← Book details Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 113

Sashe 93

Juhainah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farid yayi murmushi yace.
"Allah baki haƙuri Bab, wlh ina sonki kishine, yanzu dai gani a cikin gidanku nazo biko, Daga nan muje ki amso ɗinkin ki"

Surayya tace.
"Kaci Sa'a ƴan kirkin suna kusa da bazan fito ba. Bari na faɗa wa Abba da Mamy"

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran.

Abbah da Mamy suna zaune suna magana Surayya ta shigo da sallama.
Suka amsa.
Zama tayi kusan Mamy tana faɗin.
"Mamy Farid ne yazo, zan bisa na amso ɗinkina na Material da ba'a Gama ba kafin bikin"
Mamy tace.
"Nifa bana son shashanci, Farid muharaminki ne da dole shi zai Kaiki?"
Abba yace.

"Surayya! Shin kina son yaron nan ko karatun zaki rage kafin auren? A sona nafi son kiyi karatun ki rage, ko nan da shekara biyu ne, kafin lokacin kinyi shekara 20 harda ƴan watanni sama..."

Surayya tace.
"Eh Abba nafi son nayi karatun na rage, amma ina yinsa yanada kirki da haƙuri"

Abba ya girgiza kansa yace.
"Ok zai jiraki Kenan?"

Surayya tace.
"Ban saniba sai na tambaye shi"

Abba yace.
"Toh ban amince ki bisa amso ɗinkin ba, inda kin tashi ki faɗa min na faɗawa Jamal zai Kaiki ..."

Surayya ta ƙyalƙyale da dariya tana toshe bakinta, tuna fuskar Jamal kamar anyi wasan kura.

Mamy ta kalleta tana tafa hannayenta tace.
"Jamaluddin kike yi wa dariya Surayya? Ah lallai wuyanki ya isa yanka, tabbas ba banza ba yake naɗarki kamar ya samu Jakka, Wlh zan ɗaure masa ƙugu ya kawo tsohon nan a aura maki..."

Surayya ta haɗe hannayenta tace.
"Allah baku haƙura suɓatar bakine Mamy, don ALLAH Abba ka basu haƙuri."
Abba yace.
"Ai bakyajin magana ne, kije ki sallami yaron can ki dawo"

Surayya ta juya ta fice kamar zatayi kuka ta tsani jin zancen, za'a aure da wanda bata so, koda suke son babban mutum ita da Juhainah ai ba tsoho suke so ba, mai shekaru irin na Yah Boss suke so tsaka-tsakiya.

Farid yana tsaye jikin motarsa ta iso ta masa sallama.
Ya amsa yana kallonta.
Hararensa tayi tace.
"Ai ga shi kaja an hanani sai ka tafi"

Farid yace.
"Hummm! Naji Baby yanzu Wlh bakya sona Sojan nan ya gama da zuciyarki, kuma da gangan yayi hakan, kuma in sha Allahu sai na aure ki sai dai ya mutu"

Surayya abun dariya ya bata tayi dariya tana tafa hannunta tace.
"Wai Yah Nasir kake cewa ina so?"

Yawu ta tofar tana murguɗa masa bakinta tace.
"Na tsani mugun mutum shi Baida imani ni kai nake so, amma sai ka jira na rage karatuna, idan kana sauri kaje ka auri wata"

Farid yace.
"Nagode Baby zan jiraki in sha Allahu, nima kinga ai ina karatun"

A hankali tace.
"Ok haka yayi zan koma kar Yah Jamal ya fito ya korani, kasan halinsa."
Bai musu ba suka yi sallama ta tafi shi ma ya shiga motar sa ya tafi.


Juhainah

Bata farka ba sai bayan sallar la'asar lokacin Jamal ya dawo daga masallaci yana zaune parlour yana kallo, yana son zuwa tashinta tayi sallah yana tunanin kar ya tasheta ta farka da abun.

Wanka tayi ta gasa jikinta sosai yadda taji yana mugun ciwo, tana gasa jikinta taji daɗi sosai.

Tana fitowa tayi sallar la'asar ta murza body lotion, ta saka riga da skirt na atamfa ta murza ɗauri ta shafa lipstick.
Wani irin fitinannan kyau tayi, ta fesa turare ta nufi parlour Sbd azabar yunwa da take ji.

