Iyayen Jamal suna zuwa da yamma neman alfarma a rage masu lokacin auren bansan dalilin ba, na amsa masu dai akan sai zon"
Yah Boss ya yagi tissus yana goge bakinsa a nuste cikin kamewarsa ya furta.
"Ok alright Papa zanzo in sha Allahu daga nayi sallar la'asar, abd inada meetings yau sosai"
Papa yana murmushi yace.
"Yawwa Abbah yaron kirki Allah ya maka albarka, sai kazo"
Anutse ya amsa da.
"Aamin Ya Rabbi Papa, Maah ni zan wuce sai yamma ɗin."
Maah tana murmushi tace.
"Tom Abbah sai ka dawo, ya kwanan su Suhaima? Babu wata damuwa ko?"
Lumsassun fararen idanunsa ya kafe Maah dasu.
A hankali ya furta.
"Babu wata damuwa MAAH"
Ya ƙarasa maganar yana ɗaukan wayansa wacce yake magana da familles nasa, sauran wayoyinsa na gun Fu'adh.
Maah cikin farin ciki tace.
Ma sha Allahu, ya baƙin?"
Yah Boss anutse ya furta.
"Hajjah Mama tace yau zasu tafi, na bada Sallama a basu, ita hajjah Mama tana nan ai"
Ya ƙarasa maganar yana barin dinning room ɗin Sbd kar kuma Papa ko Maah su sake jefo masa wata tambayar.
Yana fitowa bayan ya shiga mota kai tsaye police station suka nufa.
Juhainah sai ƙarfe 10 harda mintina ta farka daga bacci.
Wanka tayi ta shirya tsaf cikin jallabiya abaya baƙa, tayi kyau kanta sanye da bak'ar hula mai kyau.
Dinning room taje ta ciko tumbinta dam ta dawo parlour ta kunna Tv ta zauna kenan, su Zarah suka fito harda hajjah Mama dasu Ramlah ƴan tafiya.
Kallo ɗaya tai masu ta watsar.
Su ma ba wanda ya sake marmarin kallonta.
Hajjah Mama tana kallonta tace.
"Namesake ya jikin naki?"
Juhainah haushin Hajjah Mama take ji ganinta dasu Zarah, amma ta amsa da.
"Ni lafiyata ƙalau, ina kwana Namesake"
Hajjah Mama tuna ashe fa ita bazata san me ya faru da ita ba, tayi shiru tana amsa gaisuwan, tana faɗin.
"Muje muyi wa baƙi rakiya mana Namesake"
Juhainah ta maƙale kafaɗa tana turo jajayen laɓɓanta masu kauri gaba, ta maida hankalinta akan Tv.
Azizah dai tuni tayi gaba da abin takaici.
Zarah ma bata yi magana ba.
Da Harara tabi su har hajjah Mama da ta zaƙe cikin lamarin.
Direban da aka tanada dan kaisu yana cikin mota zaune, harda Zarah akaje gun motar.
Duk suka shiga Zarah dai bakinta ya mutu bata iya ce masu uffan ba, tasan bata da bakin magana.
Hajjah Mama ta masu addu'ar sauka lafiya tana masu godiya tare da faɗin Sai na taho in sha Allahu.
Zarah fatan sauka lafiya tai masu bata da wani abun cewa yanzun.
Koda suka dawo Juhainah ta bar masu parlour Sbd bata buƙatar magana da kowa a cikinsu...
★
Sha biyu da ƴan mintina Khairat ta nufi gidan Aunty Sumy a motarta.
Lokacin da taje yaran basu dawo daga school sai little Sadeeq shi da Mamarsa.
Khairat cike da kunya ta faɗawa Aunty Sumy Fu'adh yana son turo iyayyensa, ta faɗawa Maah ita Wlh bazata iya ba.
Aunty Sumy ta kalli Khairat tana murmushi tace.
"Khairat! Manya, Ok shi kenan ina sha Allahu zanje gidan da yamma na sanar da Maah, yaushe ne suke son zuwa?"
Khairat tace.
"Shi fa cewa yayi ko yau ma idan an basu izinin zuwa Aunty Sumy"
Aunty Sumy tace.
"A'a zuwa kwana biyu dai Khairat! Kamar ana matse dake.
Wai Khairat ya amaryar Yah Boss? Da Juhainah iyayen rigima?"
Khairat ta taɓe baki tana faɗin.
"Anya Aunty Sumy Yah Sadeeq yana sonta kuwa?"
Aunty Sumy tace.
"Duk laifin Hajjah Mama ne ta fa san halinsa tsakani da Allah"
Khairat tace.
"Juhainah ma bataji Inaga har fitsara tai masu"
Aunty Sumy tace.
"Wlh ba ko zai hanata ba, sai dai Allah basu hƙr"
Khairat tace.
"Juhainah ga sakin zance abun sai addu'a, wannan jinnu nata babu imani jiya Wlh wani harbi da suka min ciwon kai kamar bazan waye ba, ga ninniƙe yanzu haka jikina ciwo yake"
Aunty Sumy tace.
"Yakai nawa ne, ni da Laftani da ƙasa tayi, sai da ƙuguna ya amsa, jiya tashin sukayi kenan?
Ya ALLAH kai mana maganin wannan matsala ta Juhainah..."
Aunty Sumy taja Khairat suka shiga kitchen girki ta hanata tafiya dole sai Text ta turawa Fu'adh akan yayi haquri Aunty Sumy ta riƙeta bazata samu daman dawowa ba sai yamma, zuwa dare zasuyi fira idan ta dawo.
Bayan sallar la'asar Abba Abdallah da ƙaninsa Giɗaɗo suka tafi gidansu Juhainah.
Koda suka iso Yah Boss yazo harda Mustapha Umar Nasir duk suna nan, kasancewar duk ran juma'a suna haɗuwa su saka Maah gaba ana hira, watarana harda matansu.
Amma banda Yah Boss cikin taron su, dan ba kowane lokaci yake da dama ba, wani lokacin baya ma garin ko ƙasar.
Tabar karamci sukayi masu cikin mutuntaka bayan an gaisa sun sha rawa da motsa bakinsu, suka nemi alfarma akan matso da ranan ɗaurin auren kusa.
Papa cikin mutuntaka yace su zaɓi lokacin da suke ganin yayi musu.
Abba Abdallah cikin farin ciki ya zaɓi sati biyu masu zuwa ɗaurin auren da bikin, wato juma'a ta sama.
Papa da ƴaƴansa suka amince da hakan tare da fatan Alkhairi a haka taron ya watse cikin farin ciki.
Yah Boss daga nan gidansa ya nufa akwai baƙin da zai yi a can ɗin.