← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 113

Sashe 3

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya ku kaji salon naci gaba ko a barsa? Amman fa ko shimfiɗa bamu fara ba, nayi maku kakkaɓar fili ne, akwai chakwakiya, akwai soyayya ta gasken gaske akwai romantic, akwai tausayi kai akwai komai ma, cikin wannan tafiyar...

Sai naji saƙon ku naci gaba ko nayi kwanciyta.😂💃
+22796515805
[25/12/2025 14:39] null: _*JUHAINAH*_
Love Story 💗🫂
Free Book
By
Real Rahma Ladingo
Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat.whatsapp.com/GRswtgIMDkW2NpM52fgqWx

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb76GQj5K3zPGp0sQf3U

Page 2

Juhainah ta buɗe lumsassun fararen idanunta tana riƙe hannayen mahaifiyarta tace.
"Amin my Maah I love you"
Ta ƙarasa mgnar tana sumbatar hannayen Maah, ta saki tana lumshe idanunta tare da shigewa cikin quilt ɗin.
Maah ta sauke ajiyar zuciya tanajin wata irin masifar ƙaunar ƴarta har cikin jini da tsokarta, da ɓargonta, duk so da ƙaunar da take yiwa Abubakar Sadiq kasancewar shi ɗa na farko kuma kamilin ɗa mai biyayya, amma ta rasa wa tafi so da ƙauna tsakanin shi da Autah, duka ƴaƴanta 7 da ta haifa da cikinta tana mutuwar son su, amma ƙaunar Yah Boss da Juhainah halitta ne acikin zuciyarta, da kuma jininta da ɓargonta har ma da tsokarta, bata tunanin idan ta rasa ɗaya acikin su biyun zataci gaba da rayuwa mai inganci ko anfani ma.
Sake matsowa tayi bakin bed ɗin tana sake zama ta ɗan kwanto jikin Juhainah da take lulluɓe cikin quilt ta rungumeta tana faɗin.
"Autar mata Juhainah idan kinji alamun babu sauƙi ki kirani a waya na kira doctor ko muje asibiti da kanmu fa, idan ba haka ba zan kira miki Abbah ya kaiki da kansa."
Juhainah da har bacci ya fara fizgarta ta janye quilt ɗin daga rufe fuskarta tana buɗe lumsassun fararen idanunta da wata kalar shagwaɓa ta rungume Maah a hankali tana faɗin.
"I love you Maah I love you Maah idan bazaki nutsu da kwanciyar nawa ni kaɗai ba muje can ƙasan sai na kwanta bedroom naki, amma don Allah kar ki haɗani da Yah Boss."
Ta faɗa tana sake shagwaɓe fuskarta cike da kalar tausayi.
Maah tana shafa bayanta a hankali tace.
"Shi kenan Autar mata ki kwanta ki huta anjima zanzo na sake dubaki, yi baccin ki bazan faɗa masa ba."
Juhainah murna fal zuciyarta amma taƙi nunawa ta lumshe idanunta tana sake ƙamƙame Maah tare da sake faɗin.
"I love you Maahta."
Maah ta gyara mata rufanta tana faɗin.
"Love you too Autah Juhainah ina sonki sosai har can ƙasan zuciyata ƙaunarki nake Autata."
Juhainah wannan kalamai na ma su suke sakata sangartata da jin itane zuciyar gidan baki ɗaya, shiyasa take masifar son Maah ɗinta.
Sake shigewa jikin Maah tai kamar za'a rabasu.
Yadda Maah take shafa mata dogon gashinta mai santsi tana karanto mata addu'o'i ko minti goma ba'a yi ba bacci mai daɗin gaske da nutsuwa ya sace ta jikin Maah mahaifiyarta.
Maah ganin baccin ya ɗauketa ta kwantar da ita tana lulluɓe ta da quilt ta miƙe tana rage mata ƙarfin A'cn ta rage mata hasken ɗakin ta fice tana rufe mata ƙofar.