Tun bata ƙarasa isa parlour ba Jamal ya shaƙo ƙamshinta.
Waigowa yayi suka haɗa ido.
Da mugun mamaki take kallonsa ganin fuskarsa kamar ya fito daga yaƙin takubba.

Juhainah akwai tausayi duk da bata sonsa, ga haushi sa tanaji, amma haka ta iso gunsa ta zaune kusansai tana son haɗa kalmomin da zata tambaye shi me ya sameshi.

Kusanta ya matso jikinsu ya haɗe ya riƙe hannunta ya sumbata, a hankali yace.

"Sannu Juhainah kin tashi? Kinyi sallah?"

Kai ta ɗaga a hankali tace.
"Mi ya sameka a fuska? Naga wuyanka harda dressing bandage, fita kayi bayan nayi bacci kayi accident?"

Jamal da mugun mamaki yake kallonta, yace.
"Haba Juhainah yanzu tsakaninki da Allah baki san me ya faru ba? Duk yaƙin da aka yi baki san komai ba tsakanin ki da Allah?"

Da mamaki take kallonsa tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Yaƙi akayi? Suwa saku kawo mana hari?"
Hannunta da yake cikin nasa ya murza a hankali yanajin yadda taushin hannunta yake ratsa tafin hannunsa.
A hankali yace mata.
"Ai dake akayi yaƙin kece kika jimin ciwon"

Da mugun mamaki take kallonsa ta zare hannunta cikin nasa ta dafe ƙirjinta tace.
"Ni? A'a haba dai mafarki kakeyi wallahi, ko wani ta ya zan jiwa ciwo har haka bare kai da igiyoyin auren ka suke a kaina har uku, ni bari naci abinci ma"

Ta ƙarasa maganar tana ƴar ƙaramar dariya ta nufi gun dinning table ɗin, dan sosai ya bata dariya kuma ta san yayi haka ne dan ya bata dariya.

Jamal sai tunani ya ɗarsu aransa tabbas Juhainah da gangan tayi masa, kenan duk abinda tayi masa?
Tunda ga shi zataci abinci kuma tana dariya duk da batada cikakkiyar lafiya.
Anutse Juhainah ta zauna ta buɗe kulolin ta fara zuba abincin.
Sai da ta fara ci ya miƙe yazo ya zauna kusanta.
Kallonsa tayi tana tauna tsokar naman dake bakinta, tace.

"Na zuba maka ne?"

Ganin yadda fuskarsa take sosai abin ya bata dariya, da yace wai ita ne tayi masa sai dariyar ta sake kamata ta fara a hankali Sbd batada ƙarfin yinta sosai.

Jamal zuciyarsa ta harzuƙa.
A hankali yace.
"Kenan da gangan kikayi komai dan kin ɓata min fuska ko? Ko kuma ramuwa kikayi Sbd na amshi budurcinki?"

Da mugun mamaki take kallonsa ranta ya fara ɓaci, miƙewa tayi tuna nasihar Papa, ta nufi bedroom ɗinta ta barsa, Sbd bata son su fara rikici.

Cikin zafin zuciya ya biyota tana shirin rufe ƙofar ya turo sauran kaɗan ta faɗi, ta riƙe ƙofar tana masa kallon mamaki sai ya bata dariya matuƙa.

Yanzu ta gano borin kunya yake, duk yadda akayi da yafita ya haɗu da ƴan Daba sun lafta masa tsinannan duka ne.

Dariya take sosai ta nufi bed tana ƙoƙarin hawa ya damƙota yana faɗin.

"Sbd kin maidani ɗan iska kin jimin ciwo amma kina dariya? Ko gani kike Sbd jiya aka kawo ki na amshi budurcinki Bazan iya sakinki ba na koya miki hankali da darasin rayuwa?"

Dara-daran kyawawan idanunta ta zaro gabanta yana faɗuwa, Sbd mamakin jin abinda yake faɗa.

Amma sam bata gasƙata maganarsa cikin zuciyarta ba, gani take barazana yake, ko giyar wake yasha jiya a kawota bayan ya rabata da darajarta ya saketa yau, ai zuciyarta sai tayi bindiga.