Aji Meta
Unguwar
80 Unit
Haɗaɗɗan Big House ne na gaske ginin tamkar a ƙasar Larabawa, kana kallon gidan da tsarinsa kasan mai shi attajiri ne na gasken gaske, bedroom's 3 da suke bene, tsayawa irin tsarin da aka musu ɓata lokaci ne, amma dai an zuba dukiya ta gaske.
Haka ma sauran bedroom's 7 da suke ƙasa, akwai kaya ciki amma kadaran kada han ne, sai dai akwai komai na mora rayuwa cikinsu su ma.
Ma'aikata 5 ne acikin gidan sai security's biyu, wanda iyayensa ne suka kafe dole sai an ajiye su dan tsare lafiyarsa, duk da ya nuna baya son hakan, amma ya haƙura saboda baya ƙaunar tsallake umarnin su.
Masu masa hidima duka maza ne, Walid shi ne direbansa, wani murɗeɗan matashi ne ƙaƙƙarfan gaske, wanda ya ginu da ilimin boko harda na Islam ɗin.
Security's ɗin kuwa ba'a maganar girmansu da tsare gida bindigu ne koda yaushe a hannunsu, kasancewarsu ƴan sandan da suke tsare gidan yana ƙasar ko baya ƙasar.
Idan bada umarninsu ba basa bari a dinga shiga gidan bare Malam Garba ya buɗe maka gate.
Uniform mai tsada yake ɗinkawa duk masu aikinsa, bare Malam Garba Kasancewarsa mai Gadin buɗe gate, da lura da masu shige da fice duk da akwai manyan security's su biyun.
akwai ɗan madedecin bangare a gidan wanda malam Garba da iyalinsa suke zaune, abin sai ya burge ka, haka suma security's sunada ɓangarensu na zama, kamar yadda sauran ma'aikatan kowa nada muhallin zama a ƙaton gidan, dan haka babu wanda yake kusa da ɓangaren Yah Boss.
Kukun sa Jamilu shine mai girka masa abinci ya gyara kitchen da wanke abinda ya ɓata a kitchen ɗin da wanda ogansa zai ci da Fu'adh da wasu baƙin masu mahimmanci idan yayi.
Shima yana da uniform masu kyau da tsada.
Sai Mas'ud ma'aikaci na 3 sharan compound da gyaran duka bedroom's da parlour's da goge komi ya tsaftace tsaf a kullum ko ba dattin sai an gyara sabida Allah yayi wa Yah Boss wata irin tsafta da shegen ƙyanƙyami shiyasa duka ma'aikatansa sai da ya zaɓi masu tsafta da kamun kai da ilimin addini dana boko sosai.
Ma'aikaci na 4 Habibu shi ke masa wankin a washing machine, yayi guga idan yayi kace daga Company aka bugo kayan, sannan shi yake kula da dukkan flowers ɗin gidan yake basu ruwa da gyaran su sannan shi yake kula
da garden ɗin gidan mai cike da tsari, can ɓangaren Gabas kusan garden baya akwai haɗaɗɗan swimming pool da wasu irin kujero na hutawa.
Yah Boss yana masifar son Maah son so yake wa mahaifiyarsa baya taɓa tsallake umarnin ta, baya haɗa iyayensa da kowa a duniya haka ƙanmwarsa Aunty Sumy yana mata sahihiyar ƙauna, dan har gidanta idan ya bushi iska yana zuwa, ita ɗaya ta samu gatan nan gun Yah Boss.

Ƙaton falo ne wanda ya gaji da haɗuwa.
Ƙaton Frame ɗauke da hoto.
Magidanci fari ingarma namiji tamkar Balarabe.
Matar da take rungume a jikinsa tana dariya shi kuma kyakkyawan smile akan kyakkyawar fuskarshi mai cike da kwarjini.
Kallo ɗaya zaka mata kasan Balarabe ce, saboda shigarta ma ta nuna hakan.

Sai yara biyu da suke tsakinin iyayen nasu suma suna dariya alamar suna cikin kwanciyar hankali.
Kowane frame da yake kafe jikin bangon babu wanda babu matar da mijin da kuma yaran kuma ko wannensu suna rungume da juna cikin tsantsar ƙauna da soyayya mai tsafta wanda babu sirki.
Manyan frame ɗin da suke ɗauke da hotunan su, su suke maka Welcome kowane ƙaton bangon da yake falon gabas yamma Kudu da Arewa.