Dariya ta sake tace.
"Ai nasan ko giya kake sha bazaka iya wannan gangancin ba, jiya a kawoni gidanka ka sakeni yau, kai duniya zata zaga Wlh, kuma ka daina furta kalmar saki babu kyau..."

Jamal ya zaro idanunsa yana sake matseta a jikinsa ya kamo kyakkyawar fuskarta yana murmushin mugunta yace.
"Ok Sbd nace zan sake ki kike danganta Ni da mashayin giya?"

Ya ƙarasa maganar yana shafar ta ya ɗora hannunsa akan ƙirjinta da suke bala'in kashesa, ya fara shafar su.

Turesa ta fara yi tace.
"I don't want it, Yah Jamal.

Eh ai naga maganar taka ne bata masu cikakken...."
Sai taja burki ta sakawa bakinta linzami, tana faɗin.
"Please stop it, ka sakeni naje na kwanta kaina ciwo yake, don ALLAH Yah Jamal ka rabu dani na huta.

Wai me yayi zafi ne? Wlh bana son tashin hankali a yanzu.
Aure fa muke yanzu ba da bace, babu wani abu da ya rage mun zama ɗaya.
Sakeni na kwanta juwa nake ji"

Jamal
Sakinta yayi yana faɗin.
"Bilkisu Na Sakeki saki ɗaya saki biyu saki Uku, kije ki koyo hankali da tarbiyya sai na maida ki ɗakin ki..."

Ya gama faɗin haka ya juya yabar ɗakin yana murmushi.
Ai Juhainah yana faɗin haka kanta ya yi wani irin sarawa, saki uku fa ya mata kai tsaye ba dalili, yake maganar zai maida ta, ina zata kai abun kunyar nan? Kwana ɗaya gidan miji an mata sakin da ba lailai ta zauna da shi ba.
Wasu zasu ɗauka bai saketa cikakkiyar budurwa ba, za'a kafa tarihi a kanta maybe an daɗe ba'a kafa irinsa ba.

Kuka take son yi ta gaza, ta dafe saitin zuciyarta, idanunta suka rufe rufff ta yanke jiki ta faɗi nan ƙasa sumammiya.

Sbd furucin yazo mata a mugun bazata, har cikin zuciyarta bata taɓa kawo Jamal zai iya sakinta ba, saki ma na ƙasƙanci, duk da bata sonsa baya sonta, amma tasan ƙaddara na iya sakawa su rayu tare har abadan, amma ina kashhh! Ya yanke wannan alaƙar, dan Juhainah tana muguwar zuciya idan ka tozarta ta.

Jamal yana fitowa parlour ya zauna ya kunna Tv, yana jiran Juhainah ta fito ta basa haƙuri ya maida ita.

Dan har zuciyarsa yayi mata sakin ne na wuccin gadi, ba wai har abada ba, tunda saki uku lokaci ɗaya zaman saki ɗaya ne.
Sbd yasan Mamy tana iya masa baki idan taji sakin, kafin taji zai maidata tunda, yaji zai iya zama na har abada da ita, har cikin zuciyarsa, zai koya mata hankali akan dariya da ta masa, da kiransa ɗan giya shi da sigari ya tsani jin warinta bare giya.

Sai yasha mamakin jin Juhainah shiru bata fito basa haƙuri ba, baiji kukanta ba.

A dai-dai wannan lokaci kuma
Yah Boss yana gidansa, zaune a down Stairs,
Cikin shigar ƙananun kaya na shan iska farare tass, yayi bala'in kyau, sai ƙamshi yake, sanyi Ac na ratsa dukkan sassan jikinsa.Tv yake kallo tashar Sunnah TV Sbd shi bai da lokacin kallon Film daga wa'azi sai labarai.

Su Suhaima sun tafi shopping da Fu'adh.

Yayin da mayya Zarah tana zaune itama a parlour amma kowa ɓangaren sa daban, taci ubansu kwalliya, tana waya da su Azizah.

Yah Boss Ƙirjinsa yayi wani irin bugu, Juhainah tazo masa a zuciyarsa sai yaji kamar ba lafiya ba, yana jin tsoron jinnunta sun tashi ne.
Haka kawai ya samu kansa da kiran Aunty Sumy.
Chapter 93 · 0% Book details