Wani haɗaɗɗan Black gayene zaiyi shekaru 33 a haife, kyakkyawane sosai ya haɗu ta ko ina, iya tsarin namiji dai ba laifi an tsarasa, akwai hanci ga kyawawan idanu, yanada lallausan suman gashi mai ɗan yawa.
Kana kallonsa jin daɗi ya gama kwanta masa, ko daga tsadaddiyar suturan da take jikinsa, daga cikin wandon da yake sanye jikinsa kana ganin tudun bindiga.
Wasu kima-kiman wayoyin da suke ajiye gabansa akan wani ƙaton haɗaɗɗan table na zallar Glass fari tass, duk da kana kallon wayoyin kasan banasa bane shi ɗaya saboda wayoyi ne har guda 4 biyun ƙarshe tsada ne ƙirar iPhone da ƙirar Samsung.
Fu'adh da kansa a ƙasa yake danna laptop yaji Ringing ɗin wayan ogansa na ruri tana neman agaji.
idanunsa masu kyau da tsari ya ɗago yana kallon iphone ɗin da take ta ruri.
Iskar bakinsa ya fesar waje yana ɗaga kansa yana kallon hanyar stairs, duk da yasan babu ko alamarsa, da ya fito ƙamshinsa ne zai fara kawo masa farmaki kafin ma ya sauko ɗin.
A natse ya beƙa hannunsa yana ɗaukan phone ɗin, yayi picking Call ɗin tare da kai wayan kunnansa yana sallama cikin muryansa mai daɗi da tsare gida yace.
"Hello Good morning, Sir baya kusa yana wani abun zuwa anjima zai maido kiran in sha Allahu."
Daga can ɓangaren mai kiran ya jinjina kansa kasancewar yasan Fu'adh farin sani koda kana son ganin Alhaji Abubakar da gaggawa ta ɓangaren business ko wata matsala da ta shafi sai police ya shigo lamarin, toh ka fara sanin Fu'adh, yanada tabbacin tunda Fu'adh yace zai kirasa toh tabbas zai kirasa ɗin.
Cikin karamci Alhaji Atiku yace.
"Thank you Sir Fu'adh a sake tuna masa inason haɗuwarmu yau ɗin kamar yadda na saka rai, amma yaƙi bani amsa guda Please."
Fu'adh yaja numfashi yana gyaran murya yace.
"Ok saƙon zaije kunnen sa."
Godiya yai masa ya katse kiran.
Fu'adh ya kalli hanyar kitchen yana ɗan ware murya yadda Jamilun zaiji yace.
"Jamilu! Ya har yanzun kasan fa idan Sir ya fito bazai jiraka ba fita zamuyi."
Wani tsararren kitchen ne ya gaji da haɗuwa wani matashi mai tsananin tsafta da kama jiki wato Jamilu kenan Kukun Yah Boss tsaye yanata ƙoƙarin ƙarasa masa breakfast saboda yau ya makara ciwon kai yayi fama daren jiya, bai samu bacci da wuri ba sai kusan asuba, shiyasa ya makara, dai-dai lokacin kuma muryan Fu'adh ta shiga kunnensa duk da kuwa akwai nisa tsakanin kitchen ɗin da falon amma kasancewar yanayin ginin anaji idan ka ɗaga murya.

Da sauri yabar abinda yake yana ɗaukan kitchen towel ya nufo falon yana goge hannayensa.

Cikin sakin fuska ya ƙarasa parlon yana gaishe da Fu'adh yana faɗin."Uban gidana Wlh jiya da ciwon kai na kwana mai zafi duk da nasha magani sai kusan asuba bacci ya saceni shiyasa na makara amma na kusa ƙarasawa kafin Sir ya fito, zanyi ƙoƙari na kammala komai."

Fu'adh ya tsayar da danna laptop ɗin ya ɗago yana kallon Jamilun yana faɗin.

"Subhanallahi ai da ka faɗa ba sai ka wahalar da kanka ba tunda larura ce, kaje kawai ka kwanta ka huta idan ka gama ba sai kayi girkin rana ba, sai ka raba ka kaiwa kowa nasa Allah ya ƙara sauƙi akwai isassun magani wajan ka ne ko sai kaga likita?

Ya kamata a ƙaro maka abokin aiki saboda irin wannan akasin, zanyi magana da Sir yau in sha Allahu."
Chapter 3 · 0% Book details